Sakonnin Masu Karatu (2017) (29)

Ci gaban sakonnin masu karatu. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

138

Assalamu alaikum Baban Sadik. Don Allah ni wayata ce idan na hau Intanet sai tayi ta nuna mini alamar kamar tana nemo bayanai ne (Searching) amma ba ta budewa sai ta tsaya.   Ko mene ne dalili?  Daga Anas Umar Gwadabawa, Jihar Sokoto: 09098158729

Wa alaikumus salam, barka dai.  Abin da wannan ke nunawa shi ne, ko dai ba ka da data ne a wayar, ko kuma siginar Intanet dake tsakanin wayarka da kamfanin sadarwarka ba shi da karfi.  Dayan wadannan dalilai biyu ne zai iya haddasa faruwar wannan lamari.  Don haka, sai ka bincika ka gani.  Idan rashin “data” ne a wayar, sai ka loda mata.  Idan kuma akwai, amma duk da haka wayar ta kasa hawa, to lallai akwai matsala.  Hanya ta karshe da zan ba da shawarar a gwada ita ce: a tabbatar wayar na dauke da tsare-tsaren da ke bata damar hawa Intanet, wato: “Configuration Settings.”  Duk da cewa a yanzu akwai wadannan tsare-tsare a gine a cikin katin SIM din kamfanonin waya, amma tabbatar da samuwarsa zai taimaka matuka.  Allah sa a dace, amin.


 

Assalamu alaikum Baban Sadik.  Gaskiya sai dai muce Allah ya biya da mafificin alhairi game da ilimin da muke samu daga gareka.  Kuma lallai za mu so a fara bamu ilmin programming kamar yadda ka kwadaitar damu.  Daga Yakubu Abdulkadir, Jihar Bauchi

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Yakubu, daga Bauchin Yakubu.  Ina matukar farin cikin jin cewa abin da ake karantawa yana ba da fa’ida iya gwargwado.  Dangane da bukatarka kuwa na samun mahalli na musamman don koyar da ilimin “Programming”, tabbas wannan alkawari ne da na dauka a watannin baya, cikin shekarar da ta gabata.  Kuma a halin yanzu ina kan kokarin ganin na cika wannan alkawari nawa.  Kada a mance, nayi alkawarin samar da gidan yanar sadarwa ne na musamman don yin hakan.  Duk da cewa daga baya wasu cikin masu karatu sun shawarceni da in fara samar da darussa na musamman don karantar da hakikanin kwamfuta da yadda take aiki tukun, wanda wannan ita ce asali ko tubalin da ake son duk wanda zai koyi wancan ilimi na “Programming” ya fara dashi, in yaso daga baya sai in dora kan wancan din.

Zan gina gidajen yanar sadarwa ne guda biyu; daya da harshen turanci, dayan kuma da harshen Hausa.  Kuma a halin yanzu na mallaki adireshin gidajen yanar tuni, ina kan ginawa ne.  da fatan za a ci gaba da taimakawa da addu’a tare da kasancewa damu a wannan shafi mai albarka.  Domin kasantuwarku na kara mini kwarin gwiwa a kowane lokaci.  Na gode matuka, Allah saka da alheri, amin.


 

Salaamu alaikum, Baban Sadik.  Na yi farin cikin dawowar shafin Taskar Baban Sadik, sai dai ban ga abin da na yi matukar zakuwa da in gani ba.  Wato bangaren karbar horaswa da kayi bayani a kai. Sai na ji daga gareka.  Nagode.  Muhammad Baba Idriss, mai sha’awar aikin jarida, kuma dalibinka.  Damaturu, jihar yobe.

Wa alaikumus salam, barka dai.  Idan mai tambaya bai mance ba,  cewa nayi ina kan aiki ne kan gidajen yanar da zasu dauki wadannan darussa.  Don haka sai a ci gaba da kasancewa tare damu a wannan shafi mai albarka.  Idan na gama zan sanar, ta dukkan hanyoyin da na bayar da sanarwar farko.  Wancan kawai na mana albishir ne.  A halin yanzu na mallaki adireshin gidajen yanar sadarwar tuni, kuma na fara kintsa bayanan da zan zuba a ciki na darussan da za a yi mu’amala dasu.

Sai a ci gaba da kasancewa tare damu.  Na gode matuka.


Assalamu alaikum ranka ya dade.  Tamyata ita ce: shin, ko akwai wasu makarantun koyon ilmi kan na’ura mai kwakwalwa da ake koyarwa ba tare da wahala irin ta kashin kudi ba, a fili ko ta yanar gizo, kamar yanda ka fada a baya cewa: akwai karatu ta yanar gizo da ake yi kyauta tare da samun shaidar kammalawa ta yanar gizo.  Ina fatar samun kammalallen bayani da amsa mai gamsarwa, tare da kasidun da ka rubuta daga shekarar 2015 zuwa yanzu.  Ana iya turo amsar ta wannam Imel: namadinion@gmail.com.  Usama Namadina Umar

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Namadina.  Dangane da samun kasidun da na rubuta a shekarar 2015, wannan sai dai ka ziyarci Taskar Baban Sadik dake: https://babansadik.com, a can na taskance dukkan kasidun da suka bayyana a wannan shafi, wanda na fara rubuta su tun shekarar 2006; shekaru 11 kenan a halin yanzu.  Akwai kasidu sama da 480 yanzu haka. 

Dangane da batun amsar da na baiwa wancan mai tambaya kan hanyoyin koyon ilmin kwamfuta ta Intanet na kyauta, lallai na buga bayanan a shafin jarida, watakila ka riski amsar da na baiwa wanda ya maimaita makamanciyar tambayar ne.  Duk da haka, ga kadan daga cikin amsar da na bayar nan kasa:

“Lallai akwai shafuka ko ince “Makarantun” koyon ilimin kwamfuta kyauta a Intanet.  Wadannan makarantu ko wurare dai sun kasu kashi-kashi; akwai na kudi, akwai na kyauta, akwai wadanda bayanan a rubuce suke – sai ka karanta – sannan akwai wadanda suke dauke da bayanan bidiyo ne tsantsa.  Sai dai wani abu kuma, galibinsu, kashi 90 cikin 100, duk da harshen Turance suke.  A wasu shafukan kuma, dole ne kayi rajista kafin ka fara daukan darasi.  Wasu shafukan na bayar da takardar shedar gama karatu, wasu kuma ba su bayarwa.  Wasu na dauke da wuraren gwaji, wasu kuma ba su da wuraren gwaji, sai dai kayi amfani da kwamfutarka.

Duk da ba dai ban san wani bangare kake son koyo ba, shafin da yafi kowanne shahara kuma yake baiwa masu bukatar koyon nau’ukan ilimi daban-daban (ba wai na kwamfuta kadai ba), shi ne shafi mai take: “Tutorials Point.”  Wannan shafi ko makaranta tana dauke ne da rubutattun darussa da suka shafi fannoni daban-daban na ilimi.   Duk wani fanni na kimiyya da kere-kere za ka iya koyonsu a wannan shafi kyauta.  Kusan dukkan fannonin ilimin kwamfuta za ka iya koyonsu a wanan shafi.  Sannan shafi ne dake koyar da kai a tsarin mataki-mataki; daga farko har zuwa karshe.  Adireshin wannan shafi dai shi ne: www.tutorialspoint.com.  Kana hawa shafin daga sama sai ka matsa: “Tutorials Library,” don zaban fannin da kake son koyo.  Ko kuma ka gangara can kasa, za ka wani dogon jadawali mai dauke da dukkan fannonin da za ka iya koyo a wannan makaranta.  Duk na nuna cewa makaratar na dauke ne da rubutattun darussa, sai dai akwai bangaren darussan cikin bidiyo, sannan akwai bangaren kwatanta abin da ka koyo, idan ilimi ne mai dauke da koyo a aikace.  Misali, idan bangaren gidan shafin yanar Intanet kake son koyo (Web Design), akwai bangaren da za ka je ka kwatanta abin da ka koya a aikace, ba sai kana da kwamfuta ta kashin kanka ba.  Kana iya samun wannan wuri a shafin farko daga sama, can bangaren dama, mai take: “Coding Background.”

Idan kana son kuma inda zaka koyo nau’ukan kwamfuta musamman yadda ake gina manhajar kwamfuta ne (Programming) ne kai tsaye, daga farko har zuwa karshe, tare da takardar shedar karatu (Certificate), duk a kyauta, sai kaje shafi mai take: “Solo Learn.”  Wannan makaranta na daga cikin makarantu dake karantar da ilimi cikin sauki, tare da hanyar kwatanta karatun, cikin sauki.  Ba ma wannan kadai ba, ana karantar dakai ne mataki-mataki, cikin tsari mai dauke da nishadantarwa da saukin fahimta.  Ba a cika ka da tarin bayanai.  Rubutattun bayanai kadan ne, sai misalai birjik.  Cikin kankanin lokaci za ka koyi ilimi mai yawa, wanda ke dauka da dabbakawa.  Idan ka gama karatun nan take za a aiko maka da takardar sheda ta adireshin Imel dinka.

Amma dole sai ka yi rajista kafin ka fara daukan darasi.  Idan nace rajista ban nufin biyan kudi.  A a.  ina nufin za ka bude “account” ne.  Idan kuma ba ka son bude wani “account”, kana iya hawa da adireshinka na “Facebook” ko “Gmail,” kai tsaye, a duk sadda ka tashi shiga.  Bayan dukkan wannan, kana iya saukar da manhajar wannan makaranta a wayarka daga cibiyar “PlayStore” na wayoyin Adroid, sai dai kuma dole ne sai kana da Intanet za ka iya hawa a kowane lokaci.  Adireshin wannan shafi yana:  www.sololearn.com.

A daya bangaren kuma, akwai shafukan koyon ilimi ta hanyar bayanan bidiyo, su ma kyauta.  Wannan na samuwa ta hanyar shafin “Youtube” na kamfanin Google.  Wannan shafi na Youtube dai wata duniyar ilimi ce, mai dauke da kusan “kowane” nau’in ilimi kake bukata ko abin da ya dangance shi.  Jakar magori ce!  Idan kana da wayar salula irin ta zamani mai iya mu’amala da fasahar Intanet, to lallai baza ka rasa samun manhajar Youtube a kan wayar ba.  Ko dai ya zama wanda wayar tazo dashi ne (musamman idan Android ce), ko kuma ka same ta a cibiyar Play Store ko Store, idan nau’in “Windows Phone” kake amfani da ita.

Idan kuma da kwamfuta kake son hawa shafin, kana iya shigar da: www.youtube.com.  Da zarar ka hau, a sama daga tsakiya akwai inda aka tanada don yin “tambaya” (Search) kan nau’in ilimi ko bayanan da kake bukata.  Kada ka mance, galibin ire-iren wadannan ilimi dai cikin harshen turanci suke.  Don haka, duk tambayar da za ka yi ta zama cikin harshen turanci ce, kan wani fanni na ilimin kwamfuta kake son koyo.  Kana tambayowa kuma za a baka amsa bila-adadin.

Wadannan su ne wadanda zan iya baka shawarar ka lazimta a halin yanzu.  Ba wai iyakansu ba kenan, a a, suna da yawa.  Aika maka dandazonsu zai rikitar da kai, har ka kasa tabbatuwa a kan guda daya.  Idan ka lazimci wadannan, ka fa’idantu, da kanka za ka nemo kari, ba sai ka sake tambayar wani ba.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.