Sakonnin Masu Karatu (2019) (5)

Hanyoyin mu'amala da manhajar "Playstore"

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Maris, 2019.

302

Assalamu alaikum, sunana Jamilu BBT Kiru, Kano.  Ni tambayata ita ce: idan zanyi anfani da manhajar “Play Store” yaya zan yi?  Kuma kamar idan zan rubuta sakon Imail nawa na kaina, yaya zanyi?  A taimaka a bani amsoshin tambayoyina.  Na gode.  Ina yi muku fatan alkairi.

Wa alaikumus salam, Malam Jamilu barka da warhaka.  Manhaja ko Cibiyar Play Store manhaja ce dake dauke da dukkan manhajojin da aka gina su, ta hanyoyi da ka’idojin gina manhaja da kamfanin Google ya gindaya, don amfani dasu a kan wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Android.  Wannan cibiya tana nan a kan duk wata wayar salula dake dauke da babbar manhajar Android.  Kuma akwai manhajoji nau’uka uku.  Na farko su ne wadanda dole sai ka saya, kafin ka iya saukarwa don amfani dasu a kan wayarka.  Na biyu su ne wadanda za ka iya saya don samun cikakken fa’idarsu, amma akwai na kyauta masu dauke da nakasa; har da tallace-tallace.  Sai na uku wadanda kyauta ne su gaba daya.  Wadannan sun kasu kashi biyu; akwai masu dauke da tallace-tallace a cikinsu, wanda masu su suke amfana dasu musamman idan an latsa su.  Kashi na biyu kuma wadanda ba sa dauke da tallace-tallace; garau suke.  Daga cikinsu akwai nau’in manhaja ta Kur’ani mai girma mai suna: “Android Qur’an”.

Amfani da wannan cibiya mai dauke da manhajoji dai babu wahala.  Ka’ida ko sharadin kwaya daya ne; ya zama kana adireshin Imel na kamfanin Google, wato: “Gmail” kenan. Tuwo na mai na kenan.  Masu abu da abinsu; dan kura da kallabin kitse.  Idan baka da adireshin Imel na Gmail, baza ka iya saukar da manhaja ko daya ba, balle kayi amfani da ita a kan wayarka.  Idan ka budo manhajar a karon farko, za a bukaci ka shigar da adireshinka na Imel ne, ko “lambar waya”.  Kada ka rudu.  Lambar wayar da suke nufi a nan ita ce wacce kake amfani da ita wajen shiga Gmail dinka, idan da lambar waya ka bude a matsayin suna (username).  Ko kadan kada ka dauka ana nufin kowace lambar waya ce.  Idan ba ka da adireshin Imel na Gmail, za a baka damar bude sabo nan take.  Da zarar ka bude, kai tsaye za a zarce dakai wannan cibiya, ka kwashi garabasa a sama.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik.  Da fatan lafiya, Allah kara basira.  Tambayata ita ce: ta yaya ake gina manhaja (application)?  Sannan kai tsaye yake hawa cibiyar “Play Store”?  Kuma ana biyan wani kudi na musamma ne kafin budewa da dorawa?  Ka huta lafiya.  Daga Salmanu Mukhtar Kano.

Wa alaikumus salam, Malam Salmanu barka ka dai. Tambayarka ta farko kan yadda ake gina manhaja, ba ta da amsa tilo.  In dai manhajar wayar salula kake nufi, kana bukatar kwarewa a fannin ilimin gina manhajar wayar salula, kamar yaren “Java” misali, ko “Phython”.  Sannan kana bukatar kayan aiki, wato manhajojin da ake amfani dasu wajen gina manhajar, irin su: “Android Studio” da asalin manhajar “Java” da dai sauran kayayyaki.  Don samun cikakken bayani, na zayyana wadannan abubuwa a cikin kasidar da na gabatar mai take: “Tsarin Babbar Manhajar Android”, kashi na 7. Kuma kana iya samun kasidar a shafina dake: https://babansadik.com/category/wayar-salula.

Tambayarka ta biyu na son sanin ko kai tsaye manhajar da ka gina za ta samu hawa wannan cibiya.  Amsar ita ce: a a.  A matsayinka na kwararre mai gina manhaja, dole kayi rajista a kamfanin Google, wanda wannan shi ne zai baka damar yin gwaji a karon farko, wajen ganin ko manhajar ta cika ka’idar da Google ya tanada.  Daga nan sai ka dora da kanka, a lokacin da kake so.  Idan an karba za ka sako kan haka.  Amsar tambayarka ta karshe da ke cewa ko ana biyan wasu kudade ne kafin a dora, a a.  Muddin dai kayi rajista da kamfanin Google, wanda rajistan kyauta ne, sannan manhajar da ka gina ta cika ka’idar mahallin, ba ka bukatar biyan wani kudi.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Ibnu muhammad numan says

    Fatan alkhairi kaida mutan gidanka
    Allah yabiyama buqatunkana alheri daganan duniya har alahira Abban sadik

  2. Hamisu says

    Allah ya saka da alkhairi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.