Sakonnin Masu Karatu (2020) (11)

Bayani Kan Hasken "Northern Light"

An guba wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 25 ga watan Satumba, 2020.

95

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan alhairi a gareka. Shin, hasken da ake cewa “Northern Light”, akwai shi da gaske? Kuma yaya yake samuwa? Kuma a ina ake ganinsa? Daga: Umm Haidar, Gombe.

Wa alaikumus salam, barka dai Maman Haidar. Ina godiya da jaje da kuma addu’o’i. Allah saka da alheri, amin. Dangane da wannan haske da a kimiyyance ake kira da suna: “Northern Light”, tabbas akwai shi da gaske. Suna da aka fi saninsa dashi shi ne: “Aurora”. Sannan akan kira shi da sunan: “Southern Light”, ko kuma “Polar Light.” Nau’i ne na haske dake bayyana, galibin lokutan dare, daga bangaren kuryar arewaci da kuma kudancin duniya. Bangarorin dake dauke da manyan dirkokin duniya. A fahimta, ba ina nufin dirkar dake dauke da duniyar a Zahiri bane. Kalmar da malaman kimiyya ke amfani da ita ita ce: “Pole”; kamar wata dirka da ake ishara da ita don nuna kusurwar duniya. Wadannan bangarori biyu – kudanci da arewa – musamman bangaren da yafi kowane bigire sanyi da kankara a duniya dake can saman kasar Rasha da ake kira: “Antactic Region”, su ne ke dauke da manyan sinadaran maganadisun dake tabbatar da ka’idar janyo nauyi kasa, wato: “Force of Gravity”, wanda kuma a kan wannan tsari ne duniya ke gudanuwa da ikon Allah.

Kamar yadda na fada a baya, wannan haske ne dake bayyana mai launi da garwayen shudi, ko zallan shudi, a wasu lokutan, cikin duhun dare. Malaman kimiyya, a iya abin da suka fahimta (Allah shi ne mafi sanin daidai), sun ce akwai wasu nau’in sinadarai da iskar dake wannan bigire ke debowa, yayin da take (ita iskar) tasowa da karfi. Haduwan wadannan sinadaran a cikin iskar, kasancewar nau’uka ne daban-daban, shi ke haddasa samuwar wannan haske da ake kira: “Polar Light,” ko “Northern Light”, kamar yadda kike jin ana kiransa ko ambatonsa. Idan muka yi la’akari da bayanin da ya gabata, za mu fahimci wannan iska tana bayyana ne a wurare biyu: wuri na farko shi ne bigire mafi tsayi ko bisa daga sama, wato bangaren arewaci kenan. Da kuma bigire mafi gangare daga kasa, wato bangaren kudanci kenan. Sannan wadannan wurare suna da alaka da juna wajen haduwar babban maganadisun dake tabbatar da ka’idar janyo nauyi kasa, wato: “Force of Gravity.”

Wannan shi ne abin da Malaman kimiyyar wannan zamani suka tabbatar. Amma, kamar yadda na sha fada a baya, abubuwa irin wadannan, mafi ingancin dalilin samuwarsu na ga Allah ne Madaukakin sarki. Wannan ba ya nuna cewa abin da Malaman kimiyya suka gano ya zama ba haka ba, kai tsaye. A a. Akwai dalilai na Zahiri na faruwan abubuwa. Wannan shi ne abin da galibin binciken kimiyya ke iya ganowa ko tabbatarwa. Kuma ko shi dinma, ba lalai ya zama duka ba, saboda nakasar fahimtar dan adam, da kuma nakasar dake tattare da na’urar binciken kimiyya. Dalili na biyu kuma shi ne karfin ikon Allah wajen tabbatar da kaddarar da ya zana tun fil azal, wanda kuma ke bayyana cikin halittunsa da a kowane lokaci.

Wannan shi ne dan takaitaccen bayanin da zan iya yi. Da fatan Malama ta gamsu.

- Adv -

Assalamu alaikum Malam Abdullahi Baban Sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya tare da daukacin iyalanka. Allah yasa haka amin ina maka fatar alhairi. Hakika ina matukar karuwa da irin kasidunka da kake rubutawa da kuma hirarraki da BBC Hausa suke yi da kai akan fasahar sadarwa. Allah Ya kara basira da daukaka. Na Gode. Daga Bello Isiyaku, Birnin Fulani, Jihar Gombe.

Wa alaikumus salam, Malam Bello. Na gode matuka da wadannan addu’o’i. Allah saka da alheri, amin. Lallai ina matukar jin dadin jin cewa dan abin da nake gabatarwa a wannan shafi ko sashen Hausa na BBC a lokuta daban-daban, yana yin tasiri wajen karuwar al’umma. Wannan shi ne babbar manufar kamfanin Media Trust na daukan nauyin ire-iren wadannan rubuce-rubuce a shafukan jaridun kamfanin gaba daya. Allah saka musu da alheri, kuma ya kara tabbatar da darussan a zukata da kwakwalen masu karatu. Na gode matuka. Allah saka da alheri.

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya kokari? Da fatan komai yana tafiya daidai. Tambayata ita ce: mene ne bambancin babbar manhajar wayar salula ta “Android 10” da kuma “UMEI 10” na kamfanin Huawei.

Wa alaikumus salam, barka dai. Da farko dai, “Androi 10” nau’i ne na babbar manhajar wayar salula na Android, zubi na goma kenan. Wannan ita ce Zubin mafi sabunta a yanzu. Kamfanin Google ne yake mallakar wannan babbar manhaja ta Android. Dukkan sauran kamfanonin kera wayar salula suna karban lasisi ne daga kamfanin Google don dora wannan babbar manhaja a wayoyinsu na salula. Asalin manhajar daya ce, amma akwai bambancin siffa da dabi’u a tsakanin na wayoyin salular kamfanoni daban-daban. Misali, idan ka dauki babbar manhajar android dake wayoyin salular kamfanin Samsung da na Google da kuma na kamfanin Sony, ko Hauwei. Idan ka dauki wayoyin, za ka ga da bambanci. Wannan ke nuna cewa kowane kamfani yana sauya yanayin babbar manhajar ne, don kayatar da wayoyinsa. Wannan sauye-sauye da suke yi, don samar da nau’in babbar manhajar Android da siffofinta suka sha bamban da na sauran kamfanonin waya, shi ake kira: “Android Skin.” Kamfanin Huawei shi yana amfani da babbar manhajar Android ne a galibin wayoyinsa, amma Kalmar “UMEI 10” da kake gani, nau’in “Android Skin” ne da kamfanin Huawei ya samar don kayatar da nasa wayoyin. Shi tsarin “Android Skin” nau’i ne na manhaja da ake dora shi akan babbar manhajar Android. Duk abin da kake gani na kyale-kyle idan ka kunna waya, da wanda kake gani wajen shigar da Kalmar sirri, da wanda kake gani na tsari da launin fuskar wayar, duk manhajar “Android Skin” ne.

Wannan shi ne dan takaitaccen bayanin da ya sawwaka. Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.