Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (21)

Kashi na 21 kuma na karshe, cikin jerin makalolin da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Asha karatu lafiya.

342

Idan Matsala ta Auku

A baya na bayyana cewa a kasashen Turai da Amurka, da zarar an sace zatinka har ta kai an aikata ta’addanci, kuma har jami’an tsaro suka fara nemanka, to, aiki ja ya sameka, in ji mutan Dan Ja dake Katsina.  Kamar yadda a yanzu a Najeriya, Allah kiyaye ya kuma tsare, a sace wa mutum katinsa na ATM, ko katin shedar zama dan kasa (National ID Card), ko bayan da yake amfani dasu wajen aiwatar da cinikayya a shafukan Intanet, har aje a aikata ba-daidai ba dasu, da zarar jami’an tsaro sun gano wannan badakala, ba wanda za a nema sai kai.  Ko kuma, wani ya sace bayananka na Facebook misali, ya haye shafin ya dinga aikata shegantaka a kai, har jama’a suka fara kiranka suna tambayar me ke faruwa ne?  Mun ga kaza da kaza a shafinka.  Idan irin haka ta faru, meye abin yi?

Da farko dai, kamar yadda na sanar a baya, a Najeriya babu wani tsari na musamman da aka sanar kan ire-iren wadannan matsaloli, ta la’akari da irin mahallin da suke faruwa.  Amma akwai wasu tsare-tsare na al’ada da dokar kasa ta tanada don magance hakan.  Na farko dai idan ya shafi taskarka na banki ne, kana iya sanar da bankinka kai tsaye, cewa an sace katin ATM dinka, ko an kwace daga hannunka, ko kuma an sace bayanan dake dauke cikin katin, ko kuma an sace bayanan da kake amfani dasu wajen hawa shafin dake dauke da taskar ajiyarka na banki, kuma an aiwatar da cinikayya ko cire kudi ko wani abu makamancin hakan, ba tare da sani da kuma yardarka ba.  Nan take bankin zai kulle wannan kati naka.  Idan an ciri kudade daga taskar kafin ka farga, ya danganci daga inda sakacin ya samo asali.  Idan ta bangarenka ne, to, wannan kai za ta shafa kai tsaye.  Idan kuma ta bangaren bankin ne aka samu wannan sakani (wanda gano hakan gareka zai yi wuya, kuma su ma zai yi wuya su gaya maka gaskiya idan su ne abin ya shafa), su za su dauki dawainiyar biyanka.  Amma fa sai ka dage.

Idan kuma ta’addanci aka aiwatar da katin naka, wanda ya shafi kisa, ko fashi da makami, ko sata, ko wani abu makamancin wannan, to, a nan kan wajen jami’an tsaro zaka tafi kai tsaye.  Idan ka sanar dasu abin da ke faruwa, za su baka takarda ta musamman ka cike mai dauke da sanarwar cewa abu kaza ya faru da kai a rana kaza a wuri kaza.  Wannan zai taimaka wajen baka kariya ko da nan gaba wasu sunzo suna cewa kaine ka aiwatar da wannan aika-aika a kansu, sanadiyyar shedar da suka gani na katinka ko wasu bayanai masu alaka da kai kai tsaye.  Sannan har  wa yau za ka je kotu kayi rantsuwa, cewa abu kaza din nan da ka gaya jami’an tsaro cewa ya faru, lallai gaskiya ne ba karya ba.  Wadannan takardu biyu su za su taimaka wajen baka kariya nan gaba, da kuma taimaka maka wajen samun sabon kati ko shedar da ka rasa sanadiyyar wancan sata ko ta’addanci da aka a kanka.

- Adv -

Idan kuma shafi ne a dandalin sada zumunta, nan kuma garzayawa za kayi wajen dakile hakan.  Idan an sace shafin ne, ta yadda ba ka iya hawa, to, dole ne ka bude wani shafi, ko ka sa abokanka su rubuta a kan farfajiyar shafin da aka sace, cewa duk rubutun dake bayyana a wannan shafi daga rana kaza, ba kai bane kake rubutawa.  Maimakon haka ma, an kwace maka shafin ne, ba ka iya sarrafa shi.  Don haka, ai hattara; kada wani yayi alaka da wanda ke sarrafa shafin ta kowace hanya.  Har wa yau, idan wanda ya kwace shafin yana aikata wasu abubuwa da suka shafi ta’addanci ne ga al’umma, na zance, ko na aiki, to, dole ne ka sanar da jami’an tsaro cewa ga abin da ke faruwa.  Kada yaje ya aikata abin a aikace, azo ana nemanka.

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, na tabbata mai karatu ya fahimci abubuwa da dama kuma ya dauki darasi.  A kullum ka zama mai takatsantsan wajen mu’amala da mutanen da baka taba saninsu ba, a shafukan Intanet.  Ka sani, kana da mutunci, da yake dole ka kare.  Kana da addini, da ya zama dole ka kare shi.  Kana da al’adu kyawawa, da suka zama dole ka basu kariya.  Kana da iyali, da ya zama dole ka mutunta su.  Kana da ‘yan uwa da dangi da iyaye, da suka zama dole ka karrama su ta hanyar kauce wa duk wata barna da za ta iya janyo musu abin kunya.

A kullum masu neman aikata barna ba su gajiya, kuma iya tausayinka gare su, iya yadda za su shige ka.  Don haka, wajibi ne ka zama mai takatsantsan wajen irin mu’amalar da kake da duk wani wanda baka sanshi ba, ko wanda ka sani amma ba natsatsse ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.