Satar Zati a Kafafen Sadarwa Na Zamani (3)

Ga kashi na uku cikin binciken da muke kan Satar Zati. A wannan mako mun dubi nau’ukan Satar Zati ne.

284

Nau’ukan Hanyoyin Satar Zati

Kamar yadda nayi bayani wajen bayar da ma’anar wannan tsari na ta’addanci a farkon wannan kasida, cewa masu sacewa ko tattara bayanan jama’a don aiwatar da wannan aiki suna yi ne don wata manufa ta musamman.  Manufofin masu wannan sana’a dai sun sha bamban, tsakanin nau’ukan jama’a da kuma kasashensu.  Misali, manufar masu yi a kasashen da suka ci gaba, ta sha bamban da na masu yi a arewacin Najeriya ta hanyar Dandalin Facebook.  Manufar masu yi a kasar Rasha, ta sha bamban da na masu yi a kasar Jamus, misali.  A halin yanzu ga nau’ukan wannan tsari na Satar Zati nan, ta la’akari da manufar masu yi.

Identity Cloning and Concealment

Wannan nau’in Satar Zati shi ake kira: “ID Cloning” a gajarce, ko kace “Satar Zati ta Karkashin Kasa.”  Kuma abin da ya kunsa shi ne, bayan an tattara bayan da suka shafeka, sai ayi amfani dasu wajen kera wani zati na musamman, a makwafinka. Misali, idan kana da katin shedar zama dan kasa, sai wani ya samu sunanka, da adireshin gida da wurin aikinka, da shekarar haihuwarka, da tsayinka, da nau’in jininka, da launin kwayar idonka, sai ya kera wani katin shedar zama dan kasa mai dauke da hotonka, irin naka.  Daga nan sai ya yi ta amfani dashi wajen aiwatar da abubuwa a kafafen sadarwa.

Wannan nau’i na Satar Zati an fi amfani dashi wajen buya daga hukumar shigi-da-fici na kasashen da suka ci gaba.  Wato idan mutum ya shigo wata kasa ta haramtacciyar hanya, sai ya kirkiri irin wannan kati na bogi kawai, yayi ta sharholiyarsa.  Wasu kuma kan kirkiri katin don guje wa wadanda ke binsu bashi a kafafen sadarwa ta hukuma.  Misali, mutum ne ke dauke da katin bashi (Credit Card) da wani banki ya bashi, yayi cinikayya masu yawa da katin, bashi ya taru masa.  Sai ya daina amfani da katin ya kirkiri wannan kati na bogi, yana amfani dashi.  Idan matsala ta auku, kai za a nema, don shi babu wanda ya sanshi.

Bayan wadannan hanyoyi biyu, akwai amfani da wannan tsari a dandalin sada zumunta, inda zasu bude shafi da sunan wani shahararren mutum, su dora hotonsa da bayanansu duka, amma suna aiwatar da wasu abubuwa haramtattu ta karkashin kasa, ba tare da saninsa ba.  Masu wannan nau’i a dandalin sada zumunta su ake kira:  “Posers”.  Wannan ya fi shahara a bangarenmu nan.

Criminal Identity Theft

Wannan shi ne nau’in Satar Zati da ake kirkira don aiwatar da ta’addanci – kamar sata, ko kwace, ko kisa da dai sauransu.  Masu wannan aiki kuma za su sace bayanan jama’a ne, sai su kirkiri irinsa na bogi, kamar na farko.  Amma baza su yi amfani dashi ba sai sadda jami’an tsaro suka kama su sanadiyyar wani ta’addanci da suka aikata.  Misali, irin kisa, ko sata, ko kwace, ko laifukan ta’ammali da miyagun kwayoyi da dai sauransu.  Da zarar an kama su, sai su nuna wannan kati mai dauke da suna, da kwanan watan haihuwa, da adireshi, da unguwa, da sana’a, na wani daban, ba asalin nasu ba.  Da wadannan bayanai za a kai su kotu, da shi za a musu hukunci kuma dashi za a kaisu Gidan yari, idan hakan ta kama.  Kuma nan take hukuma za ta dora tambari a kan wadannan bayanai a taskar bayananta, wanda ke nuna cewa mai wadannan bayanan, dan ta’adda ne.

Matsalar ba ta fitowa fili sai sadda asalin mai bayanan yaje zai aiwatar da wani ciniki, ko wata hulda da hukumar gwamnati, ko kuma aka yi rashin sa’a barawon ya gudu daga hannun jami’an tsaro, da zarar an je nemansa, za a nufi Gidan dake dauke da adireshin dake katinsa ne.  Kai kuma kana zaune a gida lafiya kalau, sai kawai kaga jami’an tsaro sun zo suna muzurai, wai kai mai laifi ne, domin ka gudu daga hannun jami’an tsaro, ko kuma bayanai sun nuna ka yi laifi kaza.  Ga lambarka ta shedar zama dan kasa, ga hotonka, ga adireshinka;  yaya Kenan?  Kaka-tsara-kaka!

A kasashen irin su Amurka da Ingila dai, wannan shi ne mafi muni daga cikin nau’ukan Satar Zati.  Domin wanda aka yi amfani da bayanansa wajen aiwatar da wadannan ayyuka munana har hukuma ta dora tambari a kan sunansa a taskarta na bayanan ‘yan kasa, da wahala ya tsira.  Idan haka ta faru, dole sai kai, a matsayinka na wanda aka saci zatinsa, ka je wajen jami’an tsaro ka barrantar da kanka, cewa ba kai bane.  Hakan kuwa bai yiwuwa da fatar baki.  Sai ka je kotu ka yi rantsuwa cewa ba kai bane.  Sannan za a dauki tambarin hannunka (Thumbprint) da sinadaran jininka don yin gwajin siffofi da dabi’un halitta (DNA Test), wadanda za su tabbatar wa hukuma cewa lallai ba kai bane wanda aka kama a baya, ko ba kai bane ka aikata wancan laifi.  Wadannan matakai ne masu wahala, domin kai ne za ka ta dawainiyar kashe kudin wajen hakan.  Ba ruwan hukuma.  Idan har hukuma ta gamsu cewa ba kai bane, to, nan take za a dauki asali bayananka sai a dora su akan wancan na bogin, ana ishara cewa kaine mai asalin bayanan.  Tirkashi!

Synthetic Identity Theft

Wannan shi ne nau’in Satar Zati na uku, wanda na kira: “Satar Zati na Bogi.”  Karkashin wannan nau’i da tsari, Barawon Zati kan tattaro bayanai ne, sai ya cakuda su da bayanan bogi da ba su da asali.  Misali, idan ya samu lambar katin tallafin kasa (Social Security Number), sai ya jona masa kwanan watan haihuwa na wani daban, ko na bogi, wanda ko an binciko katin ba za a iya gani ba, amma a hukumar lura da tallafin jama’a akwai shi.  Masu aiwatar wannan nau’i na Satar Zati dai suna yi ne don yin cuwa-cuwa wajen samun tallafin hukuma da take baiwa marasa aikin yi a kasashen da suka ci gaba, musamman kasar Amurka.

Medical Identity Theft

- Adv -

Karkashin wannan nau’i na Satar Zati dai, Barawon Zati na amfani da bayanan wasu ne don samun damar karbar tallafin kiwon lafiya kyauta, idan shi ba shi dashi ko kuma kimar tallafinsa ya kare.  Wanda ya kirkiri wannan kalma dake wakiltar wannan nau’i na Satar Zati dai shi Pam Dixon, wanda kwararre ne a fannin sirrin bayanan sadarwa na jama’a.  Suna yin hakan ne ta hanyar satar lambobi ko bayanan Inshoran Lafiya (Health Insurance Number) na mutane, sais u dora sunayensu a kai, don samun tallafin da mai asalin lambar ke samu, ba tare da saninsa ba.  Bincike ya nuna masu aikata manyan laifuka a kafafen sadarwa na zamani don manufar tattalin arziki sun fi son wadannan irin bayanan, fiye da lambobin katin tallafin hukuma na jama’a.

Idan kayi rashin sa’a aka sace wannan lamba dake wakiltar tallafinka na Inshoran lafiya, to, duk sadda barawon yaje asibiti yaga likita, kai za a caja kudin hidimar da aka masa, ko nawa ne kuwa.  Wannan nau’i dai ya shahara ne a kasashen dake da tsarin Inshoran lafiya, wato: “Health Insurance Scheme.”  A Najeriya an fara amfani da wannan tsari musamman ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.  Don haka, sai ayi hattara.

Child Identity Theft

Wannan shi ne nau’in Satar Zati da ya shafi bayanan kananan yara.  A kasashen da suka ci, hatta kananan yara suna da wani tallafi na musamman da hukuma ke basu.  A katinsu, wanda ke dauke da bayanansu, babu wasu bayanai masu yawa.  Don haka Barayin zati kan sace bayanan, su alakantansu da kansu, don neman bashi daga hukumomin gwamnati, ko bankuna, ko lasisin tukin mota, ko sayan gida.  Babbar matsalar dake tattare da wannan nau’i na Satar Zati dai shi ne, ba a iya gane wani ya faru ma sai bayan shekaru masu dimbin yawa.  Musamman ganin cewa kanan yara ba a cika damuwa da bayanansu ba.  Daya daga cikin kwararru wajen gano wani ta’ada mai suna Richard Power dake cibiyar bincike ta Carnegie Mellon Cylab, ya tabbatar da cewa bayanan yara sama da dubu arba’in (40,000) ne Barayin zati suka ce don aiwatar da nau’ukan ta’addanci daban-daban.

Financial Identity Theft

Sai wanda ya shafi harkar kudi zalla, wato: “Financial Identity Theft.”  Wannan shi ne wanda ya shafi tsarin satar bayanan mutane don manufar samu wata fa’ida da ta danganci kudi.  Misali, masu sace lambar katin bashin (Credit Card) mutane, suyi ta sayen kayayyaki dasu ana cajan mai katin kai tsaye.  Da masu satar bayanan don cin bashi a banki ko hukumomin bayar da basuka, da sunan mai katin, ba da saninsa.  Ko kuma satar bayanan da yin amfani dasu wajen biyan wata bukata da ta shafi hidimarsu.  A irin wannan yanayi, ba shi da bambanci da wanda zai sace maka katinka na ATM, sai dai kawai kayi ta jin sakonnin ciran kudi na shigowa wayarka ta salula.  Za ka samu natsuwa?  Wannan nau’in ne kadai ke faruwa a Najeriya, musamman a manyan birane irin su Legas.  Ai wannan ma yafi na katin ATM hadari.  Domin wasu zasu je suci bashi ne da katin mai dauke da bayananka.  Kuma hukumar lura da basuka ta kasa (Credit Bureau) bata san kowa ba sai kai.  Idan ma sakon “ya isa haka” ake son aikowa, kai za a aiko wa kai tsaye.  Tunda adireshin gidanka ne akan katin.  Tirkashi!  Wata badakalar sai Turai.

Political & Religious Identity Theft

Wannan nau’i shi ne na karshe da za mu duba.  Kuma shi ne nau’in da yafi yaduwa a dandalin sada zumunta a arewacin Najeriya.  Tsarin Satar Zati Kenan don manufar siyasa ko addini.  Wannan ya faru ko ince yana ci gaba da faruwa a dandalin Facebook, kuma bayan manyan malamai da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa, yana shafin mata – matar aure da ‘yan mata.  A kan wannan nau’i na Satar Zati ne shirin “Ra’ayi Riga” na BBC ya ta’allaka.

Wannan nau’i na Satar Zati babban dalilin samuwarsa galibi shi ne hassada, da tsana, da gilli, da neman shahara ko suna, da kokarin samun yabo ba tare da cancanta ba.  Hakan na daukan fuskoki da dama.  Wani zai sace bayanan wani malami ne ko dalibin ilimi da yake ganin ya kai masa ko ina, ya kasa iya wargaje hujjojinsa.  Sai ya bude shafi da sunansa, da hotonsa, ya yada bayanai masu hadari, watakila ma masu alaka da abin da hukuma ba ta so.  Duk wanda ya gani zai dauka mai sunan ne yayi.  Kenan, za ayi ne don a hada shi fada da hukuma.

Wasu kuma kan bude shafuka ne da sunan ‘yan mata, su dora hotuna na batsa, a zuwan masu sunan shafin ne suka bude kuma suka zuba.  Sukan yi hakan ne don muzanta ‘yan matan.  Watakila saboda siyasar soyayya irin ta zamani.  Wasu kuma kan yi kutse ne cikin shafin ‘yan matan, su kwace shafin, suyi ta aikata abubuwa marasa kyau dashi.  Wannan shi yafi muni, domin asalin shafin mai shafin ne aka kwace.  Ka ga, da wahala mai shafin ya fid da kansa Kenan.

Daga cikin dalilai har wa yau akwai na siyasa.  Wani zai bude shafi ne da sunan wani dan siyasa ko mai masa hidima, ya watsa bayanan sabanin akidar mai sunan shafin, don nuna samuwar barakar da watakila babu ita. Ana hakan ne don cinma manufa ta siyasa mummuna.

Wasu kuma kan kwace shafin wani mutum ne mai mutumci, ko malami ko gama-garin mutum mai kima a idon mutane, mai jama’a.  Idan suka kwace sai su rika bibiyar abokanansa suna rokonsu cewa su turo masa katin waya ko a aika masa kudi, saboda ya samu kansa cikin wani matsatsari a wani wuri.  Wannan tsohuwar hanyar zamba ce da tayi suna a kasashen Girka da Ingila da sauran Kasashen Turai tun karnonin baya.  A shekarar 2017 ne wani daga cikin manyan malamai ya kira ni yake sanar dani cewa an kwace masa shafinsa na Facebook kuma barawon na can yana ta rokon abokansa cewa su tura masa kudi.  Bai san hakan ba sai da wasu suka kira shi suna tambayar lafiya?  Sai yace ai bai ma san abin da ke faruwa ba.

Wannan kadan ne cikin munin wannan hanya ta Satar Zati mai alaka da siyasar rayuwa da ta addini.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Abdullahi i.nuhu says

    Aslm Baban sadiq muna godiya Allah ya saka da alkhairi

Leave A Reply

Your email address will not be published.