Sakonnin Masu Karatu (2019) (22)

Kwarewa a Fannin Kimiyyar Kwamfuta

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na ranar Jumma’a, 6 ga watan Disamba, 2019.

89

Assalamu alaikum, gaisuwa da fatan alkhairi. Yarona ne ke son zama qwararren injiniya akan gyaran waya da kwamfuta. Shi ne nake son sanin matakan da suka kamata mubi tun daga matakin sakandare har zuwa jami’a, da irin kwasa-kwasan da suka kamata a dorashi don cimma burinsa na rayuwa. Yanzun haka yana karatu a cikin daya daga cikin Technical School a Katsina. Nagode. Abu Mus’ab, Kaduna. 08033602969

Wa alaikumus salam, barka ka dai Baban Mus’ab, godiya nake da fatan alherin da ake mini. Dangane da manufar dora danka a fannin ilimin da ya danganci injiniya na gyaran wayar salula, ina iya cewa wannan wani abu ne mai matukar mahimmanci. Na farko dai zai samu aikin yi kai tsaye. Na biyu zai zama mai daukan wasu aiki. Na uku, wanda yafi mahimmanci, shi ne zai rika koya wa wasu, har su kware kamar yadda yak ware shi ma. Samun irin wannan tsari da tafarki a aikace, musamman a wannan lokaci da muke fama da rashin aikin yi a kasarmu, abu ne da zai taimaka matuka wajen fitar da matasanmu daga kangin rashin aikin yi da zaman banza da kuma shaye-shaye.

Duk da cewa ban san kwasa-kwasan da wannan makarantar koyon sana’a dake Katsina take karantarwa ba, amma a jami’o’inmu bance akwai wani fanni na musamman don karantar da fannin gyaran wayar salula ba. Amma zai iya daukan fannin Computer Engineering. Fanni ne da ya shafi yadda kwamfuta ke aiki da yadda ake kwance ta da gyara ta da kuma kirkirar abubuwan fasaha daga gareta. Sai dai hakan ya danganci tsarin makarantar. Akwai jami’o’in da suke karantar da wannan fanni a aikace, wato a koya maka yadda komai ke gudanuwa da yadda kaima zaka aiwatar da karatun, ba wai a nazarce kaxai ba. Amma galibin makarantunmu suna karantar da ire-iren waxannan fannoni ne a nazarce, sai in dalibai sunyi sa’an malamin da zai fuskantar dasu ta hanyar basu ayyukan gida a aikace da sauransu dabarun qwarewa.

A tare da haka, shawara ita ce, ko ma wani irin fanni ya karanta, zai iya qwarewa a fannin gyaran waya sosai. Sirrin na cikin abubuwa guda uku ne. Abu na farko shi ne, ya zama yana da sha’awa kan fannin sosai. Wannan zai sa ya yawaita karance da mayar da hankali kan abin. Abu na biyu shi ne, ko dai ya samu qwarewa a makaranta ta musamman inda ake karantar da wannan fanni a aikace, ko kuma a nema masa wani qwararren mai gyaran waya inda zai koya a aikace. Abu na uku shi ne, duk wata na’ura ko kayan aiki da zai bukata, a saya masa. Wannan zai taimaka masa wajen kwatanta abin da yake koya ba tare da fargaba ba. Domin shi wannan fanni fa fanni ne da ke bukatar aikawata. Ba wai tsantsar karatu ke sa a kware a kai ba. Ba kamar fannin tarihi bane.

Wannan shi ne dan abin da zan iya bayarwa na shawarwari da fuskantarwa. Allah sa a dace, amin.

- Adv -

Assalamu alaikum, barka dai. Don Allah Abban sadik Ina son ka fada man shafin da zan rika saukar da manhajar kwamfuta kamar irin yadda akeyi a wayoyin salula na zamani ta hanyar cibiyar Playstore. Kuma don Allah ina son ka rubuto man sunan makarantar da zanyi karatu ta kafar Intanet. Na gode: abdulmalikhassandanmoyi@gmail.com. 08173472741

Wa alaikumus salam, Malam Abdulmalik. Da farko dai ina baka hakuri sanadiyyar kin daukan kiranka a lokuta daban-daban. Hakan ya biyon wasu dalilai ne guda biyu. Na farko shi ne, nace tes kawai za a rika aikowa a wannan layi. Idan kana da bukatar zantawa dani ka sanar dani ta tes, zan iya baka lokaci na musamman da zaka kira ni ko ni in kiraka sai mu tattauna in saurari bukatarka. Dalili na biyu kuma shi ne yanayin shagulgula dake gabana. Wannan yana cikin dalilan da suka sa kawai sakon tes nake karba a layin ba kira. Idan nace zan saurari kowa ya kira, to, bazan iya gabatar da komai nawa ba. In ka lura, tun cikin watan Yuli muke ta amsa tambayoyin masu karatu, har yanzu kuma bamu gama ba. Ka kaddara kira na kowanne daga cikin masu saqonnin nan yayi; yaushe zan iya biya wa kowa bukatarsa? A gafarceni.

Dangane da bukatarka kuma, ina son ka san cewa, tsari da kintsin wayoyin salula na zamani, da irin babbar manhajar da suke amfani dashi yasa aka samar musu da tsari na musamman wajen saukar da manhajoji masu tsafta kuma cikin sauqi, galibinsu ma kyauta. Amma kwamfuta bata samu wannan gatar ba. Tabbas akwai wuraren da za ka iya saukar da manhajojin kwamfuta kyauta, amma ba su da tsafta. Kuma suna iya cutar da kwamfutarka ko da kuwa kana da manhajar kariya daga kwayar cutar kwamfuta, wato: “Anti-virus”.

Akwai daidaikun shafukan Intanet dake xauke da manhajoji na kyauta zalla. Waxannan su ake kira: “Shareware” ko “Free Applications”. Galibin waxannan zaka samu suna xauke da tallace-tallace a soke a cikinsu. Idan kazo loda wa kwamfutarka, kuma aka yi rashin sa’a baka san kan abin ba, zaka yi kitso da qwarqwata. Sai bayan kwana biyu sai ka fara ganin wasu dabi’u marasa kan-gado da kwamfutarka ke nunawa. Ba komai bane illa kwaya tasha, wanda aka dura mata ta hanyar wadancan manhajoji na kyauta. Hausawa kance: “Araha ba ta ado”. Daga cikin shafukan da zaka iya samun waxannan nau’ukan manhajoji akwai shafin CNET (http://download.cnet.com), sai kuma shafin Softonic (http://en.softonic.com). Sannan akwai shafi na musamman inda za ka samu manhajojin da ba ka bukatar loda wa kwamfuta, wato: “Installing”. Su kawai manhajoji ne na tafi-da-gidanka. Amfaninsu galibi idan kayi aron kwamfuta ne, baka son loda manhajojin da kai kaxai ne zaka yi amfani dasu, ko kuma baka da damar da zaka iya loda manhaja, sanadiyyar karancin ‘yanci da aka baka. Hakan kan faru ga kwamfucocin da ofis ke baiwa ma’aikata. Akwai manhajoji na al’ada, gama gari (irin su Google Chrome, Mozilla Firefox da sauran makamantansu). Waxannan su ake kira “Portable Apps”. Idan ka saukar sai dai ka matsa, nan take zasu buxo sai kayi amfani dasu. Idan ba ka bukata, sai kawai ka goge su (Delete) daga kan kwamfutar shikenan. Kaje shafin PortableApps dake: https://www.portableapps.com.

Akwai waxanda ke xauke da manhajoji na kyauta amma masu nakasasshiyar sifa da aiki. Asalinsu na sayarwa ne, amma idan kana son gwadawa don ganin yadda suke aiki, sai a baka kyauta ka dandana. Idan ka gamsu, sai ka saya. Waxannan su ake kira: “Trial Version Applications”. Kana iya samunsu a shafukan manya-manyan kamfanonin kwamfuta irin su Microsoft, da Adobe, da IBM da sauransu. Za a baka kyauta na wasu ‘yan kwanaki ko watanni. Galibi bai wuce kwanaki 90; watanni uku kenan. Da zarar kwanakin sun qare, sai ka kasa amfana da manhajar, saboda irin kariyar da suka sanya a ciki.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.