Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (14)

Kashi na 14 cikin jerin kasidun da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Asha karatu lafiya.

140

Dokoki Don Yakar Satar Zati a Kafafen Sadarwa

Daga bayanan da masu karatu suka karanta a baya tun fara wannan kasida mai tsayi, za su fahimci irin munin da wannan mummunar ta’ada take dauke dashi a fannin rayuwar daidaikun mutane, da tattalin arzikin kasa a jumlace, da mutunci da nagartar rayuwa, da kuma fannin tsaro na lafiya da al’umma da kasa baki daya.    Wanna ya ja hankalin kasashe da dama a duniya wajen samar da dokokin da za su yaki wannan nau’in ta’addanci.

Daga cikin kasashen da suka samar da dokoki akwai kasar Amurka, wacce tafi kowace kasa yawan dokoki kan kowane irin nau’in barna da ka iya faruwa ta wannan kafa.  Wannan ba abin mamaki bane ta la’akari da cewa ire-iren wadannan nau’ukan ta’addanci sun fi faruwa a can ne, sanadiyyar ci gaba da kuma habbakar fannin a nahiyar ma baki daya.   A cikin kasidarmu mai take: “Shahararrun Samame Kan ‘Yan Dandatsa”, wacce muka buga a shekarar 2010, mun kawo sunaye da bayanan ire-iren mutane da hukumar kasar Amurka musamman ta kama, tare da gurfanar dasu a gaban kuliya, inda a karshe aka yanke wa da yawa cikinsu hukuncin zaman gidan maza ko tara mai dimbin yawa.

Bayan dokoki da ta samar har wa yau, gwamnatin Amurka ta samar da hanyoyin wayar da kan jama’a kan matsalar Satar Zati, da irin abin da yake haddasawa na tashin hankali, da kuma kafofin da ‘yan kasa zasu je idan haka ta kasance dasu.  Hukumar tsaro na kasar Amurka ta gina shafin yanar sadarwa wanda a can take wayar da kan jama’a.  A cikin wannan shafi ta tanadi abubuwa da dama da zasu taimaka wa mutane idan an sace musu zatinsu, musamman wadanda aka aikata ta’addanci da bayanansu.  Akwai bayanai kan hanyoyin da za su bi wajen wanke kansu, da neman shawarwari da dai sauransu.  Mai karatu na iya isa wannan shafi na kasar Amurka ta wannan adireshi:  http://www.identityTheft.gov.  Wannan ya kamata ya zama abin koyi ga gwamnatin kasarmu Najeriya.  Domin kamar yadda bayani ya gabata ne a makonnin baya, bayan kasar Amurka da Ingila, kididdiga ya tabbatar da cewa babu ‘yan kasar dake aikata wannan laifi irin ‘yan Najeriya.  Daman mun sani, tuni sunan Kura ya baci tun tana karama.

Bayan kasar Amurka, akwai kasar Ingila, da kasar Ostiraliya, da kasar Kanada, da kasar Faransa, da kasar Hong Kong, da kasar Indiya, da kasar Filifins, da kasar Suwidin, da wasu kasashen ma.  Daga cikin kasashe Afirka kuma akwai kasar Kenya wacce ta samar da nata dokar cikin wannan shekara (2018), sai kuma kasarmu Najeriya.  A namu bangaren, Najeriya ta samar doka a shekarar 2015, wanda zai yi yaki da nau’ukan ta’addancin da ake aikata su ta hanyar kwamfuta musamman; ya Allah mai dauke da Intanet ne ko mara Intanet.

Wannan doka mai suna: “Nigeria Cyber Crime Act, 2015”, wacce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rattafa wa hannu, tana dauke da dokoki ne masu yawa, kuma ta fi karkata ne ga irin laifukan da ake aikatawa wajen satar bayanai ta hanyar aikin Dandantsa (Hacking).  Kuma dokar ta yanke hukuncin dauri a gidan yaki daga shekara 5 zuwa shakaru 20, iya gwargwadon girman laifi.  Sai kuma tara da yanke a matakin laifi daban-daban, shi ma daga abin da ya kama daga naira miliyan daya har zuwa miliyan 20 duk yana ciki.

- Adv -

Amma dokar bata yi Magana kan tsarin ayyukan laifi da suka shafi “Satar Zati” ba.  Duk da cewa alkali na iya daure mutumin da yayi hakan sanadiyyar sato bayanan jama’a ta hanyar sace kwamfuta ko barkowa cikinta ta hanyar amfani da wata manhaja, ko lalata bayanan dake dauke cikin kwamfutar.  Amma ta hanyar laifi mai sunan “Satar Zati” kam, dokar bata tabo bangaren ba.  har wa yau wannan doka bata tabo abin da ya shafi kazafi da kushiya mara dalili da kuma cin zarafi ko batanci da wani zai iya yi wa wani ta hanyar kafafen sadarwa na zamani ba.  Idan mutum ya aikata wani abu mai alaka da hakan, sai dai hukuma ta masa hukunci da dokokin kazafi a zahirin rayuwa.  Hakan kuma na da bukatar bincike na musamman don tabbatar da laifin da aka yi ta hanyar kafar sadarwa – Gidan yanar sadarwa ne ko shafin sada zumunta – da shedu da komai.  Wanda wannan ba karamin aiki bane.

Wannan yasa daya daga cikin ‘yan Majalisar Dattawa mai suna Sanata Bala Ibn Na-Allah yayi yunkurin samar da wata doka da za ta magance hakan, ta hanyar kudurin da ya samar a majalisar dattawa ta tarayya, amma wannan kuduri bai samu hayewa ba.  A karshe ma dai kashe kudurin aka yi saboda rashin amincewar sauran mambobi, da kuma korafe korafen da ‘yan kasa suka ta yi, musamman ‘yan jaridu masu zaman kansu.

Don haka, a halin yanzu dai doka daya ce muke da ita a Najeriya, wacce ke yaki da satar bayanai ko salwantar dasu ta hanyar kwamfuta da Intanet.  Ita kanta wannan doka a halin yanzu wasu daga cikin masana masu sharhi kan harkokin yau da kullum suna korafin cewa dokokin dake cikinta sun yi tsauri, sannan kuma bata tattaro galibin laifukan da aka fi aikatawa a kafafen sadarwa na zamani ba a Najeriya.  Da yawa cikinsu suna kira ga hukuma cewa a sake bitar wannan doka don fadada ta, da rage kaifinta.

Sai dai ni a ra’ayina, ko anyi bitar wannan doka a rage mata kaifi, an kuma fadada laifukan dake cikinta, muddin ba sake salon tsarin aiki da doka aka yi a Najeriya ba, ba abin da wannan bitar ko ma samar da dokar zai fa’idantar.  Dalilina a nan kuwa shi ne, muna da dokoki da dama a Najeriya kan abubuwa daban-daban, amma babbar matsalar kasarmu ita ce, ba a sa ido wajen tabbatar da jama’a sun bi doka sau da kafa.  Wannan abu na farko kenan.

Dalili na biyu kuma shi ne, wannan doka da aka samar na yaki da ta’annati ta hanyar kwamfuta da sauran kafafen sadarwa na zamani, tana bukatar bincike mai zurfi, ta hanyar kwarewa a fannin, wanda suke bukatar zurfin ilimi a fannin sadarwa da dokokin kasa, kafin tabbatar da mai laifi.  Domin idan yanzu misali mutum yayi amfani da kwarewarsa ta fannin sadarwa, ya kutsa cikin wata kwamfuta da ke Najeriya, ya aikata ta’addanci.  Tabbatar da cewa shi ne ya aikata hakan, ba karamin aiki bane.

Domin dan Dandatsa na iya amfani da wata kwamfuta da ke wata kasa daban, ya umarceta ta isar masa da sako zuwa kwamfutar da yake son kutsawa cikinta, ko ya aiwatar da sadarwa tsakaninsa da ita, ta hanyar wancan kwamfutar dake wata kasa.  Ka ga nan, idan ka duba, zahirin dubawa, baza ka ga sawunsa ba a matsayinsa na dan Najeriya, ba kuma za ka ga adireshin kwamfutarsa ba (IP Address) wajen aikin, sai dai na wancan kwamfutar da ya mallake.  Bayan haka, yana iya amfani da manhajar dake layance adireshin kwamfuta, wato: “Connection Encryption System” wajen ziyartar kowace irin kwamfuta ce a duniya, baza ka taba ganin alamar shi yayi hakan ba.

A nan ba wai cewa nake ba a iya gane wadannan nau’ukan laifuka bane har abada, a a.  An aiya ganewa, amma sai anyi amfani da kwarewa na hakika a fannin sadarwa, da kuma kayan aiki masu tsada da zasu taimaka wajen gano “hakikanin” mai laifi, ba wai kwamfutar da ta aikata laifin ba.  Samuwar hakan kuma a Najeriya, a dai halin yanzu, ba abu bane da yake cikin damuwar hukuma.  Wannan zai faru ne saboda nau’ukan matsalolin da kasarmu ke fuskanta a bangaren tattalin arzikin kasa da kuma tsaro.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.