Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (1)

Bunƙasar Wayar Salula - Tsakanin Jiya da Yau

Manyan babbar manhajar wayar salula dake cin kasuwansu yanzu su ne: “Android”, wanda kamfanin Alphabet (ko Google) yake mallaka tare da bayar da lasisinsa ga sauran kamfanonin ƙera wayar salula dake duniya.  Sai kuma babbar manhajar wayar salula mai suna “iOS” na kamfanin Apple, wanda ke ɗauke kan manyan wayoyin salula da kusan suka fi kowace irin wayar salula tsada a duniya. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 4 ga watan Agusta, 2023.

107

Matashiya

Ga waɗanda suka fara bibiyar wannan shafi mai albarka a farkon lokaci, za su iya tuna doguwar maƙala da muka taɓa gabatarwa kan wayar salula mai take: “Bayani Kan Wayar Salula”, mai shafuka 86.  Na gabatar da wannan maƙala ne cikin makonni kusan 30.  Wajen watanni 7 kenan.  Wannan maƙala ita ce maƙala mafi tsayi da muka ɗauki mafi tsayin lokaci muna kawowa a wannan shafi mai albarka.  Domin ta ƙunshi kusan dukkan wani abin da za ka iya hararowa ne kan wayar salula a wancan lokacin.

Tun bayan gabatar da wannan maƙala mai tsayi da nayi tsakanin shekarar 2011 da 2012, ban gushe ba ina ta samun saƙonni masu alaƙa da rubutun, wajen neman cikakkiyar maƙalar, ko neman shawara kan wace irin waya za a saya, ko kuma meye yasa wayoyin salula wasu suke da ɗan karen tsada, wasu kuma da araha?  Me ke kawo wannan banbancin na farashi?  Amsa kan wace irin waya mai karatu zai saya, na sha maimaita shi a wannan shafi namu mai albarka, da ma saƙonnin Imel ko na tes da nake aikawa ga galibin waɗanda ke min irin wannan tambaya.  Abin da ya rage bamu amsa ba shi ne dalilan da ke sa wasu wayoyin salula ke da ɗan karen tsada, wasu kuma da araha.  Wannan, a taƙaice, shi ne abin da wannan maƙala ta mu ke ƙunshe dashi in Allah Ya yaso.

Bunƙasar Wayar Salula: Tsakanin Jiya da Yau

Ko shakka babu akwai bambanci mai girman gaske tsakanin fasahar wayar salula na shekaru 10 zuwa 20 da suka gabata, da irin waɗanda muke amfani dasu a zamanin yau.  A shekarun baya, kamfani mafi girma da tasiri a harkar salula a duniya shi ne kamfanin Nokia.  A yanzu ba a jin ɗuriyarsa. A baya babbar manhajar salula da ake taƙama da ita – wanda duk cikan wayar salula, idan ba ita bace a kanta, a banza ne – ita ce babbar manhajar “Symbian”, wanda kuma kamfanin Nokia ne ya mallaketa a lokacin.  Duk sauran kamfanonin wayar salula na karɓar lasisi ne a wajensa don ɗora wannan babbar manhaja a wayarsa don samun kasuwa.  A yanzu ba maganar wannan babbar manhajar ma ake ba. Da yawa cikin samari ‘yan bana-bakwai ma, idan ba waɗanda suka samu labarinta a jami’o’i wajen karatu, basu ma santa ba.

- Adv -

Manyan babbar manhajar wayar salula dake cin kasuwansu yanzu su ne: “Android”, wanda kamfanin Alphabet (ko Google) yake mallaka tare da bayar da lasisinsa ga sauran kamfanonin ƙera wayar salula dake duniya.  Sai kuma babbar manhajar wayar salula mai suna “iOS” na kamfanin Apple, wanda ke ɗauke kan manyan wayoyin salula da kusan suka fi kowace irin wayar salula tsada a duniya.

Haka abin yake a ɓangaren zahirin siffofin wayar salula, wajen buɗewa da rufewa, wajen kiran waya da amsa kira, wajen aikawa saƙonnin tes, wajen ɗora katin SIM. Duk a yanzu sun zama tarihi.  Wasu ne suka maye gurbinsu, suna kuma kere su wajen inganci, da girman jiki, da tsawon lokacin amfani, da kuma tsada.

Wayoyin zamanin jiya suna ɗauke ne da manhajojin wayar salula da ake ƙera ko gina da Java, ko waɗanda aka gina da C++, ko waɗanda aka gina da Python.  A yanzu ma ana gina manhojin wayar salula da waɗannan nau’ukan dabarun gina manhaja, amma bambancin dake tsakani shi ne, waɗancan mamhajojin na zamanin jiya, idan aka gina su aka ɗora su tun sadda ake haɗa wayar, to, ba a iya sake ɗora wata manhaja kuma akan wayar.  Amma a zamanin yau, muna da cibiyoyin manhajojin wayar salula akan wayar; ka hau, ka duba manhajar da ta maka, ka saukar, sannan ka ɗora wa wayarka taci gaba da aiki.  Ba wannan kaɗai ba.  Idan kai ƙwararre a fannin gina manhajar wayar salula, kana iya amfani da wayarka wajen gina wata manhaja, sannan ka ɗora manhajar a kan wayar don amfani da ita kai tsaye.

Dangane da yanayi da hanyoyin sadarwa na rediyo ko Intanet ma, wayoyin zamanin yau sun sha bamban nesa ba kusa ba, idan aka kwatanta su da wayoyin salula na zamanin jiya.  A baya mafi girman waya wajen inganci da tsada takan taƙaitu ne da tsarin sadarwa na 3G.  Sauran kuma duk ba su wuce wayoyi masu amfani da tsari da kuma ƙa’idar sadarwa na ƙarni na 2 (2G Network).  Amma a halin yanzu, saboda saurin ci gaba a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani, galibin wayoyin salula suna ɗauke ne kan tsari da ƙa’idar sadarwa na ƙarni na 4 (4G Network) da ƙarni na 5 (5G Network).  To duk me ya jawo wannan saurin ci gaba ne, cikin shekarun da basu shige 15 ba zuwa 20, idan ma sun kai kenan?

Manyan dalilan da suka hadda saurin yaɗuwa da bunƙasar inganci da yawaitar wayar salula da fasahar da ta danganceta a duniya, suna da yawa.  Shahararre daga cikinsu sun haɗa da: ingancin binciken a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani, da samuwar na’ukan wayoyi daban-daban, da yawaitan kamfanonin ƙera wayoyin salula, da samuwar wayoyi masu farashi daban-daban, da tilascin zamani wanda ke sa mutane mallakar wayoyin salula a wasu wuraren da fasahar bata kai ba, da samuwar dokokin kula da harkokin sadarwa daga hukumomin ƙasashe daban-daban a duniya, da dai sauran dalilai masu yawa da suka danganci waɗanda suka gabata.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.