Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (13)

Wannan shi ne kashi na 13 daga cikin jerin bayanan da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Asha karatu lafiya.

197

Munanan Tasirin “Satar Zati” (2)

Illoli a Zahirin Rayuwa

A zahirin rayuwa ma akwai illolin dake riskar wadanda aka sace wa zati.  Jama’a, lamarin fa babba ne.  Bayan damuwa da bakin ciki dake haddasa rashin cin abinci, da rashin bacci, da rashin natsuwa na zuci, a zahirin halittar mutum ma wasu illoli na riskarsa, har suyi tasiri ta yadda jama’a ke iya ganewa.  Da farko dai wasu kan kamu da rashin lafiya mai muni, sanadiyyar wancan bakin ciki da damuwa, har ta kai ga an kwantar dasu.  Wannan illa ce mai girma.  Na biyu, wasu kan kasa zuwa aiki, saboda shagaltuwa da wannan matsala.  Domin gaba daya suna rasa daga inda za su fara rayuwarsu ne.  Daga cikin illolin har wa yau akwai yana kai-komo, saboda kokarin gamsar da jami’an tsaro hakikanin halin da suka samu kansu a ciki. Idan matsala ta girmama kuma, kamar yadda mai karatu ya gani a baya, wasu kan kashe kansu.  Domin babbar matsalar da za ta yi ta kai-komo cikin zuciyarsu ita ce: shin, ta yaya za su iya gamsar da hukuma, da ma’aikatar da suke aiki, da ‘yan uwansu, da matansu ko mazansu, da abokanansu ko kawayensu, cewa abin da ake tuhumarsu da shi, ko abin da ya same su da gaske ba su da wani hannu a ciki; kawai kaddara ce?

Damuwa da wannan tambayar kadai ta ishi wasu matsala da hujjar kashe kansu.  Musamman ganin cewa a kasashen irin wadannan, ba kowa ke da tawakkali ba, sanadiyyar nisa da addini da suka yi da kuma daukaka karfin kudurar dan adam wajen taimako a kan karfin kudurar Allah.  Misali, da yawa daga cikinsu basu ma yarda akwai Allah ba, ma’ana ba musulmai bane ba kuma kiristoci bane.  Idan kuma sun yarda akwai Allah ma, to, tasirin dabi’ar mahalli – jari hujja (capitalism) da akidar cin duniya da tsinke (secularism) – kadai ta kwashe musu zurfin yakini da dogaro ga Allah ko abin da suke ikirarin bauta masa, idan ba musulmi bane misali.

- Adv -

Illoli a Zamantakewa

Bangare na karshe da ya kunshi nau’ukan illolin dake addabar wadanda aka sace musu zatinsu musamman a kasashen Amurka da Turai shi ne bangaren zamantakewa.  A wannan janibi akwai illoli da dama.  Illa ta farko dai ita ce: rugujewar mutumci a idon jama’a, musamman abokai.   Wannan illa kan samu ne musamman idan abin da ya faru ya shafi muzanta wanda aka sace wa zati.  Misali, idan dan dandatsa ya sace zatinka a kafafen sada zumunta, yana iya loda hotuna da bidiyo na batsa, ko masu nuna alakantuwar mai shafin da wasu bata gari ko ‘yan iskan duniya.  Duk wanda bai san hakikanin mai shafin ba a zahirin rayuwa, bai kuma ga wani sako dake nuna cewa sace shafin aka yi ba, zai dauka mai shafin ne ke loda su da kanshi, don more wa rayuwa ta hanyar shashanshi.  Wannan zai zubar masa da mutuncinsa, kuma duk inda ko sadda yaga sunansa, ko da a zahirin rayuwa ne, ba abin da zai rika tuna shi dashi face wadannan abubuwa na assha da ya gani a shafinsa.  Wadanda ke sace shafukan mutane a dandalin facebook da sauran kafafen sada zumunta, sanadiyyar kyama ko kyashi ko hassada ko kishi, kan yi amfani da wannan hanya don muzanta wanda suke son muzantawa a idon duniya.

Illa ta biyu a wannan bangare ita ce: rashin yarda daga jama’a.  Hakan kan faru ne idan sace zatinsa da aka yi ya jefa shakku a zukatan jama’a game dashi.  Wannan zai sa a samu rashin amintuwa musamman wajen ba shi bayanai, ko mu’amala dashi, saboda tsoron kada abin da ya shafeshi ya shafi jama’a.

Illa ta karshe da za mu dakata a kanta ita ce: sace wa mutum zatinsa a kafar sadarwa na zamani na iya ja masa bakin jini a idon jama’a.  Dalilin da za su janyo hakan suna da yawa, ya danganci nau’in abin da aka yi da bayanansa bayan sace su.

Wadannan, a takaice, su ne nau’ukan illolin dake tattare da satar zati a zamanin yau; bamu san me gobe za ta haifar ba.  Idan Allah ya kaimu mako mai zuwa za mu kawo bayani kan dokokin da kasashe suka samar don fada da wannan hanya ta ta’addanci mai suna Satar Zati, ko “Identity Theft”.  A kasidar karshe kuma in Allah Ya so, mu kawo hanyoyin kariya ko gyara.  A ci gaba da kasancewa tare damu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.