Shawarwari Ga Gwamnatin Tarayya Kan Hanyoyin Ciyar Da Najeriya Gaba A Fannin Kimiyya Da Ƙere-Ƙere (2)

Kafin mu tsunduma cikin shawarwari, zan so tunatar da Mai Girma Shugaban Ƙasa kan ma’aunai da za su haska mana halin da ƙasarmu take ciki.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 23 ga watan Yuni, 2023.

119

Muna Da Arziƙi

Kamar yadda Mai Girma Shugaban Ƙasa ya sani, alal haƙiƙa wannan ƙasa Allah ya hore mata tarin albarkatun ƙasa da na sararin samaniya.  Ba wai tsabar kuɗaɗe da muke samu daga cinikin danyen mai nake nufi ba; tsantsar arziƙin ƙasa nake nufi. Bayan tarin albarkatu irin su azurfa da zinare da tagulla da nau’ukan ƙarafa da Allah ya tara mana a ƙarƙashin wannan ƙasa tamu, ita kanta ƙasar da muke takawa a maƙare take da albarka irin ta noma.  Kada mu mance, shekaru kusan sittin da suka gabata, lokacin da ƙasar Malesiya tazo da ƙoƙon baranta neman irin shuka na kwakwar manja, bayan mun bata ta tafi da shi ƙasarta, ta shuka, wannan iri bai yi kai ba.  Saboda yanayin ƙasarsu bai da sinadaran da wannan itaciya ke buƙata.  Sai da suka dawo Najeriya, suka debi ƙasarmu cikin jirgin ruwa, suka tafi da shi.  A can ne suka gudanar da bincike mai kyau kan irin sinadaran da wannan ƙasa tamu ke ɗauke dasu, sannan suka cakuɗa wannan ƙasar da suka ɗebo daga Najeriya da nasu ƙasar, sannan suka fitar da wani irin ƙasa na musamman da zai iya baiwa wannan itaciya ta kwakwar manja sinadaran da take buƙata don samar da ‘ya’ya.

A yanzu duk duniya babu ƙasar da ta kai ƙasar Malesiya arziƙin kwakwar manja.  Daga tuwon siddin mota har zuwa tsantsar manjar miya, wannan ƙasa na sarrafawa – domin babu abin da take watsarwa daga itaciyar kwakwar manja.  Idan har sai da ƙasar Malesiya ta wahala wajen tarbiyyantar da ƙasarta kafin ƙasar ta iya ɗaukan wannan shuka, me za a ce ga ƙasarmu?  Yanzu idan kaje Kudancin Najeriya, za ka samu gonakin kwakwar manja sun zama saura.  Idan mai gonar ya ga dama ya noma, ko kuma ya mayar da itaciyar zuwa tulun banmi, ya rika tatsa yana sha; ba Ruwan Hukuma da wannan.

Ta ɓangaren yanayi kuma, wato Weather, Allah ya mana arziƙi har babu iyaka.  Wani Darakta cikin ma’aikatun gwamnatin tarayya ya taɓa bani labarin ziyarar da ya kai ƙasar Amurka inda ya haɗu da wani Farfesa masanin yanayi.  Bayan sun tattauna, sai baturen ke tambayarsa daga wace ƙasa ya fito, ya ce shi ɗan Najeriya ne.  Sai baturen yace masa, ai ya daɗe yana burin zuwa wannan ƙasa tamu, domin ya daɗe yana bincike (na karatu tsantsa) dangane da yanayin ƙasarmu.  A ƙarshe sai ya sanar dashi cewa, duk wani yanayi na mahalli da ake dashi a sauran ƙasashen duniya, to, akwai irinshi a Najeriya.

- Adv -

Wani babban malamin musulunci ya bamu wani labari mai ban dariya da takaici, shekaru kusan goma sha shida da suka wuce, inda yace wani ɗan ƙasar Sin (Chinese) ya kama hanya zuwa ƙasar Abiya (Abia State) dake Kudu maso gabashin ƙasar nan.  Yana cikin wata tawaga ce ta ‘yan Najeriya, suna tafiya a cikin mota.  Da suka fara shiga kurmi, sai wannan mutumin ya fara mamakin irin yadda Najeriya ke noma babu ƙaƙƙautawa.  Sai ɗaya daga cikin ‘yan Najeriya dake tawagar ya tambaye shi, me ya gani?  Sai yace ai ya ga ko ina ya duba, sai ya ga shuki ne zalla; gaba ɗaya ƙasa ta zama koriya!  Bai san duk tarin ciyayi bane da gamyayyaki waɗanda ruwan sama ya tsirar dasu; kurmi ne ya gani tsantsa.  Daga nan sai aka sanar dashi cewa ai duk wannan tarin ciyayin Allah ne da yake ciyar da dabbobi dasu; ba wai shuka su aka yi ba.  Sai mamaki da baƙin ciki ya kama shi nan take.  Ya ce a ƙasarsu sai sun yi renon ƙasa sun cakuda ta da wasu dabarun kimiyya sannan take musu yadda suke so.  Tare da haka, ƙasar Sin na cikin ƙasashe masu ciyar da duniya a bangaren noma.  Labarai makamantan wannan ba za su kare ba.

Mai Girma Shugaban Ƙasa, manufar bayanan da suka gabata dai shi ne, don tabbatar da cewa muna da arziƙin da zai iya juya wannan ƙasa tamu ta shallake kowace ƙasa ne wajen ci gaba a kowane fanni a duniya.  To amma kaico, kamar yadda larabawa ke cewa: ga rakumi ɗauke da tulun ruwa a cikin sahara, ƙishirwa na gab da kashe shi, saboda bai samu wanda zai sauke masa wannan ruwa ba balle ya kwankwaɗa. Bayan waɗannan bayanai taƙaitattu da muka koro kan albarkatun ƙasarmu, shin, a wani matsayi muke yanzu?

Wasu Ƙa’idoji Shida

Kafin mu tsunduma cikin shawarwari, zan so tunatar da Mai Girma Shugaban Ƙasa kan ma’aunai da za su haska mana halin da ƙasarmu take ciki.  Malaman Kimiyya da Ƙere-ƙere suka ce akwai wasu sifofi guda shida da duk ƙasar da ta cika su, to, ta tabbata naƙasasshiya a fannonin ci gaban rayuwa.  Siffa ta farko, idan ta kasa ƙera manyan injinan sarrafa abubuwa; daga noma zuwa ƙere-ƙere, misali irin su katafilolin noma da na sharan hanya, da na haƙo abubuwa daga ƙarƙashin ƙasa, da jiragen ƙasa, da motoci, da wasu injinan zaƙulo abubuwa daga ƙasa ko ɗora su a sama, to ba a ƙirga ta cikin sahun ƙasashen da suka ci gaba.  Idan muka dubi Najeriya za mu ga cewa haka muke.  Ko keken ɗinki na zamani mai aiki da wutar lantarki ba na tunanin muna ƙera shi a ƙasar nan, balle na hawa, balle babur, balle mota, har a kai ga katafilar noma (tractor).

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.