Sakonnin Masu Karatu (2020) (6)

Hanyoyin Koyon Gina Manhajar Kwamfuta

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 17 ga watan Afrailu, 2020.

119

Salamun alaikum Malam, barka da wannan lokaci.  Ina karatu ne a Jami’ar Bayero dake Kano.  Ina sha’awar in koyi fannin gina manhajar kwamfuta (Programming) sosai.  Domin ina son in iya gina manhajar kwamfuta da kuma gidajen yanar sadarwa.  Ina da babbar waya kuma ina da kwamfuta.  Kuma alhamdulillah na iya sarrafa kwamfuta dai dai gwargwado. Kuma ina da dan ilimi kadan akan wannan fanni.  Malam, so nake a bani shawara hanyar da zan fadada ilimina.  Da hanyoyin da suka kamata inbi. Allah ya kara basira. – Abubakar Umar, Bayero University, Kano: abubakarumarh2015@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abubakar, babana.  Tabbas ilmi da dabarun gina manhajar kwamfuta na cikin nau’ukan ilmi masu mahimmanci a wannan zamani da muka samu kanmu a ciki.  Sannan, in ka duba dukkan abin da ake mu’amala dasu a wayar salula da kwamfuta, kusan duk dai manhajar ce, tunda ita ce ruhi ko ran kwamfuta.  Na yi farin ciki da jin cewa kana son ka kware a wanni na musamman.  Kuma ga shawarwari nan takaitattu amma gamammu don samun daman cin nasara a abin da aka sa a gaba.

Abu na farko shi ne hakuri da juriya.  Tunda ka riga ka canki fannin da kake son kwarewa a kai kuma kana da sha’awa a kansa.  Shi wannan fanni na gina manhajar kwamfuta ko wayar salula, duk da cewa a wannan zamani an dada sawwake shi sanadiyyar samuwar hanyoyin zamani, amma fanni ne mai fadi da kuma sarkakiya.  Don haka, dole ne ka lazimci hakuri.  Abu na biyu shi ne zaban bangaren da kake son kwarewa a kai.  Kamar yadda na sanar da farko, fanni ne mai fadin gaskiya.  Fannonin da suka fi shahara dai su ne bangaren gina manhajar wayar salula, wato “Mobile Programming”, amma ba ka fara gina manhajar wayar salula kai tsaye ba tare da sanin ka’idojin gina manhajar kwamfuta ba, wato: “Programming”.  Wannan ya kai mu ga abu na uku, wato koyon tsarin gina manhajar kwamfuta.  Shi wannan wani ilmi ne gamamme kan yadda ake tsara hanyoyin gina manhaja, da irin yare ko dabarun da suka kebanci fannin, da kuma matakan da ake bi wajen koyon ilimin cikin sauki; daga farko har karshe.  Idan ka gama fahimtar me ake nufi da tsarin gina manhaja (Programming), sai abu na hudu, shi ne zaban wani yare na musamman wanda kake son kwarewa a kai.  Misali, idan bangaren gina manhajar kwamfuta ne, akwai yaruka ko dabaru da dama – C, C++, C#, Java, Python dsr.  Idan bangaren gina manhajar gidan yanar sadarwa ne (Web Design), akwai yaruka da dabaru irin su: JavaScript, PHP, HTML, CSS dsr.  Idan bangaren gina manhajar wayar salula ne kuma akwai dabaru irin su: Java, da Koatlin, da Julia, da Python (Kivy) dsr.  Sai ka yi nazarin tsarin gina manhaja za ka fahimci wannan rabe-rabe.

Abu na biyar, shi ne, bayan ka gama zaban fanni da bangaren da kake son koyo, sai ka dukufa aiki.  Wannan kuma ya kunshi shiga makaranta inda za a koya maka abin a nazarce da aikace.  Makarantar na iya zama ta Zahiri, ko daga kai sai malaminka ne, ko ta zama ta shafukan yanar sadarwa a Intanet, inda za a koya maka abin mataki mataki. Abu na shida shi ne, duk abin da ka koya ko aka koya maka, kayi kokarin kwatanta shi a aikace.  Wannan fanni na ilimi yana bukatar kwatanta abu ne a aikace, ba fanni bane da ake karatu a nazarce.  Duk abin da ka koya, sannan ka kwatanta shi, to, ya zauna maka kenan.  Da haka ake tafiya har a kware.

- Adv -

Abu na bakwai kuma na karshe shi ne, ka guji gaggawa, da kasala, da kuma yawan fashi bayan ka fara.  Shi gaggawa ba abin da zai ja maka sai nadama.  Domin da yawa cikin matasanmu masu hazaka sun fara koyon wannan fanni, amma gaggawa ya hana su kwarewa, saboda so suke nan take da farawa kawai su kware har su fara samun kudi. Manufarsu ita ce kudi.  Eh, muddin ka koyi wannan fanni za ka samu kudi, amma kada kudi ya zama babbar manufa da dalilin da zai sa ka koyo ilimin. Idan kayi haka, baza ka taba zama ka koya cikin natsuwa ba, sannan za ta neman hanyoyin “sauki” wajen yin abubuwa.  Hakan kuma zai sa ka tsira da karamin ilimi, wanda Hausawa suka kira “kukumi”.

Da fatan ka gamsu da wadannan shawarwari takaitattu.  Ina maka fatan alheri da dacewa da kuma albarka cikin abin da ka koya.  Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah ya kara fasaha da lafiya da rufin asiri. Ya kuma kareka daga sharrin makiya.  Ina so ka taimaka ka aiko min kasidunka. Daga dalibinka mai bibiyarka a Aminiya, shafin Kimiyya da Kere-kere. –  Umar Ibrahim, 09068867436: ibrahimumar7436@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Umar.  Ina godiya matuka da addu’o’inku.  Allah saka da alheri.  Dangane da abin da ya shafi aiko maka da makalolin da nake rubutawa, na farko dai baka yi bayanin wanne ko wadanne daga ciki ba.  Na biyu, na daina aiko Makala ga masu karatu ta adireshin Imel.  Shi yasa na bude gidan yanar sadarwa (Website), wanda na gina shi da kaina, don zuba dukkan makalolin da nake rubutawa a wannan shafi.  Don haka, idan kana bukatar makalolin, kana iya ziyartar shafin dake: https://babansadik.com.  Ko kuma ka hau shafin Google (https://www.google.com) sai ka rubuta Taskar Baban Sadik, in Allah Yaso za ka ci karo da shafin, shi ne na farko daga sama.  Allah sa a dace, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.