Sakonnin Masu Karatu (2019) (21)

Gyara Shafin Facebook

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na ranar Jumma’a, 29 ga watan Nuwamba, 2019.

65

Assalamu alaikum, barka da wannan lokaci. Ina daga cikin tsofaffin dalibanka a shafin Kimiyya da Kere-kere. Na karu matuka da rubuce-rubucenka. Kana daya daga cikin dalilan da yanzu haka suka sa nake koyon dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming languages). Ina maka addu’ar Allah ya kara maka lafiya, da imani, da ilimi, da nisan kwana. Daga karshe, shin, zan iya tuntuvarka wajen neman shawarwari ta wannan lambar a kodayaushe, ko akwai wani adireshin naka daban? Asha ruwa lafiya. 08149273937

Wa alaikumus salam, ina godiya matuka da addu’o’inku.  Allah bamu dacewa baki daya, da amfanuwa da abin da muke karantawa a wannan shafi mai albarka.  Na yi farin ciki matuka da jin haka.  Daman manufar samar da wannan shafi shi ne don karuwar al’umma, musamman da nau’ukan ilimi na zamani da kowace al’umma ke tinkaho dashi a zamanin yau.

Daga lokacin da na fara rubutu a wannan shafi, cikin watan Oktoba na shekarar 2006, wato shekarar da aka fara buga jaridar AMINIYA kenan, da yawa cikin masu karatu sun aiko saqonni makamantan wannan.  Kuma wannan ke nuna cewa ana fa’idantuwa da bayanan da muke kwararowa.  Hatta masu karatun digiri na uku (PhD) suna amfana da wannan rubutu sosai.  Akwai waxanda suka bukaci in aiko musu wani vangare na rubuce-rubucen da nayi a baya a wasu fannoni na sadarwa, suna karatun PhD a wasu qasashe na Afirka.  Wannan abin alfahari ne ba gareni ba kaxai, ga Hukumar Media, wacce ke samar da wannan jarida a duk ranakun juma’a.  Allah saka mata da alheri da sauran ma’aikata da editocin da ke kashe lokuta don ganin kowane shafi ya kintsu a kan lokaci.

A karshe, kana iya tuntuvana ta wannan lambar, ta hanyar saqonnin tes, kamar yadda ka rubuto yanzu.  Idan bukata ce mai tsayi, kana iya aiko bukatar muyi Magana kai tsaye, duk da yake saqonnin tes kaxai nake karba a wannan layin, amma zan iya kiranka don bayar da nawa gudummawa iya karfina.  Haka kuma, kana iya aiko sako ta adireshin Imel din TASKAR BABAN SADIK, wato: wasiku@babansadik.com.  Na gode matuka.

Salamun alaikum Baban Sadik ya aiki, ina fata ka sha ruwa lafiya.  Allah yasa mu dace amin.  Dan Allah Baban Sadik shafin Facebook dina akayi Hacking.  Yaya za a yi in dawo dashi? Na gode Allah ya saka da alkhairi.  Daga Kamaliddeen, Kano state. 07046357914

- Adv -

Wa alaikumus salam, Malam Kamalu barka ka dai.  Abin da zan iya fahimta dai a takaice, shi ne, wani ya kwace shafinka.  Hanya mafi sauqi ita ce ka kai koke ga hukumar Facebook don su taimaka maka cikin sauqi.  Wannan wani abu ne da suka saba yi.  Domin ko nace zan maka bayani filla kan yadda zaka dawo da shafin ba lale bane ka fahimta cikin sauqi, sannan bayanin zai tsawaita matuka.  Ka shiga wannan adireshin:  https://m.facebook.com/hacked.

Shafi ne na musamman da hukumar Facebook suka tanada musamman don saurara da karban koken masu matsala irin wannan.  Sun san ana sace shafukan mutane.  Sun san irin badakalar da ke faruwa a wajen.  Domin a duniyar Intanet gaba daya babu inda ake aikata manyan laifuka cikin sauqi irin dandalin Facebook.  Kawai ya danganci saninka ne ko idan abin ya shafeka.  Don haka, ka hau shafin sai ka basu bayanan da zasu bukata.  Kafin nan, ka tanadi hoton ID Card xinda na makaranta ko wajen aiki ko wanda Gwamnatin Najeriya ta baka, irin katin zave, ko katin shedar zama dan kasa, wato: “National ID Card”, domin zasu tambayeka ko ma suce ka loda musu hotonka mai xauke da waxannan bayanai.  Manufar ita ce don su tantance kaine hakikakin mai shafin tukun, kafin aje batun taimaka maka wajen karbo shafin.  Kada ayi kitso da qwarqwata.

Ina maka fatan alheri kuma Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, fatan alheri.  Ina tambaya kan buxe shafin facebook ne; idan na fara buxe facebook sai insa sunana da sunan mahaifina, to sai a bukaci lambar waya ko email address.  Wannan lambobi sune?  Bagane ba; lambar wayar da nike amfani da shi ne ko wani ne daban? Tambaya daga Idris Musa, Ilorin, Kwara:  08034988388.

Wa alaikumus salam Malam Idris barka ka dai.  Lallai lambar da ake bukata taka ce, ko adireshin Imel.  Domin su ne zasu wakilceka a sahar Facebook din, kuma dasu za ayi amfani wajen nemanka ko hada ka da mutanen da kuke da kamaiceceniya na alaka ko wurin zama ko harkar rayuwa iri daya. Idan ka shigar za a aiko maka lambobi don tantance kai ne, daga nan shafi ya samu.

Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.