Sakonnin Masu Karatu (2019) (10)

Matsalar Intanet a Wayar Salula Nau'in Lumia

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Afrailu, 2019.

219

Assalamu alaikum Baban Sadik, ni tambayata ita ce: ina da waya kirar Lumia wajen shekara 3 kenan amma ta ki yin setting, kuma ba ta shiga yanar gizo.  Har ofishin MTN na kai ta amma abin ya gagara.  Daga Aisha Tudun Maliki.

Wa alaikumus salam, barka dai Malama Aisha.  Duk da cewa baki yi cikakken bayani kan kirar da nau’in Lumia din ba, ga alama tsohuwar yayi ce.  Abin da ke faruwa shi ne, kamfanin Microsoft, wanda shi ne mamallakin wadannan nau’ukan wayoyin salula na zamani, ya daina bai wa tsofaffin nau’ukan wayoyin Lumia sakonnin tagomashi da zai kara musu inganci ta hanyar sabunta su.  Abin da wannan zance ke nufi dai a fayyace shi ne, ire-iren wadannan wayoyin salula an daina yayinsu.  Na farko kenan.

Na biyu, ban san me ke damun wayarki ba wanda ya hana ta iya tagaza komai, amma ga alama matsalarta ba karama bace; tunda har kin kai ta ofishin MTN amma su ma sun kasa yin wani abu, kamar yadda kika fada.  Shawarata dai ita ce, in da hali a samu sabuwa a saya.  Akwai wayoyi nau’uka daban masu inganci, kuma masu araha, wadanda za su iya yin komai babbar waya za ta iya yi ta hanyar yin kira da amsa kira da hawa Intanet.  Wadannan sun fi samar da natsuwa da kwanciyar hankali.  Amma gyara tsohuwar waya wacce kamfanin da ya samar da ita ma ya daina sabunta bayananta, kashe kudi ne kuma ba lalai a samu cikakkiyar biyan bukata ba.

Wannan ita ce shawarata, kuma ina miki fatan alheri.  Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah ya taimaki gwanina a duniyar intanet. Ban ga mutum mai son taimakon al’umma ko son ci gaban al’umman Hausawa a wannan fanni irinka ba. Wallahi ban ganshi ba har yanzu. Allah ya taimakeka akan wannan manufa naka. Daga sabon mai bibiyarka Muhammad bin Muhammad, Numan, Adamawa State Nigeria.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Muhammad, mai babban suna.  Ina godiya matuka da addu’o’inka da kuma kyautata mini fata da kayi.  Duk abin da kake ganin yana birgeka daga gareni, kyautar Allah ce da dacewa cikin ganin damarsa.  Wallahi ba hikima da kokarina bane. Fatana shi ne, duk abin da nake rubutawa, wanda sakamakon bincike ne da nake gudanarwa, da kuma fahimtata kan abubuwan da nake karanta, ya zama mai amfani da ga al’umma, ya samar da fa’ida ta hanyar inganta fahimta da tunanin wadanda suke karantawa.  Abin da yake kuskurene kuma, Allah nusar dasu su gane hakan, kada su hakkake kuskure a cikin kwakwalwa da zukatansu.

- Adv -

Ina maka fatan alheri a ko ina ka samu kanka.  Na gode matuka.  Allah saka da alheri.

Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah ya kara maka kwarin gwiwa, da kwakwalwa da basira akan wannan shafi naka.  Allah ya kare mana kai daga sharrin masharranta.   Domin kana ilmantar damu ta bangarori da dama a rayuwa kamar su: fannin sadarwar waya, da kwamfuta, da ilmin sararin samaniya, da fasahar haske, da tauhidi, da asalin hallita da sauransu.  Allah ya jarabceni da son kwamfuta da kuma ilmin waya.  Ina karuwa sosai.  Sanadiyyar haka na soma kasuwancin sayar da kwamfuta har ma da TV Plasma daga Legas zuwa Kaduna.  Sunana: Nuhu Abdullahi.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nuhu.  Ina matuka farin cikin da jin cewa wannan shafi ya taimaka maka wajen jefa maka sha’awa da son wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa, kuma cikin dacewar Allah har hakan ya zama sanadiyyar hanyar kasuwanci gareka.  Na gode matuka da addu’o’inka.  Ina rokon Allah ya tabbatar dakai kan wannan kasuwanci sannan ya albarkaci dukkan abin da ka taba ko zuba na jari a ciki.

Daman rayuwa haka take; a yayin da wasu ke karatu su bar karatun a inda suka karanta shi, wasu kan karanta ne su dauke shi cikin kwakwalwa da zuciyarsu.  Hakika ana son duk abin da ka karanta, ka nanata shi cikin zuciyarka, ka jinjina shi cikin kwakwalwarka, sannan tsinci abin da ka tsinta a ciki.  Wannan zai taimaka maka a duk sadda kaci karo da wani abu mai alaka dashi.  In da hali ma ya zama sanadiyyar tsira a gareka duniya da lahira.

Kamar yadda nasha nanatawa a wannan shafi, wannan fanni na bincike kan kimiyya da fasaha, asali ba a makaranta na karance shi ba, kai tsaye.  Hasali ma, idan ka kebe tilasci na tsarin makaranta da yace dole kowane dalibi ya dauki darussan kimiyyar sinadari da kere-kere (Physics and Chemistry) a ajinsa na hudu a sakandare sadda nake makaranta, ban taba karantar wadannan fannoni ba sai bayan shekaru kusan goma sannan.  Amma a hakan, abubuwan da nake rubutawa a wannan shafi yayi tasiri ga daliban dake karantar wannan fanni ba wai a sakandare kadai ba, hatta ga wadanda ke matakin jami’a.  Kai, hatta wadanda ke karantar digiri na uku sun amfana da rubuce-rubucen da wannan shafi ke bugawa a duk mako.

Don haka, ina kara godiya ga Allah sannan ga hukumar Media Trust da suke daukan nauyin buga wadannan rubuce-rubuce tun shekarar 2006.  Allah saka wa kowa da alheri, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.