Abubuwan Lura Cikin Sabuwar Dokar NITDA (1)

A sashe na 1, sakin layi na 5 na wannan sabuwar doka, an tabbatar da cewa duk wanda ya dauko sakon da wani ya wallafa, wanda asalin mai sakon ba a Najeriya yake ba, to, wanda ya yada wannan sako, muddin ya saba doka, zai zama shi ne mai laifi. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 5 ga watan Agusta, 2022.

350

Bayan tsokaci da bayanai kan bangarorin da wannan sabuwar doka ta kayyade tsarin ma’amala da kafafen sadarwa, a yau za mu dubi wasu bangarorin dokar da ke bukatar Karin bayani ko Karin fayyacewa ko ma cirewa in ta kama, don tabbatar da an samu doka mai ma’ana, wacce za ta kiyaye hakkokin dukkan bangarorin masu amfani da wadannan kafafe na sadarwa a wannan kasa tamu.  Domin a yayin da gwamnati ke kokarin bayar da kariya ga ‘yan kasa, kamar yadda dokar ke riyawa, a bangare daya, a dayan bangaren kuma dole ne ta lura da hakkokin wadannan kafafe, da irin kokarin da suke yi wajen kayyade masu ma’amala da shafukansu, kamar yadda makalarmu ta makon shekaranjiya ta tabbatar.  Wadannan abubuwan lura dai su ne:

Yada Sakonnin Wasu

A sashe na 1, sakin layi na 5 na wannan sabuwar doka, an tabbatar da cewa duk wanda ya dauko sakon da wani ya wallafa, wanda asalin mai sakon ba a Najeriya yake ba, to, wanda ya yada wannan sako, muddin ya saba doka, zai zama shi ne mai laifi.  Misali, idan wani dake kasar Jamus ya dora sako kan wani abin da ya shafi Najeriya, ko wani dan Najeriya, ko wata hukumar Gwamnati, wanda ya saba ma wannan doka ta NITDA ko dokoki makamantanta, sai wani dake nan Najeriya ya yada (share) wannan sako a shafinsa, to, za a dauka shi ne asalin mai sakon.  Kenan idan laifi ne, to, shi ne yayi laifin.

Ta wannan bangare hakan zai taimaka wajen ragewa yaduwar sakonnin karya da na bogo.  Idan muka sake kallon yadda tsarin wallafa sakonni a wadannan kafafe a halin yanzu, za mu ga wannan sabuwar doka za ta takura jama’a musamman masu kokarin fadakar da mutane wasu daga cikin miyagun bayanan da ake wallafawa a wadannan kafafe.  Misali, da yawa cikin mutane kan nakalto ko yada wasu sakonni masu dauke da hadari, amma da niyyar fadakar da mutane ne, ba wai don sun yarda da gundaken abin da ke dauke cikin sakon ba.  Sannan galibin mutane ba sa yin Karin bayani, sai dai kawai sun tunkudo sakon kai tsaye.  Dole ne wannan doka ta sanya kaidi tsakanin masu tunkudowa don sun yarda da sakon, da masu tunkudowa don fadakarwa ko kafa hujja.

Wace Kotun?

Daga farko har karshen wannan sabuwar doka, an ta maimaita Kalmar “kotu”, ba tare da bambancewa ba, ko Karin bayani kan darajar kotun ba.  Abu ne sananne cewa kotuna sun sha bamban wajen martaba da matsayi.  Ba kowace kotu ke saurare tare da yin hukunci kan kowane irin laifi ba.  Amma a wannan sabuwar doka, an ambaci cewa “kotu” na iya neman bayanai wajen kamfanonin sadarwa na zamani kan wani sako, ko wanda ya wallafa sakon, amma ba ayi bayanin nau’in kotun ba.  Shin, kotun Shari’ar musulunci ce, ko babban kotun fedara ko na jiha (Federal/State High Court), ko kotun daukaka kara na jiha ko fedara (Appeal Court), ko kotun Shiyya (Area Court)?  Duk babu bayani kan hakan.  Yana da kyau hukumar NITDA ta yi Karin bayani kan irin kotun da ita ce kadai za ta iya neman bayanai, da sauraren kara ko yin hukunci kan ire-iren wadannan al’amura da suka shafi laifuka daga kafafen sadarwa na zamani.

Bukatar Neman Bayanai

- Adv -

A cikin wannan doka, anyi bayanin nau’in bangarori uku da za su iya zuwa kotu don neman a tilasta wani kamfanin sadarwa na zamani ya bayar da bayanai ko Karin bayani ko bayyana hakikanin mawallafin wani sako.  Wadannan bangarori kuwa su ne: hukumar gwamnati, da daidaikun mutane, da kuma kungiyoyi.  A bangaren daidaikun mutane akwai masu rajista, da kuma marasa rajista.  Inda matsalar take shi ne, kamfanin sadarwa na zamani na iya sauraren koke daga wadanda ke da rajista dashi ne, wadanda suka bude shafi kuma suka amince wa dokokin da ya gindaya.  Mutane irin wadannan kam dole ne kafar sadarwa ta kalli kokensu, ta kuma saurari kotu ko umarnin kotu wajen bukatarsu.  Amma wanda bai yi rajista da kafarsu ba, akwai takura ace dole sai wata kafar sadarwa ta saurare shi, ko saurari koken kotu kan bukatarsu.

Misali, kafar sadarwa ta Youtube, inda jama’a ke wallafa sakonnin bidiyo, wuri ne da ko ba ka da rajista za ka iya gani, da kallo da kuma ta’ammali da wadannan sakonni.  Kana ma iya sauke su zuwa kan wayarka ko kwamfutarka.  Idan mai wannan aiki ya tashi kai korafi ga Youtube, babu hanyar da zai iya bi dole sai ya yi rajista da shafin.  Haka sauran kafafen sadarwa suke; ba ka iya kai musu korafi su saurareka sai kana da rajista dasu.

Masu Amfani da Virtual Private Network (VPN)

Lokacin da kamfanin Twitter ya kulle shafin shugaban Najeriya, wanda hakan yayi sanadiyyar kulle shafin ga ‘yan Najeriya baki daya.  Wannan bai hana wasu daga cikin ‘yan Najeriya amfani da shafin ba, ta amfani da manhajar Virtual Private Network (VPN).  Tsarin VPN dai hanya ce dake bai wa mutane damar isa ga wani shafi na Intanet da aka hana, ta hanyar canza adireshin waya ko kwamfutarka da wata adireshin daban.  Misali, idan adireshin wayar salularka 192.113.19.211 ne, da zarar ka jona tsarin VPN, za a baka wata sabuwar lambar, wacce ke dauke kan wata kwamfuta dake wata kasar da ba a hana ta hawa shafin ba.  Wannan zai sa ka isa kan shafin kai tsaye.  kuma ko da anzo bincike, ba za a ga lambar waya ko kwamfutarka ba; wancan lambar za a gani, daga wata kasa daban.

Tambayar ita ce, idan wasu ‘yan Najeriya dake Najeriya suka yi amfani da tsarin VPN suka bude shafi, suka wallafa wasu sakonni da suka saba wa wannan doka, ta wace hanya hukuma ko wadannan kafafen sadarwa za su iya tantance su, bare su gurfanar dasu a gaban kotu?  Wajibi ne wannan doka tayi bayani kan hakan, don kada wasu su rika amfani da wannan tsari ko hanya ta VPN don cin zafin wasu.

Sassauci Cikin Doka

Galibin masan da suka yi nazarin wannan sabuwar doka sun nuna cewa lallai akwai bukatar hukumar NITDA ta sake bitar wannan doka.  A tare da cewa hukumar ta tuntubi sauran kafafen sadarwa kafin hada wannan doka, har yanzu akwai abubuwa da dama da suka kamata ta sake dubawa don tabbatar da sassauci cikin dokar.  Wannan zai taimaka wajen samar da gamammen tsari da amincewa tsakanin masu ruwa da tsaki baki daya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.