Mazan Jiya Da Yau…(1)

Daga wannan mako za mu fara kawo tarihin wasu zakakuran Malamai da suka yi fice a duniyar kimiyya da fasahar sadarwa, amma musulmai daga cikin magabata. Kasidar wannan mako mukaddima ne ga sauran dake tafe.

294

Fannoni

Ilmi wani abu ne mai fadi, ta duk yadda ka so kayyade shi da wani bangare nasa, sai ka ga hakan ba ya yiwuwa ta dadi.  Abin nufi a nan shi ne, duk da cewa ilmi nau’i-nau’i ne, amma galibi za ka ga akwai alaka tsakanin nau’ukan, musamman kan ilmin da ya shafi sana’a da kere-kere. Idan muka koma kan ilmin addini ma haka za mu gani; akwai bagaren tauhidi, da bangaren fikihu, da bangaren hadisi da dai sauransu. Amma a karshe idan ka dunkule su duka, sai ka ga suna komawa ne ga ilmin tauhidi ko ibada ga Allah, domin shi ne abin da yake asali kan alaka tsakanin wanda ya sanar da ilimin, wato Allah, da kuma wadanda ake son su yi bautar, wato dan adam da aljan kenan.  To haka sauran nau’ukan ilmi su ma suke.

Binciken da masana suka yi ko suke kan yi a yanzu, daga karnonin baya zuwa cikin karnin da muke ciki, sun taimaka wajen kacalcala ilmi zuwa bangare bangare, iya gwargwadon wayewa da zamanin da ake ciki. Wannan tasa idan muka dubi tasirin binciken da masana magabata suka yi a baya, zuwa na yau, za mu ga sun karkasu ne zuwa fannoni kamar; fannin likitanci ko kiwon lafiya, da fannin sararin samaniya, da fannin lissafi, da fannin sarrafa bayanai, da fannin zane-zane (na gidaje, ko na’urori, ko garuruwa), da fannin safara – kamar mota, da keke, da babur, da injina, da jiragen sama, da jiragen kasa – da fannin sadarwa – kamar na tarho, da fas, da talabijin, da rediyo,da tauraron dan adam, da yanayin sadarwa.  Wadannan a takaice, su ne shahararu cikin fannonin ilmin da za mu kawo masanan da suka yi bincike mai zurfi a cikinsu, ko suka yi sanadiyyar gano su, ko kuma suka habaka su.

Asali da Akidu

Sau tari, abin da ya fi komai tasiri wajen ilmi da karantar da shi, shi ne akida ko asalin wanda ya yi bincike ko ya karantar da ilmin.  Wannan a fili yake. Duk malamin da ya karantar da kai wani nau’in ilmi, to, akwai tabbacin akidarsa na iya tasiri wajen nau’in abin da ya karantar da kai.  Na kawo wannan bayani ne don in nuna mana cewa, dukkan fannonin ilmi da muke karantawa ko karantarwa a yanzu, akwai tasirin akidun masanan da suka yi bincike a cikinsu tun asalin za munnan baya.Hakan ya faru ne saboda bambancin akidun addini da rayuwar masanan da bayanin tairihin rayuwarsu zai zo nan gaba, kamar yadda taken kasidar take nunawa.

- Adv -

Kamar yadda wasunmu suka sani ne, akwai musulmai daga cikinsu, wadanda su ne asali wajen assasa turban galibin nau’ukan ilmin kimiyya da fasahar kere-kere, da bangaren ilmin likitanci, da fannin ilmin sararin samaniya, a zamanin farko.  Wadanda suka biyo bayansu galibi ba musulmai bane, musamman wadanda suka yi binciken ilmi kan harkar kimiyya da kere-kere bayan rushewar daular musulunci da ke Andalus a lokutan baya.  Wasunsu kiristoci ne, wasu yahudawa, wasu kuma maguzawa ne, irinsu Charles Darwin, wanda ake tinkaho da bincikensa kan fannin Ilmin Halittu, da asalin halittu (wato Evolution) da dai sauransu – duk da cewa ya gina wannan nau’in ilmi ne a bisa akidarsa ta maguzanci da rashin yarda da mahalicci.  Don yana nuna cewa dukkan halittu suna samuwa ne daga dabi’a da tsawon zamani, babu wanda ke samar da su, kuma da zarar sun gama zamaninsu suka mutu, wasu za su maye musu, shikenan haka rayuwa za ta ci gaba da gudanuwa.

Wannan akida ce ta wasu nau’ukan maguzawa da Malam Musulunci ke kira “Dahariyyah”, kamar yadda wasu ayoyin Kur’ani suka yi ishara.  Wanda kuma hatta a kasar Amurka ma akwai masana da yawa da suke sukar wannan sakamakon binciken ilmi. A takaice dai, masana nau’ukan ilmi sun karkasu ne zuwa gida hudu; da musulmai, da kiristoci, da yahudawa, da kuma maguzawa.  Haka na da muhimmanci ne wajen fahimtar nau’ukan ilmin da muke karantawa a halin yanzu da wadanda muka karanta a baya.

Tsarin Asali da Samuwa

Kamar yadda bayanai suka gabata a baya kuma kamar yadda muka sani, asalin kowane ilmi dai daga Allah ne, amma yana sanar da shi, ta hanyar ilhama ga wasu daga cikin bayinsa, wadanda ya hore musu kwazo da fahimta da juriyar bincike; musulmi ne ko wadanda ba musulmi ba.  Daga cikin masana akwai wadanda ake danganta wa asali wajen samuwar nau’ukan ilmi.  Ire-iren wadannan su ne wadanda asalin binciken fannin ilmi ke komawa zuwa gare su. Bayan haka, akwai wadanda su kuma habbaka fannin suka yi, ta hanyar fadada bincike cikin wani bangare ko kan asalin binciken farko.  Sannan akwai wadanda suka kirkiri wasu fannoni ko bangarori cikin wani fanni na ilmi.  Misali, a fannin ilmin sararin samaniya (wato Astronomy) akwai wadanda suka yi bincike kan taurari, wasu kan Wata, wasu kan Rana, wasu kuma kan tsari da rayuwar taurari.  Sannan akwai wadanda suka yi bincike kan na’urorin da ke taimakawa wajen hango taurari, da wata, da rana, da ma dukkan buraguzan da ke shawagi a cikin falaki.

Wannan ke sa a samu bangarori daban-daban cikin wani fannin ilmi guda daya.  Kamar a fannin ilmin lissafi misali, akwai wadanda suka yi bincike kan tsarin lissafi. Akwai wadadna suka yi kan ka’idojin lissafi (wato Scientific or Mathematical Formulas).  Akwai wadanda suka yi bincike kan alakar fannin lissafi da ilmin kere-kere.  Akwai wadanda suka yi kan agajin fannin lissafi ga ilmin kwamfuta.  Akwai wadanda suka yi kan fannin lissafi da bangaren likitanci, da dai sauransu.  Wannan na daga cikin dalilan da suka haddasa yaduwar ilmi sosai, har ya game duniya, musamman dai kasashen da ke da hakkin habbaka shi a wannan zamani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.