Hamshakin Mai Kudin Duniya, Mista Elon Musk, Ya Saye Kamfanin Twitter Kan Kudi Dala Biliyan 44 ($44Bn)

Mista Elon Musk, wanda shi ne mai kudin duniya a halin yanzu, ya kasance cikin shahararrun mutane dake amfani da shafin Twitter sosai, kuma ya shahara da ra’ayinsa na ganin rashin dacewar hanyar da kamfanin Twitter ke bi wajen rufe shafukan mutane, musamman mutane masu kima, saboda saba wa ka’idar da aka girka cikin manhajar.  – Jaridar AMINIYA, ranar Jumma’a, 6 ga watan Afrailu, 2022.

388

Bayan watanni ana tattaunawa, a karshe dai shugabannin kamfanin Twitter sun sallama wa tayin da Elon Musk ya musu na sayan kamfanin gaba daya kan zunzurutun kudi dala biliyan arba’in da hudu ($44 bil), kwatankwacin naira tiriliyon 24 (N24 trl) kenan kudin Najeriya.  Wannan sallamawar ta biyo bayan amincewar shugabannin kamfanin ne, inda Elon Musk ya zama shi ne na karshe kuma wanda yafi bayar da tayi mafi girma da tsoka don sayan kamfanin na Twitter.

Ranar Litinin (25 ga watan Afrailu, 2022) da ta gabata ne sashin Hausa na BBC ya tattauna dani kan wannan al’amari da masana ke ta cecekuce akansa tsawon wannan mako, don baiwa masu sauraronsu damar fahimtar lamarin a mahangar fannin sadarwa.

Da farko dai, kafin Elon Musk ya mika tayinsa na sayan Twitter, kamfanin ya dade yana fama da ‘yan matsaloli musamman na rashin ci gaba ta bangaren adadin masu rajista, idan an kwatanta shi da sauran shafuka irin su Facebook da Instagram, sai kuma karancin kudaden shiga da yake fama dashi.  A daya bangaren kuma, shafin Twitter yayi fice wajen dakushe abin da yake kira “munanan ra’ayoyi” ko duk wani zance da ya saba wa ka’idojinsa na mu’amala.  A cewarsa, yana hakan ne don rage yawaita da yaduwar kalaman batanci ga wata al’umma, ko kabila, ko addini, da kuma yunkurin dakile hanyoyin yaduwa da bunkasar sakonnin bogi da wasu ka iya wallafawa a shafin don kokarin cinma wata manufa boyayya.

Tasirin wannan ka’idar ta fito fili a lokutan da kamfanin yayi ta rufe shafukan manya kuma shahararrun mutane da shugabannin wasu kasashe, sabo da saba wannan ka’ida tasa.  Daga cikinsu akwai shahararrun mawaka da sanannun mutane a duniya, ciki har da tsohon shugaban kasar Amurka Mista Donald Trump da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.

- Adv -

Mista Elon Musk, wanda shi ne mai kudin duniya a halin yanzu, ya kasance cikin shahararrun mutane dake amfani da shafin Twitter sosai, kuma ya shahara da ra’ayinsa na ganin rashin dacewar hanyar da kamfanin Twitter ke bi wajen rufe shafukan mutane, musamman mutane masu kima, saboda saba wa ka’idar da aka girka cikin manhajar.  Duk da cewa da dama cikin masu rajin kare hakkin dan adam da kokarin tabbatar da tsarin dimokiradiyya a duniya sun gamsu da wannan mataki na kamfanin Twitter, saboda dakushe abin da suka kira: “Yaduwa da bunkasar labaran bogi, da kalmomin batanci a kafafen sada zumunta.”

Jim kadan bayan karban tayinsa da shugabannin kamfanin suka, Mista Musk ya sanar da cewa, lokaci ya yi da “shafin Twitter zai samar da sarari ga sakakkiyar ‘yan fadin albarkacin baki.”   Masu fashin baki da lura da fannin sadarwa a duniya sun nuna damuwarsu da wannan zance nashi, inda suka ce kamar hannunka mai sanda yake yi kan abin da zai biyo baya da zarar ya karbi ragamar shugabancin wannan kamfani.  Wannan, a cewarsu, abin damuwa ne sosai.  A nata bangare, Cate Blanchett, daya daga cikin masu goyon bayan matakin da Twitter ke dauka wajen yaki da labaran bogi ta hanyar rufe shafukan masu laifi, ta sanar da cewa: “Sayan kamfanin Twitter da Mista Musk yayi, abu ne mai hadarin gaske.”  Tace abin da wannan yunkuri ke nufi shi ne akwai yiwuwar nan gaba ya bude wa mutane irin su Donald Trump shafukansu da aka rufe a baya, don su ci gaba da yada barnar da a suka fara amma aka dakile su.  In kuwa hakan ya faru, to, labarun bogi da miyagun halayyar masu yada su zai karu har ya kazanta.  Har yanzu dai babu wani jawabi da Mista ya fitar kan matakan da zai bi, da ire-iren sauyin da za a samu a wannan kamfani bayan ya karbi ragamar shugabanci.

Wannan ciniki dai zai sauya matsayin kamfanin Twitter daga kamfanin kasuwanci na jama’a (Public Company), zuwa kamfanin mutum daya.  Wanda hakan ke nufin, duk wani mai hannun jari a kamfanin daga yanzu sai zai sayar wa Mista Musk ne kai tsaye, ba wai kasuwar hannun jari (Stock Exchange) zai je ya sayar ba. Mista Musk dai ya sayi kowane hannun jarin kamfanin ne a kan $54.20 na kasar Amurka. Kusan naira dubu 30 da doriya kenan nairan Najeriya.

Daga sadda ya karbi ragamar shugabancin kamfanin, ana sa ran samun sauye-sauye masu yawa, musamman wajen canza tsarin tattaro bayanai da shafin ke dauke dashi, wato: “Twitter Algorithm”, da tsarin mu’amala da kamfanonin dake dora tallace-tallace a shafin, sai kuma canza tsarin wallafawa da bitar sako a shafin.  Mista Musk dai tuni ya fara ba da shawarar samar da “maballin gyara sako” (Edit Button) a Twitter, kamar yadda yake a shafin Facebook.  Abin da masana da dama ke ganin bai dace ba, saboda hakan zai rage ingancin sakonnin da ake wallafawa, tare da bai wa wasu damar yaudarar mutane.  Misali, mutum na iya rubuta wani ra’ayi wanda ke daukan hankali.  Sai bayan jama’a sun rajja’a wajen goyon baya da adadi mai yawa, a karshe kuma ya sauya asalin sakon da wani abu daban.

Ya zuwa yanzu dai ba wanda zai ce ga hakikanin alkiblar Mista Musk dangane da garambawul din kamfanin.  Amma akwai rade-radin cewa wasu daga cikin manyan injiniyoyin kamfanin sun sha alwashin cewa muddin tunaninsu ya zama gaskiya kan abubuwan da ake zaton zai yi wanda ya saba wa ka’idarsu, za a fice daga kamfanin ne ba tare da wani bata lokaci ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.