Sakonnin Masu Karatu (2018) (9)

Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

162

Assalamu Alaikum da fatan kana cikin koshin lafiya amin.  A gaskiya yau na fara rubuto sako gareka, da fatan Allah ya ba da ikon amsawa.  Tambayata ita ce: Kwamfuta ce take saurin cinye cajin battery a kodayaushe.  Idan na sanya batir din a wata kwamfutar sai ya dade fiye da yadda yake dadewa a kwamfutar.  Ina bukatar karin bayani, na gode.  Daga Sagir Kmwdutse:  sageerm17002@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Sagir.  Da fatan kana lafiya.  Duk da cewa baka bayanin wace irin kwamfuta bace, kuma wace irin babbar manhaja ce a dauke a kan kwamfutar, ga alama akwai abubuwan dake cinye batirin.  Kamar yadda na fada a farko, zan so sanin wace irin babbar manhajar kwamfuta ce?  Tunda babu bayani kan hakan, zan yi bayani kan abubuwan dake cinye batir a kwamfuta, sannan a karshe in ba da shawarar abin da nake ganin zai iya zama maslaha.

Abu na farko dake cinye batir dai shi ne yawaitar manhajoji a bude a lokaci daya.  A duk sadda ka bude manhaja a kan kwamfuta, kwamfutar za ta yanko wa wannan manhaja mahalli a ma’adanar wucin gadi (RAM).  Idan ire-iren wadannan manhajoji suka yawaita a bude, to, aikinta na karuwa matuka kuma tana jan makamashi mai yawa; iya gwargwadon abin da manhajojin suke bukata.

Abu na biyu su ne yawa da nau’ukan manhajojin da kwamfuta ke motsar dasu a yayin da aka kunnata.  Wadannan su ake kira: “Autostart Applications.”  Wannan ya kebance babbar manhajar kwamfuta ta Windows ce.  Hikimar ita ce, a duk sadda ka bukaci ire-iren wadannan manhaja, nan take sai kwamfuta ta baka su, tunda an riga an motsa su.  Ire-iren wadannan manhajoji na kamfanin Microsoft ne; musamman manhajar “Internet Explorer” ko “Microsoft Edge”, da manhajar “Microsoft Office” (irin su “Word”, da “Excel”, da  “PowerPoint” da dai sauransu).

Abu na uku su ne kananan manhajoji masu suna “Processes and Threads”, wadanda manhajoji ne kanana, wadanda saiwowin manyan manhajojin dake kwamfuta ne.  Aikinsu shi ne gudanuwa a karkashin kwamfutar, suna raya wadancan manhajoji, ko ba a kunna su ba.  Idan wadannan manhajoji suka yawaita a karkashin kasa, ko da kwamfutar a ajiye take ba a amfani da ita, kuma ba a jone take da wutar lantarki ba, suna iya cinye batir.

Abu na hudu shi ne hasken fuskar kwamfutar, wato: “Screen Brightness.”  Idan kwamfuta tana kan batir ne, iya gwargwadon hasken da ke fuskarta iya gwargwadon makamashin da take ci.

Abu na biyar shi ne adadin manhajoji da ke kan kwamfuta.  Idan kwamfuta tana dauke da manhajoji dari misali, ta fi wacce ke dauke da manhajoji hamsin cin batir.  Abin da zai baka mamaki shi ne, ko da ba a kunne suke ba, kwamfuta tana tanada musu mahalli a ma’adanarta, sannan duk sadda aka kunna ta sai ta kididdige dukkan bayanan dake dauke a kanta.  Wannan ma aiki ne na musamman.

Abu na shida shi ne amfani da manhajar bidiyo a kan kwamfuta.  Nau’ukan bayanai da kwamfuta ke mu’amala dasu dai su ne: tsagwaron bayanai (texts), da sauti (audio), da hotuna (images/pictures), da bayanan bayanai (metadata), sai kuma bidiyo (videos/motion images).  Daga cikin wadannan gaba daya, bayanan bidiyo sun fi sauran cin batir a kwamfuta.  Saboda kowane bidiyo na dauke ne da hoto, da sauti, da kuma tsagwaron bayanai.  Shi yasa ko wajen mu’amala da Intanet ne, bidiyo ya fi jan data.  Don haka, amfani da bidiyo akan kwamfuta, dole za ta ja batir sosai, sabanin idan kana amfani da tsagwaron bayanai ne zalla ko na hotuna ko sauti.

Abu na bakwai wanda za mu dakata a kai, shi ne amfani da Fasahar Intanet.  Idan kwamfutarka tana kan batir kuma ka kunna siginar Intanet, ba za ta dauki tsawon lokaci ba kana amfani da ita sabanin idan kana rubutu ne da manhajar Word ko Excel misali.  Dalili kuwa shi ne, amfani da fasahar Intanet na dauke ne da abubuwa da dama.  Na farko dole kwamfuta ta bukaci makamashin manhajar lilo, wato: “Browser” Kenan.  Domin da wannan manhajar ake amfani.  Abu na biyu shi ne bukatuwar makamashin lantarki don amfani da siginar rediyo kafin isa ga Intanet.  Abu na uku shi ne, aikin musabayar bayanai da kwamfuta ke yi tsakaninta da kwamfutar dake daya bangaren.  Wannan shi ma yana bukatar makamashin lantarki mai yawa.  A takaice dai wadannan su ne shahararru cikin abubuwan da ke cin batirin kwamfuta.

- Adv -

A daya bangaren kuma akwai yanayin mizanin batiri.  Batir martaba martaba ne, ko mataki mataki ne.  kowanne da irin mizaninsa.  Idan mizanin batirinka karami ne kuma masarrafar bayanan kwamfutarka (System Processor) mai girma ne, zai yi wahala kwamfutar ta jure.  A daya bangaren, kowace babbar manhaja (Operating System) tana da siffofinta daban. Misali, babbar manhajar Windows XP ta fi karancin bukatar makamashi idan aka kwatanta ta da babbar manhajar Windows Vista.  Haka bangaren Windows 7 yake da Windows 8.  A nata bangare, babbar manhajar Windows Vista ta fi sauran cin makamashi.  Hakan ya faru ne saboda yawan kyale-kyalen da kamfanin Microsoft ya zuba mata, ga rashin nagarta, ga yawan kananan masarrafai masu gudanuwa a karkashin kasa.  Wannan yasa bata yi wani tsawon lokaci ba a kasuwa kamfanin ya canza ta da Windows 7.

Don haka, shawarata a nan ita ce; kayi nazarin manhajojin dake dauke a kan kwamfutar, sannan ka kwatanta su da wadanda ke dayan kwamfutar.  Sannan kayi la’akari da mizanin kwamfutar wajen masarrafa.  Idan tana da babbar masarrafar bayanai (Processor), dole ne ta bukaci kayan aiki sosai.

Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa.  Da fatan ka gamsu.  Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan alheri a gareka da iyalanka.  Sakon gaisuwa daga Garba Sabiyola Gashu’a:  muhammadgarba8383@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Ina godiya matuka Malam Garba.  Allah saka da alheri ya kuma bar zumunci.  Na gode.  Na gode.  Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadik, hakika wannan fili naka yana ilmantar damu sosai.  Allah ya ba da lada.  Shin, mene ne amfani “Wi-Fi” a wayar salula, kuma yaya ake amfani da wannan tsari na sadarwa?  Sako daga Aminu Adamu Malammadori, jihar Jigawa: 07064880092 – aminuadamummr@gmail.com.

Wa alaikumus salam Malam Aminu, barka da warhaka.  Abin da Kalmar “Wi-Fi” ke nufi shi ne, “Wireless Frequency Radio,” kuma tsari ne dake killace a cikin yanayin sadarwa na zamani.  Idan kana son ganin wannan tsari a wayarka mai dauke da babbar manhajar Android, ka je: “Settings”, a bangaren “Network Connections” za ka ga wannan tsari, sai ka kunna shi.  Idan akwai na’urar Wi-Fi a inda kake, nan take wayarka za ta sanar da kai cewa: “Akwai tsarin sadarwar Intanet a nan, ta hanyar Wi-Fi.  Shin, kana a son a jona ka da shi?”  Idan kace eh, sai a jona ka.  To amma sai dai ba dukkan tsarin Wi-Fi yake kyauta ba.  Galibin wuraren da za ka je ka ci karo da wannan tsari za ka samu na wasu kamfanoni ne ko hukumar gwamnati, wanda dole sai an saita maka ta hanyar shigar da wasu kalmomi na sirri da suka kebanci kamfani ko hukumar da ke dashi.

Daga cikin amfanin tsarin “Wi-Fi” shi ne, kana iya jonuwa da yanayin sadarwa na Intanet a duk inda tsarin yake.  Haka idan kana na’urar Router, wacce ke dauke da wannan tsari a gidanka, kana iya amfani da tsarin a wayarka don amfani da Intanet ba tare da matsala ba, muddin ka sayi “Data” daga kamfanin sadarwar da ya sayar maka da na’urar “Router” din.

Bayan tsarin “Wi-Fi” da ake amfani da shi wajen hawa Intanet, akwai nau’I na biyu mai suna: “Wi-Fi Direct,” wanda ke taimakawa wajen aikawa da sakonni masu babban mizani, daga wayar salula zuwa wata wayar salular.  Misali, kana iya aikawa da sako na hoto ko bidiyo ko sauti mai mizanin 1GB, a kasa da minti biyu ko uku.  Galibi ana samunsa a wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Android.  Kuma shi kyauta yake, ba a bukatar biyan ko sisi ko sayan “Data”, domin an yi shi ne don aikawa da sakonni kai tsaye, a tsakanin wayoyin salula.   Kuma ko da babu katin SIM a wayar salula, kana iya amfani dashi.

Wannan shi ne dan abin da ya samu.  Kuma da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.