Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (20)

Kashi na 20 cikin jerin makalolin da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Asha karatu lafiya.

203

Hanyoyin Kariya (4)

Takatsantsan Wajen Yada Bayanai a Dandalin Sada Zumunta

Duk wanda ya bude shafi a dandalin sada zumunta, to, da wahala kaga bai rubuta wani abu ba, ko da kuwa daga wajen wani ya kwafo.  Wannan ita ce al’adar mahallin.  Kuma ba hakan bane laifi.  Inda lamarin yake shi ne:  me ka rubuta ko zuba a shafinka?  Da yawa cikin mutane kan tona wa kansu asiri a shafukansu na dandalin sada zumunta.  Su suke aibanta kansu a cikin hotuna a cikin zance.  Su suke janya wa kansu hassada, wanda a karshe zai bayu zuwa ga saryar da mutuncinsu da kuma dukiyarsu.  Amma ba kowa ya fahimci  haka ba.

Su ‘yan Dandatsa masu shawagi don kalato bayanan mutane a ire-iren wadannan wurare, sun fi saurin sace mutum mai yawan surutu da alfahari, da fadin abin da ba a tambayeshi ba, kuma mara alfanu ga rayuwa ko addininsa.  Nan take sai su sa masa ido.  Misali, akwai wasu mutane, kowane irin yanayi suke ciki, sai sun rubuta shafukansu.  Idan cin tuwo suke, sai sun fada, tare da dora hoton tuwan ma.  Idan rashin lafiya suke, sai sun fada, ba ma fada kadai ba, sai sun dauki hotonnsu a kan gadon asibiti, sun dora.  Idan mutuwa aka musu sai sun fada, ba ma fada kadai ba, hatta hoton gawan ma sai sun dora a shafinsu.  Idan mota suka saya sai sun fada, sannan su dora hoton motar a shafinsu.  Idan aiki suka samu, sai sun fada, sannan su dora hoton wasikar tayin aikin da aka basu.  Idan makaranta suka gama, sai sun fada, sannan su dora hoton shedar gama karatun a shafinsu.  Idan tafiya za su yi, sai sun fada, sannan su dauki hotonsu suna tukin mota, ko suna cikin jirgin sama ko na kasa, ko babur ko keke, duk su dora a shafinsu.  Idan kwalliya suka yi, duk sai sun fada, sannan su dora hoton kwalliyar ko “wankan”, kamar yadda Kanawa ke fadi a yanzu, a kan shafinsu.  Kuma galibinsu, kana hawa “Profile” dinsu sai ka gansu tsirara.  Ma’ana ga bayanansu nan a bude, ko sutura babu.  Alamar cewa basu san manufar kasancewarsu a wannan mahallin ba Kenan.  Mai karatu, idan kana cikin ire-iren wadannan mutane, kayi hakuri.  Ba manufata bace in aibantaka.  Shi yasa ma ban ambaci sunan kowa ba.  Manufar ita ce fadakarwa.

Dabi’a irin wannan bai kamaci mai hankali ba, mai manufa a rayuwa da al’ada ba, wanda yasan ciwon kansa.  Don haka mu kiyaye.  Ka sani, irin bayanan da kake rubutawa ko yadawa a shafinka, duk abokanka suna gani.  Idan ba yanzu hukumar Facebook ta canza tsarin ba, hatta abokan abokanka (Friends of Friends), su ma suna gani.

Idan kayi rubutu a shafinka na Facebook misali, jama’a na iya ganin rubutun ta dayan dalilai hudu ne.  Abokanka (Friends) na iya gani, saboda a hankalce su ne amintattun mutane a gare ka.  Na biyu, abokanan abokanka (Friends of Friends) na iya gani, saboda amintuwar dake tsakanin abokanka dasu.  Na uku, duk wanda yaci karo da shafinka a Facebook yana iya ganin abin da ka rubuta a farfajiyar shafinka (Timeline), idan ka bar tsarin a “Public” kenan.  Sannan a karo na karshe, kana iya rubuta bayanai ka boye shi, a shafinka, ba tare da kowa ya iya gani ba sai kai kadai (Only Me).  Wadannan su ne tsare-tsare da suka shafi sirrin bayanai a Facebook, wadanda mai shafi ke rubutawa.  A ka’ida idan ka bude sabon shafi a Facebook, babu wanda zai iya ganin bayanan da kake rubutawa a shafinka sai kai da abokanka kadai.  Sai idan ka canja wannan tsari.

Duk wannan dogon bayani dai ina so in jawo hankulanmu ne kan hadarin dake tattare da abin da muke yi a Facebook musamman, ko Twitter, ko LinkedIn ta bangaren yada bayanai da wadanda ke iya isa ga bayananmu.  Duk abin da ka san zai zama aibi a gareka nan gaba, kada ma ka taba dorawa ko rubuta shi a shafinka na Facebook ko Intanet.

Takatsantsan Wajen Yin Abota a Dandalin Sada Zumunta

- Adv -

Dandalin abota irin na zamani kamar kasuwa ce, wadda a cikinta jama’a kan hadu daga ko ina a duniya.  Wannan kasuwa dai tana da hanyar shiga da na fita. Sannan akwai ka’idojin mu’amala da hukumar kasuwar ta gindaya.  Amma me jama’a ke sayarwa, ko me suke tallatawa, ko me suke aiwatarwa a ciki, ko kuma mutanen kirki ne ko na banza a kasuwar, duk ba damuwar hukumar kasuwar bane, har sai an kai mata kara.  Wannan yasa jabun mutane da jabun shafuka suka fi yawaita a gidajen yanar sadarwar sada zumunta na Intanet.  In kuwa haka ne, shin, mai karatu, ko ka taba zama ka lura da su waye kake mu’amala dasu a shafukanka na sada zumunta?

Babbar manufar bude shafukan sada zumunta musamman na Facebook, zan kara nanatawa, ita ce don mutane da suka san junansu a gari guda, ko wata makaranta da suka taba yi, ko wani taro da suka taba haduwa na addini ko kasuwanci, su samu damar sake haduwa da juna don sadarwa kuma alakarsu taci gaba.  Amma ba a bude wadannan shafuka don yin mu’amala ko abota da mutumin da baka taba saninsa ba.  Amma haka lamarin yake a aikace?  Amsar ita ce: a a.

Daga cikin manyan matsalolin dake jawo hasarar dukiya da mutunci a dandalin abota akwai yawan karban abokai barkatai ba tare da tantancewa ba.  Tabbas ba abu bane mai yiwuwa ace dole sai wanda ka sani a zahirin rayuwa kadai za ka yi abota dashi, amma kuma wannan ba lasisi bane wajen karban kowane irin kwamacala da sunan aboki.   Masu neman abota da mutum a dandalin sada zumunci sun kasu kashi-kashi.

Akwai masu neman abota don karuwa da kai, musamman idan ka shahara wajen rubuce-rubuce masu fa’ida a addini da rayuwa ko siyasa da al’adu.  Wannan daidai ne kuma yana da kyau.  Wannan ya fi shahara a bangaren malaman addini da siyasa da sauran fannonin ilimi.   Akwai masu nemanka da abota saboda sun sanka ne a zahirin rayuwa.  Wannan yayi daidai da manufa da kuma al’adar Facebook, misali.  Akwai masu nemanka da abota kawai don sun sanka a suna sanadiyyar shahara ko sun taba jin sunanka a wajen wasu amma basu taba ganinka ba.  Wannan, ta wata fuskar kuskure ne, musamman idan ba mutanen kwarai bane su, ko kai da ake nemanka da abotan ba mutumin kirki bane.  Wannan ya fi shahara a bangaren ‘yan fim, da marubuta littafan soyayya, da shahararrun ‘yan siyasa da ‘yan jaridu.

Har wa yau, akwai masu nemanka da abota saboda su samu damar kusantarka don wata manufa mummuna.  Wannan ya fi shahara a bangaren ‘yan dagaji, masu mugun nufi kenan.  Suna kusantar ‘yan siyasa kamar yadda suke kusantar shahararrun mata da maza dake wadannan wurare.  Akwai kuma masu nemanka da abota kawai don sun ga garinku daya, ko jiharku daya, ko kunyi makaranta daya – ko da ba tsarekunka bane – ko kuma kuna da ra’ayin siyasa ko addini iri daya.  Akwai kuma masu nemanka da abota ba don komai ba sai don kyaun hoton da ka sa a shafinka, ko hotunanka da ya gani, ko irin nau’in sunanka.  Wannan ya fi shahara a bangaren mata, inda mazaje musamman samari ke nemansu da abota saboda kyaun hoton dake shafukansu ko sunayensu kawai, ba don wata karuwa mai fa’ida ba.  A karo na karshe kuma, akwai masu nemanka da abota don manufar kasuwanci.  Da zarar ka karbe su kawai zasu ta jefo maka tallace-tallace a shafinka da sunan “Tagging.”

Duk wanda za ka karbeshi a matsayin aboki, dole ne kasan daga ina yake?  Idan ka taba saninsa, shin, mutumin kirki ne?  Idan baka taba saninsa ba, akwai alamar gyaruwa tare dashi?  Ta dalilin wa ya sanka?  Mutum nawa ne kuka hada a matsayin abokai tsakaninka dashi (Mutual Friends)?  In kun hada abokai, wasu iri ne?  Masu mutunci ne?  Wasu irin hotuna ne a shafinsa?  Shin, hakikanin hotonsa yasa?  In eh, a wani siffa yake?  In a a, hoton meye a profile dinsa?  Akwai nau’ukan hotuna kusan 100 a Facebook wadanda duk inda na gansu, na san jabun hotuna ne, kuma masu shafukan ba hakikaninsu bane, sannan kuma dole dayan biyu; ko dai ya zama ‘yan madigo ne ko wani kato ne ya bude shafin da sunan mata.  Ka sani, irin yanayin abokanka irin yanayinka.  Masu iya Magana na cewa, sai hali yayi daidai ake abota.  Ana iya gane nagartarka ne da zamaninka, da kuma irin mutanen da ka zauna dasu.  Shi yasa, a tunani mai saiti na addini, babu wadanda suka kai Sahabban Annabawa nagarta bayan gushewar Annabawan.

Rashin tantance mutanen da za ka karba a matsayin abokai ko nemi abotarsu, na taimakawa wajen jajibo miyagu kusa da kai.  Kuma wannan zai basu damar ribatarka ta hanyar abin da kake zubawa a shafinka.

Haka idan ya da kowa kana iya hira a shafinka, tare da fayyace musu rayuwarka gaba daya, babu sirri.  Da yawa cikin miyagu kan bukaci hira da mutanen da suke son zambata, don kara fahimtarsu, da kuma rarakar bayanan da suke nema kai tsaye daga gare su.  Wannan tsari shi ake kira: “Social Engineering”, a ilimin kimiyyar sadarwa na zamani.  Idan ya zama kowa ka tashi hira dashi sai ka fayyace masa rayuwarka, da inda aka haifeka, da garinku, da sana’arka, da watakila ma har da bashi lambar waya ba tare da sanin hakikaninsa ba, wannan kana haka wa kanka ne rami mai zurfi.

Yadda ka zama mai kaffa-kaffa wajen yada bayanai, ka zama mai takatsantsan wajen yin aboka ta mutane.  A duniyar Intanet babu mahalli mafi hadari irin dandalin sada zumunta.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.