Sakonnin Masu Karatu (2021) (3)

Fasahar "Artificial Intelligence"

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 5 ga watan Fabrairu, 2021.

126

Assalamu alaikum, barka da wannan lokaci. Yaya iyali ya jama’a? Allah kara basira. Ina mutkar jin dadin bayaninka na AI (Artificial Intelligence). Dan Ina karuwa da sanin abubuwan da a baya ban san amfaninsu ba, musamman ni dake da burin zama kamar Kai a fagen sanin kimiyya. Duk da nasan kaifin basirar ba daya bane. Amma Ina fata Allah ya bani nasara akan haka,  idan ina son karantar wannan Fannin wani course zanyi Apply? Na gode – yahyarahinat@gmail.com – Rahinat Yahya.

Wa alaikumus salam Malama Rahinat, ina godiya matuka da addu’o’inku.  Allah biya mana bukatunmu na alheri baki daya, amin.  Ai wannan Makala ta Artificial Intelligence (AI) mabudi ce.  Nan gaba zan ci gaba da rubutu don kara kayatar da makalar, ta hanyar bayyana wasu kayatattun fasahohin da a baya ban yi Magana a kansu ba.  Dangane da bukatarki na karantar fannin kwamfuta ko AI, in na fahimceki sosai, shi ilimin kwamfuta wani abu ne dake bai daya.  Babu kwasakwasai na musamman irin su AI a jami’o’inmu, said ai gamammen fannin “Computer Science” ko “Computer Engineering”, ko “Information Technology”, da sauran makamantansu.  Amma kwasakwasai na kwarewa galibi sai dai mutum ya karanta su ta hanyar makarantu masu zaman kansu, ko ta shafukan Intanet.   A karshe, ina miki fatan alheri.  Allah sa a dace, ya kuma ba da abin da ake nema na alheri, amin.  Na gode matuka.

Assalamu alaikum Baban Sadik, ya kokari? Allah ya taimaka. Tambayata ita ce: Shi WordPress yaya yake?  Mene ne bambancinsa da Blog? Na sauke manhajar WordPress ne a kan wayata kafin inyi rajista nake son karin haske a kanta.  Na ga wasu masu shafukan jaridu a Intanet suna amfani da WordPress ne, wasu kuma abubuwan da suka shafi harkokinsu ne su keyi a kai.  Shin, zan iya bude gidajen yanar sadarwa sama da daya akan WordPress a kan wayata har kuma a iya gani ko ziyartarsu akan kwamfuta?   Tambaya ta biyu, na sauke manhajar Wix a wayata na ga sunce ana iya bude website address dashi, to kyauta ne ko akwai one time pay ko kuma biya za a rika yi annually? Ka taimake ni da amsoshin nan ta wannan email din nawa don bama samun jaridar Aminiya a yankinmu tun tsawon watanni hudu.  Na gode.  – Ahmed Ali: ahmedaaly@yahoo.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ahmad. Da farko dai, “Wordpress” sunan kamfani ne dake da manhajar ginawa da adana bayana a shafukan Intanet mai suna “Wordpress”.  Tsarin WordPress dai shi ne, manhaja ce da za ka iya hawa a shafinsu dake Intanet, ko kuma ka sauke a kan kwamfutarka, kamar yadda kayi a wayarka, don baka da damar gina shafukan Intanet a wuri daya, sannan idan ka gama, sai ka dora shi a mahallin da ka saya don adana shi ga masu ziyara.  Bayan WordPress akwai wasu manhajoji makamantanta, irin su: “Joomla”, da “Django” da dai sauransu.  Ana kiransu da suna: “Content Management System”, ko “CMS”a gajarce.  Haka ma Wix manhaja ce ta gina shafukan Intanet.  Sai dai ban taba amfani da ita ba.

- Adv -

Bambancin WordPress da Blog kamar bambancin dan adam ne da wata halitta daban.  Ba jinsi daya bane.  Shi Blog dai shafi na kashin kai da za ka gina don taskance ra’ayoyinka a matsayinka na kwararre a wanni fanni na rayuwa.  Galibi yana dauke ne da babban shafi, inda dukkan makalolin da kake rubutawa suke jere, sai kuma shafin daidaikun makaloli, wanda idan aka latsa Makala za a zarce da kai.  Amma WordPress asalin manhajar da ake amfani da ita ne wajen gina shafukan Intanet, ciki har da Blog.

Sai dai zai dace ka san cewa, kana iya amfani da wayarka ta salula ne cikin sauki wajen loda bayanai a shafinka na Intanet wanda ke dauke a manhajar WordPress.  Amma idan gina shafin ne, dole ko dai ka saukar da manhajar ne a kan kwamfutarka ko kuma ka rika hawa shafinka a Intanet.  Domin gina shafin Intanet ba abu bane da a al’adance ake yinsa ta wayar salula.  Aiki ne ja, inji mutan Dan Ja dake Katsina.

Dangane da ko za ka iya gina shafukan Intanet sama da guda a WordPress, amsar ita ce eh, amma ba yadda kake tunani ba.  Akwai abin da ake kira “Multisite”, wanda ya tsari ne da manhajar WordPress ke baka wajen ta’ammali da shafuka sama da daya a hurumi guda.  Da asalin shafinka, da kuma wani shafi dake jingine da adireshin uwar shafin, wato: “Subdomain” kenan.  Amma duk da haka, kamar yadda na fada a baya, saukar da WordPress da gina shafukan Intanet abu ne daya, sannan mallakar adireshin shafin, da kuma inda za a adana bayanan don baiwa mutane damar ziyartarsu, wani abu ne shi kuma daban.  Ba abu bane da za ka gudanar dashi ta hanyar WordPress a lokaci daya.  Yadda tsarin yake shi ne, ko dai ka saukar da WordPress a kwamfutarka, ka gama gina shafukan da kake so, sannan ka sayo adireshi tare da mahallin adana shafukanka, sai ka dauki wannan shafi da ka gina a kwamfutarka ka dora a mahallin da ka saya.  A cikin mahallin ne za ka saita adireshin shafin, da duk abubuwan da suka shafe shi.  Ba abu bane da za a iya rubuta shi a karanta kuma a fahimceshi cikin sauki ba.  Yana bukatar a ganshi a aikace.

Wannan shi ne takaitaccen bayanin da zan iya yi a yanzu.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.