Yadda Aka Kera Jirgin Ruwan “RMS Titanic” (1)

Shirin Fim din “Titanic” ya shahara matuka, har ta kai ga da yawa cikin mutane sun dauka kirkirarren labari ne kamar sauran mafi yawancin fina-finai. Wannan yasa naga dacewar gudanar da bincike don fahimtar damu cewa labari ne tabbatacce ba kirkirarre ba. Kalmar “Titanic” da aka baiwa shirin, sunan wani jirgin ruwa ne da aka kera mai girman gaske tsakanin shekarar 1909 zuwa 1912. A sha karatu lafiya.

1,671

Shahara

Cikin shekarar 1997 ne kamfanin shirya fina-finai na 20th Century Fox da ke Amurka, ta hadin kai da wasu kamfanoni ‘yan uwansa suka fitar da wani fim mai suna “Titanic”, wanda ya samu shahara fiye da sauran fina-finan da aka fitar cikin shekarar.  Wannan fim na “Titanic”, wanda shahararrun ‘yan wasa irinsu Leonardo DiCaprio, da Kate Winslet suka fito a ciki, ya yi suna musamman a tsakanin matasa masu sha’awar jigon soyayya a cikin fina-finai.  Wannan a bayyane yake.  Ba ma a kasashen Turai da Amurka inda aka shirya fim din kadai ba, hatta a nan gida Nijeriya wannan fim ya samu shahara sanadiyyar wannan jigo na soyayya da aka tsofa cikin fim din; inda jarumi Leonardo DiCaprio, da kuma jaruma Kate Winslet suka narke cikin kogin soyayya.  Bayan haka, editan fim din shi ma wani sananne ne wajen sana’ar, wato James Cameron.  A takaice dai, an sayar da kwafen fim din na gundarin kudi da kimarsa ta kai dalar Amurka sama da biliyan daya da dubu dari takwas.  Kuma har zuwa yau, shi ne fim da aka kashe kudi wajen yinsa fiye da kowane fim a duniya.

Sai dai kuma, sabanin wannan jigo na soyayya da ke cikin wannan fim, wani abin da ya fi kama hankalin wasu cikin masu kallo – musamman masana Kimiyyar Kere-kere –  shi ne tarihin da ke tattare da wannan jirgin da dukkan wannan lamari ya faru a cikinsa.  Da farko dai, wannan lamari ya faru ne cikin shekarar 1912, a cikin wani tafkeken jirgin ruwa mai suna RMS Titanic da kamfanin White Star Line na kasar Ailand (Ireland) ya kera tsakanin shekarar 1909 zuwa 1912.  Sanadiyyar girma da kayan alatun da ke cikin wannan jirgin ruwa, da kuma cewa babu wani jirgin ruwan fasinja mafi girma kamarsa a lokacin, tasa aka shirya wannan shiri, daidai lokacin da wannan lamari na hadarin jirgin yake cika shekaru 85 (1912 – 1997).

A halin yanzu akwai buraguzan wannan jirgi na RMS Titanic a karkashin teku, kuma masana kan ilimin karkashin kasa da teku sun yi hasashen cewa nan da shekaru hamsin masu zuwa buraguzan za su dangana da gundarin kasan tekun baki daya, wato Ocean Floor.  A yau in Allah Ya so za mu dubi yadda aka kera wannan jirgin ruwa, da wadanda suka zana shi, da kuma yadda aka yi wannan lamari ya faru.

Asali

Kamfanin kera jiragen ruwa mai suna White Star Line da Harland & Wolff da ke kasar Ailand ne suka kera wannan tafkeken jirgin ruwan fasinja mai suna RMS Titanic.  Sun yi wannan aiki ne a filin kera jiragen ruwa da suke dashi a birnin Belfast na kasar Ailand din.  Kuma hakan ya faro ne cikin shekarar 1909.  Kafin wannan shekara, wannan kamfani na White Star Line ya fara kera wasu jirage masu girma wadanda ya sanya wa suna Olympic, sannan yayi kudurin kera wasu manya na musamman, masu dauke da kayan alatu na kasaita, wadanda kuma babu kamarsu a wancan zamani – wajen girma, da kayan alatu, da fasahar kere-kere da kuma tsarin sadarwa.  Asalin sunan da wannan kamfani yayi niyyar baiwa wannan jirgi na Titanic dai shi ne “Gigantic”; ma’anarsu daya ne da “Titanic”.

- Adv -

Wannan jirgi na Titanic dai an kera shi ne da mafi kwarewar kwarewa na zamanin, ta amfani da kwararrun injiniyoyin lokacin, da kuma mafi kwarewar fasahar kere-kere na lokacin.  Bayan dukkan wannan, shi ne jirgin da yafi girma a lokacin; domin bayan mutum dubu uku da dari biyar da arba’in da bakwai (3,547) da yake iya dauka, har wa yau yana iya daukan jirgin sama nau’in Airbus 380 guda daya,  da manyan motoci nau’in bas, da kuma kanana.  A takaice dai, wannan jirgi na iya daukan kaya da mutanen da nauyinsu ya kai tan 46,328.  Kamfanin J.P.Morgan da International Mercantile Marine Company ne suka dauki nauyin kera jirgin.  Ma’ana su suka bayar da kudade da kayan aikin da ake bukata don kerawa.

Injiniyoyi

Jirgin ruwan Titanic ya samu albarkar manya da kuma shahararrun injiniyoyin fasaha da kere-kere na wancan zamani.  Akwai mutum uku da suka dauki nauyin zana tsari da kira da kuma yanayin rayuwar wannan jirgi.  Na farko shi ne Lord Pirrie, wanda Darakta ne a kamfanin Harland Wolff da White Star Line.  Sai wani kwararren mai zanen jiragen ruwa mai suna Architect Thomas Andrews, wanda shi ne manajan kere-kere na kamfanin, wato Construction Manager kenan.  Sai na ukunsu, wato Alexander Carlisle, wato babban manajan ma’aikatan kera jirgin ne baki daya (Shipyard General Manager).

Tsarin Kira

Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, asalin sunan da aka so baiwa wannan jirgin ruwa da farko dai shi ne “Gigantic”, to amma daga baya sai kamfanin White Star Line ya canza wannan suna saboda wasu dalilai.  An fara kera jirgin ne a shekarar 1909. Cikin shekarar 1911 ne kuma aka gina mazauninsa, wato kwarangwal din da gaba dayan jikinsa ke zaune a kai.  Wannan shi ake kira “Hull” a turancin kere-keren jirgin ruwa.  Sauran gangar jikin jirgin, da kayan alatun makale-makalen cikinsa kuma an gama su ne a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 1912.

Wannan jirgi na Titanic yana da tsawon kamu 882 ne da inci 9, kuma zai iya daukan kayan da nauyinsa ya kai tan 46,328.  Akwai injina manya wadanda ruwan zafi ke sarrafa su (wato Steam Engines) tafka-tafka guda hudu.  Akwai bututun salansa masu fitar da hayakin injin guda uku, da kuma guda daya mai samar da iska ga jirgin.  Dukkan wadannan bututu kowannensu ya kai tsawon kamu 62.  A kasan jirgin kuma akwai wasu bututun amayar da ruwa guda takwas da aka tanade su, wadanda kuma aka kiyasta cewa suna iya amayar da ruwa daga cikin jirgin (idan matsala ta kama) sama da galan 420,000 cikin awa guda.  Aikinsu shi ne amayar da dukkan wani ruwa da ya shigo cikin jirgin daga kasa.

Zan ci gaba mako mai zuwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.