Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (2)

Sikin Ɗin Wayar Salula

Dukkan wayoyin salula masu amfani da sikirin nau’in LCD suna sarrafa haske da launi ne ta amfani da fasahar “In-Plane Switching”, wato: “IPS”, ko kuma “Plane to Line Switching”, wato: “PLS”. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 11 ga watan Agusta, 2023.

92

Ɓangarorin Wayar Salula

Kafin muje bayani kan dalilan dake sa wayar salula tayi tsada ko araha, ta la’akari da ɓangarorinta, zai dace mu san shin, ita wayar salula ɓangarori nawa ne take ɗauke dasu, a kimiyyance nake nufi, ta la’akari da tsari da ƙa’idojin fannin kimiyya da fasahar sadarwa da ƙere-ƙere.  Domin wannan ne zai sa mu iya fahimtar dalilan dake sa wata wayar ta ɗara wata wayar farashi da ma shahara, musamman wajen waɗanda suka san amfani da fa’idojin keɓantattun siffofin da suka keɓance ta da sauran wayoyin salula dake sa’anninta.

Kowace irin wayar salula, kai, da ma sauran na’urorin sadarwa na zamani, suna ɗauke ne da manyan ɓangarori guda biyu; ɓangaren gangar-jiki, wanda a harshen turanci ake kira: “Hardware”, da kuma ɓangaren ruhi, wanda ake kira da suna: “Software”.  Ɓangaren gangar-jiki na ɗauke ne da dukkan sasannin wayar salula na zahiri.  Irin murafu (Cover case), da fuska (Screen display), da na’urar sarrafa bayanai (SoC ko “Chipset”), da batir, da majiyan sauti/murya (Earpiece), da maɗaukan sauti/murya (Mouthpiece ko “Microphone”), da dai sauransu.  Wasu ɓangarorin a waje suke ana iya ganinsu kai tsaye, wasu kuma sai an buɗe wayar ake iya ganinsu.

Ɓangaren ruhi ya shafi babbar manhajar wayar ne, wato “Operating System”, wanda ke ɗuke a saman ƙwarangwal ɗin wayar kenan; dukkan wata manhaja (Software ko Application) da ba wannan ba, to, tana ɗauke ne a saman babbar manhaja.  Babbar manhajar wayar salula dai ita ce ruhi ko ran wayar baki ɗaya.  Idan babu ita, ba ka iya yin komai da wayar salula.  Domin ba za ta tashi ba balle ma ka iya ma’amala da ita wajen musayar bayanai ko sarrafa su.

Waɗannan, a taƙaice, su ne mahimman ɓangarorin wayar salula, kuma kowanne daga cikinsu yana tasiri wajen sa farashinta yayi sauƙi ko tsada.

Dalilan Tsada Ko Araha

- Adv -

Kamar yadda na ambata a baya, dalilan dake sa wayar salula tayi tsada ko araha suna da yawa.  Za mu yi magana akan dalilan da suka shafi ɓangarorinta ne, da abin da ya shafi kamfanin da ya ƙera wayar.  Ga bayanan nan tafe:

Fuskar Wayar Salula – “Sikirin” (Screen Display)

Daga cikin ɓangarori masu mahimmanci a wayar salula musamman ta zamani, akwai fuskar wayar, wanda muke kira “Sikirin”, a ararriyar kalmar turanci da ake kira: “Screen”, ko “Screen Display”.  Wannan ɓangare ne ke lura da bayyana maka kowace irin ma’amala ce kake yi da wayarka.  Daga buɗe manhajar kira, zuwa aiwatar da kira, da neman lambar wanda za ka kira, da aika saƙonni, da karɓarsu, da buga wasanni (Games), da duba lokaci, da duk wata ma’amala da za kayi da wayar salula, kana samun daman yin hakan ne ta fuskar wayar.  Ɓangaren ne mai matuƙar muhimmanci, kamar yadda fuskar ɗan adam take da muhimmanci.

Wayoyin salula na zamani baya ba su da fuska mai faɗi. Amma na zamanin yau suna zuwa ne da fuska mai girman, tare da fasahar latsawa don samun sakamakon ma’amala.  Wannan shi ake kira: “Touch calibration”.  Idan ka latsa alamar dake fuskar wayar, sai abin da kake so ya bayyana.  Idan kira ne, kana latsa lamba ko sunan dake wakilar lambar wayar, nan take za a fara kiran wanda kake son magana dashi, muddin akwai kuɗi a kan layin.

Sikirin ɗin wayar salula irin ta zamani nau’i biyu ne.  Akwai nau’in Liquid Crystal Display (LCD), da kuma nau’in Light Emitting Diods (LED).  Waɗannan nau’ukan sikirin basu taƙaitu ga wayoyin salula kaɗai ba.  A taƙaice ma dai, an fara amfani dasu ne a talabijin na zamani.  Daga baya ne aka fara ɗora su kan wayoyin salula.  To meye bambancin dake tsakaninsu, kuma meye tasirin kowanne wajen sanya wayar salula ta zama mai tsada ko araha?

Sikirin nau’in LCD dai nau’i ne na fuskar wayar salula dake karɓan haske daga bayansa.  Ma’ana, idan wayarka na ɗauke da sikirin nau’in LCD ne, to duk abubuwan da kake gani akan sikirin ɗin na haske, ba daga asalin sikirin ɗin bane.  A a.  Hasken na harkowa sikirin ɗin ne ta bayansa.  Aikin sikirin ɗin shi ne bayyana hasken dake ɗarsuwa daga baya, ta amfani da wata fasaha mai suna: “Light Shining Filter” (LSF).  Abin da wannan ke nufi shi ne, ba dukkan hasken dake zuwa daga bayan sikirin ɗin bane kake gani.  Wancan rariya mai suna “Light Shining Filter”, ita ce ke tace hasken.  Wannan ke sawwaƙe maka ganin nau’ukan launuka daban-daban masu cakuɗe da haske.

Dukkan wayoyin salula masu amfani da sikirin nau’in LCD suna sarrafa haske da launi ne ta amfani da fasahar “In-Plane Switching”, wato: “IPS”, ko kuma “Plane to Line Switching”, wato: “PLS”.  Kamfanin Samsung na amfani da fasahar PLS ne, yayin da sauran kamfanonin ƙera wayar salula ke amfani da fasahar IPS – musamman su Tecno da Infinix da kuma iTel.  Sikirin masu amfani da fasahar IPS/PLS sun fi sauƙin ma’amala idan kana amfani da wayarka a cikin rana ne.  Amma suna da naƙasa wajen nuna launuka masu armashi.  Domin asalin hasken da sikirin ɗin ke amfani dashi ba daga gareshi kai tsaye yake ba.  Yana ɗarsano haskensa ne daga baya.  Don haka, launin baƙi a wayoyi masu amfani da fasahar IPS/PLS yana bayyana ne da cakuɗen haske a tare dashi.   Haka ma sauran launuka suke.  Kuma kasancewar hasken na bayyana ne da’iman, sikirin nau’in IPS/PLS sun fi cin batir; ma’ana cajinsu ya fi saurin ƙarewa.  Domin kullum a kunne suke.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.