Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.
Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da aiki. Kalmar “Hardware” da “Software” ya za mu fassara su da Hausa? Sannan kuma mene ne banbancin dake tsakanin “System software” da kuma “Application Software”? Muna godiya Baban Sadik da amsa mana…