Web 3.0: Fasahar “EDGE Computing” (3)

Fasahar Cloud Computing

A halin yanzu fasahar “Cloud Computing” ce tafi shahara cikin nau’ukan wadannan hanyoyin adana bayanai ta hanyar Intanet.  Sai dai kuma, wannan fasaha tana dauke da nakasu ta wani bangaren.  Domin fannin fasahar sadarwa a kullum ci gaba yake dada samu, saboda yaduwar hanyoyin amfani da ita.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a 17 ga watan Yuni, 2022.

148

Matashiya

A makon jiya mun yi bayani kan marhalolin tsarin ma’adanar bayanai na tafi-da-gidanka.  Wannan tsari ya kunshi baiwa mai amfani da na’urar sadarwa ne damar adana bayanansa a wata ma’adana dake karkashin kulawar wani kamfani na musamman, wanda aikinsa ne yin hakan.  Ta yadda ake samun alakar musayar bayanai tsakanin kwamfutarka ko wayarka ta salula, wacce a kanta ne ake samarwa da kuma aika bayanan.  Sai kuma na’urorin kamfanin dake adana bayanan, wanda ke karba, su kuma adana maka. A duk sadda ka tashi bukata, kana iya isa gare su ta hanyar manhaja ko masarrafar da aka tanada don hakan, ta amfani da fasahar Intanet.

A halin yanzu fasahar “Cloud Computing” ce tafi shahara cikin nau’ukan wadannan hanyoyin adana bayanai ta hanyar Intanet.  Sai dai kuma, wannan fasaha tana dauke da nakasu ta wani bangaren.  Domin fannin fasahar sadarwa a kullum ci gaba yake dada samu, saboda yaduwar hanyoyin amfani da ita.  A duk yini duniyar yau na samar da bayanai masu dimbin yawa; tsakanin sakonnin kashin kai, da sakonnin kasuwanci, da sakonnin hukumomin gwamnati, da na kamfanonin sadarwa.  Babban kalubalen da tsarin ke fuskanta na ga nau’ukan bayanan ne da ake ta’ammali dasu a duniya a yau.

Kalubalen Marhalar “Cloud Computing”

Da yawa wasu kan ce: “Meye amfanin samar da tsarin “EDGE Computing” a yau bayan ga fasahar “Cloud Computing” na samar da fa’idar adana bayanai, da kuma sarrafa su da kuma taskance su?”.  Amsar wannan tambaya za ta bayyana ne idan muka fahimci nau’ukan bayanan da a duniyar muke samarwa.  Wadannan bayanai dai sun kasu kashi uku ne.

- Adv -

Nau’in Farko su ne irin bayanan da muke samarwa daga ayyukan da muke gudanarwa ta hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani da muke amfani dasu, ko a daidaikun jama’a, ko a hukumomin gwamnati, ko a asibitoci, ko a cibiyoyin binciken kimiyya da dai sauransu, wadanda suke bukatar adanawa ne kadai, don amfanin gaba.  Ire-iren wadannan baynai su ne wadanda muke adana su ta amfani da tsarin Google Drive, ko OneDrive na kamfanin Microsoft, ko kuma tsarin DropBox.  Dukkan wadannan hanyoyi ne da a yanzu ake amfani dasu wajen adanawa da taskance bayanai a ma’adanar tafi-da-gidanka na “Cloud Computing”, kuma a duk sadda kake son komawa gare su, za ka kunna data ne a wayarka ko kwamfutarka, sai ka hau don ta’ammali dasu.

Misali, ina amfani da tsarin Google Drive wajen adanawa da taskance dukkan makalolin da ake bugawa a wannan shafi naku mai albarka.  Haka dukkan hudubobin da nake rubutawa a dukkan mako, da ma lissafin rabon gado da nake yi idan bukata ta tashi, duk ina dora su ne a kan wannan ma’adana ta Google Drive.  Idan na sauya wasu bayanai daga cikin abin da na rubuta a baya, ko na kara wasu bayanai, ko na goge wasu, da zarar na jona kwamfuta na ko wayar salula da Intanet, nan take wadannan bayanai za su sabunta kansu kai tsaye, ba bata lokaci.  Haka idan ina bukatar bayanan, zan kunna datar wayata ne, ko in jona kwamfuta na da Intanet, sai in hau.  Idan na gama in sauka.  Wannan shi ne nau’in bayanan na farko da ake samarwa da adana su ta amfani da tsarin “Cloud Computing”.  Manufar samar dasu ita ce don adanawa don amfani dasu nan gaba.

Nau’i na biyu su ne bayanan da ake samarwa don amfani dasu nan take; ba bukatar sarrafa su balle adana su don amfanin gaba. Misalin ire-iren wadannan bayanai dai sun hada da hotunan bidiyo da muke kallo kai tsaye daga shafukan Intanet, ko shirye-shiryen rediyo da muke saurare ko wakoki, kai tsaye, ko kuma na’ukan bayanan da na’urorin sadarwa ke samar dasu don gano cututtuka.  Kamar su na’urar daukan hotunan jikin dan adam, wacce take hasko bayanai ta fuskar kwamfuta (Digital Scanner), da na’urorin hasashen yanayin zafi ko sanyi ko saukan ruwan sama, kai tsaye (Meterological devices) da dai sauransu.  Ire-iren bayanan da ake samar dasu ta wadannan hanyoyi, duk ana amfani dasu ne kai tsaye, nan take; ba bukatar adana su ko aika su wani wuri don sarrafa su.

Sai nau’in bayanai na uku kuma na karshe, su ne nau’ukan bayanan da suke bukatar bayanan an samar dasu, a sarrafa su, sannan ana iya bukatarsu a kowane lokaci nan gaba.  Ire-iren wadannan bayanai sun hada da bayanan da ake taskance a asibitoci na zamani, ta hanyar na’urorin sadarwa, masu dauke da bayanan mara lafiya masu mahimmanci.  Da bayanan da na’rorin hasashen yanayi ke samarwa da aika su cibiyoyin bincike don amfani dasu. Da kuma irin bayanan da muke musayarsu kai tsaye, don biyan bukatun kasuwanci ko hada-hadar kudi da sauransu.  Misali, idan kaje banki don cirar kudi, sai an tantanceka don tabbatar kaine mai taskar ajiyar, sannan a biya ka.  Wadannan bayanai da za a tambayo daga kwamfuta, ba a nan bankin suke ba.  Suna jibge ne a wata uwa duniya.  Ta yiyu ma ba a Najeriya asalin ma’adanar take ba.  Wannan shi ne abin da ke faruwa ga Hukumar Zabe na kasashen dake amfani da hanyoyin sadarwar zamani wajen karba da sarrafa bayanan masu jefa kuri’a, ko ma kurkun da ake jefawa, kai tsaye.  Asalin bayanan na ajiye ne a wani wuri daban, wanda a aka kintsa ta amfani da fasahar “Cloud Computing”.

Wadannan na’ukan bayanai duka a halin yanzu ana amfani da fasahar “Cloud Computing” wajen adanawa da kuma sarrafa su.  Sai dai, kasancewarsu bayanai ne da ake bukatarsu kai tsaye, don amfanin yanzu-yanzu, musamman abin da ya shafi rayuwar mutane a asibiti, yasa dole ya zama duk sadda aka bukacesu a samesu kai tsaye, ba saibi, ba jinkiri, kuma cikin aminci da inganci.  A nan ne gizo ke sakar.  Domin  fasahar “Cloud Computing” na da nakasu wajen musayar bayanai na kai tsaye; akan samu tsaiko. A wasu lokuta kuma bayanan su gurbace.  Haka kuma, idan babu Intanet, ba za ka ma samesu ba.  Wadannan dalilai ne suka sa a yanzu ake hankoron samar da tsari mafi inganci, kuma wannan tsari na girke ne a fasahar “EDGE Computing.”

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.