Sakonnin Masu Karatu (2018) (6)

Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

122

Assalamu alikum. Ina yi wa Malam fatan alheri, Allah ya kara nisan kwana mai amfani. Don Allah Malam yaya zan yi in samu adireshin Imel mai suna “info”?  Misali: info@yconnect.com.  Na gode. Sako daga Yahuza Idris Hotoron Arewa. Kano 08039180699: yahuza09@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Yahuza.  Da fatan kana lafiya.  Mallakar adireshin Imel mai wannan suna na samuwa ne idan kana da adireshin Gidan yanar sadarwa, wato: “Website Address.”  Kafin ka bude Gidan yanar sadarwa jama’a su iya isa ga bayanan da ka zuba, dole ne sai ka sayi adireshi.  Wannan adishireshi kuwa shi ne kwatankwacin: www.babansadik.com.  Da zarar ka mallaki wannan, sai ka sayi mahallin da za ka dora Gidan yanar sadarwar.  Wannan mahalli shi ake kira: “Hosting”.  A cikin tsare-tsaren “hosting” din galibi kamfanin da kayi rajista dashi don adana maka shafinka, zai hada maka da manhajar Imel na kai tsaye, wanda za ka iya zaban irin sunan (username) da kake.  Idan “info” din kake so, kana iya zaba. 

Amma idan ta manhajar Imel na Intanet ne irin su Gmail da Yahoo!, zai yi wuya ka iya mallakar irin wannan suna.  Da fatan ka gamsu.


Salaamun alaikum Abban sadik, barka da yamma.  Ina fatan kana lafiya.  A gaskiya ina jin dadin karanta jaridar AMINIYA, hakan yasa naji kodayaushe ina tare da ita.  Na kasance ina nuna so da kauna a gareka duk da ban taba ganinka ba, amma wallahi kana bargeni kuma kana sa ni nishadi a kodayaushe.  A karshe ina maka fatan alhairi.  Daga Nura Jigawa: 09063340724

Wa alaikumus salam, Malam Nura barka dai.  Ina godiya matuka da nuna kauna da kake min, tare da kebance ni da wannan kaunar.  Allah saka da alheri, musamman da ka sanar dani.  Ni na ina kaunarka don Allah.  Kuma ina rokon Allah ya hada fuskokinmu da alheri a ko ina muke.  Allah kuma ya kara fahimta cikin abin da kake karantawa daga gare ni.  Na gode.  Na gode.  Na gode.


Assalamu alaikum; gaskiya ba abin da zamu ce sai dai Allah ya kara basira.  Baban Sadik don Allah meye bambancin “Java” da “Python”?  Kuma wanne ne yafi saukin koyo? Na gode. A. A. Namada: 08168315523

Wa alaikumus salam Malam Namadi, muna godiya da sakonka.  Da farko dai zai dace muyi takaitaccen bayani kan kowanne daga cikin wadannan nau’ukan dabarun gina manhajar kwamfuta da wayar salula guda biyu, kafin mu san meye bambancin dake tsakaninsu.  Mu fara da Java:

- Adv -

“Java” – Wannan yare mai suna “Java” an samar da shi ne a shekarar 1995, ta hanyar kokarin wani bawan Allah mai suna: James Gosling. Tsari da kintsin “Java” sun samo asali ne daga yaren “C++”, bambancin dake tsakaninsu ba shi da fadi sosai.  Ana amfani da yaren Java wajen gina abubuwa da yawa, daga manhajojin sarrafa injina zuwa na wayar salula.  Kashi 80 cikin 100 na manhajojin wayar Android duk da yaren “Java” aka gina su.  Haka galibin manyan manhajojin kwamfuta na zamanin yau, duk da “Java” aka gina su.  “Java” ita ce “amarya” a tsakanin dabarun gina manhajojin kwamfuta.

“Python” – Wannan yare an samar dashi ne a shekarar 1990, ta sanadiyyar kokarin Guido Van Rossum, wani masanin fannin lissafi (Mathematician) dan kasar Holland.  Ana amfani da wannan yare wajen gina shafukan Intanet, da manhajojin kwamfuta masu amfani da Intanet.  Shahararru daga cikin manhajoji da shafukan da aka gina da “Python” dai sun hada da: shafin “Youtube”, da “BitTorrent”, da wani bangaren manhajar “Facebook,” da “Yahoo Maps”, da “Google”, da “Pinterest”, da “Instagram”, da “Drop Box,” da “Firefox” na kamfanin Mozilla, da manhajar “Blender,” da “Cinema 4D” da dai sauransu.  Sannan a daya bangaren kuma, ana amfani da “Python” wajen gina manhajojin wayar salula na Android, ta amfani da wani yare mai sauki mai suna: “Kivy.”  Wannan yare na “Python” yana da matukar sauki wajen koyo, kuma da “Python” kana iya gina duk irin manhajar da ka ga dama, muddin kana da kwarewa da kuma zimmar yin hakan.

Bambancin dake tsakanin wadannan yaruka guda biyu dai ba wani mai yawa bane can-can.  Da farko dai dukkansu yaren gina manhaja ne na zamani masu amfani da salon gina manhaja mai suna: “Object-Oriented Programming,” ko “OOP” a gajarce.  Sannan dukkansu na cikin sahun yarukan gina manhaja na sama-sama wadanda ake wa lakabi da: “High Level Programming Languages,” domin sun sha banban da yaren “C”, wacce ke da alaka ta kai tsaye da kwakwalwar kwamfuta.  Bayan haka, kowannensu ana amfani dashi wajen gina manhajar kyauta, wanda tsari ne da ake kira: “Open Source.”  Wadannan manyan siffofi uku su ne abubuwan da suka hada alaka tsakaninsu.

A daya bangaren kuma, yaren “Java” ya fi shahara a duniya, kuma an fi amfani dashi sosai wajen gina manhajojin kwamfuta da na wayar salula fiye da Python.  Sai dai kuma, Python ya fi Java saukin koyo, da saukin al’amari, da kuma saukin fahimta wajen karantarwa.  Abin da za ka rubuta shi cikin layi ko sadara daya da yaren Python, sai ka rubuta sadara uku ko hudu in yaren Java ne.

Bayan haka, yaren Python yafi shahara a fannin nazarin bayanai a duniya yanzu, wato: “Data Analysis.”  Sannan an fi amfani dashi wajen gina manhajojin kwamfuta masu kwailwayon dabi’un kwakwalen mutane, wato: “Machine Learning” ko “Deep Learning Applications.”  Wannan ya faru ne saboda kwararru da aka samu masu lura da wannan yare, wadanda suka kirkiri dabarun nazarin bayanai da koya wa kwamfuta yin abubuwan da kwakwalwar dan adam ke iya na fahimta, cikin yaren.  Shahararru cikin tsare-tsaren dake taimakawa wajen aiwatar da hakan kuwa sun hada da: “Matplotlib”, da “SciPy”, da “SymPy”, da “TensorFlow”, da “Pandas”, da “Numpy”, “SciKit Learn” da dai sauransu.

A bangaren gina manhajar wayar salula (Mobile Applications) kuma, yaren Java yayi fintinkau, a halin yanzu.  Domin kusan dukkan ko galibin manhajojin wayar salula na Android, duk da yaren Java ake gina su.  A nasa bangare, yaren Python na da tsarin “Kivy” da ake amfani dashi wajen gina manhajar Androids na wayar salula, amma bai shahara ba sosai.  Bayan shi kuma akwai tsarin “React Native”, wanda bangaren tsarin “React” ne na kamfanin Facebook, mai asali daga yaren “JavaScript”, da ake amfani dashi wajen gina manhajojin wayar salula na Android da na iOS.

Wannan, a takaicen takaitawa, shi ne kadan daga cikin abin da ya samu na alaka da kuma bambancin dake tsakanin yaren Java da Python.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Mustapha Alkasim Kabo says

    Wallahi ni bansan iya adadin godiyar da zan maka ba bababn sadik, Domin iyaka karatu agaskiya kana bamu, Allaah ya saka da alheri ya sa muma abinda muka koya mu fadawa wadansu da basu sani ba ameen. Allaah ya saka maka da alheri yakuma sa Aljanna ce makoma insha Allaah, da haka kuma nake son a gaishemin da sadik, maman sadik, Allaah ya jikan mahaifa ameen

Leave A Reply

Your email address will not be published.