Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (12)

Wannan shi ne kashi na 12 daga cikin jerin bayanan da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Asha karatu lafiya.

165

Munanan Tasirin “Satar Zati”

Kafin wannan marhala ko sashe, masu karatu sun ji bayani dalla-dalla sanka-sanka kan ma’ana, da asali da kuma hanyoyin da ‘yan dandatsa ke bi wajen aiwatar da wannan mummunar ta’ada mai cike da ta’addanci na Satar Zati.  Zai dace kuma mu san wasu hanyoyi za mu bi, a matsayinmu na daidaikun mutane ko kamfanoni ko hukumomin gwamnati, wajen ganin mun kare kawunanmu daga afkawa wannan musiba, ko kuma idan cikin kaddarar Ubangiji mun samu kanmu ciki tsundum, yaya za muyi mu fita daga ciki.  Sai dai kafin nan, a yau za mu dubi munanan tasirin wannan dabi’a ne ga duk wanda hakan ta afka dashi.  Ma’ana, idan aka aiwatar da Satar Zati ga rayuwar mutum ko wata hukuma, wani irin tasiri ne hakan ke haddasawa?

A cikin wani sharhi mai tsayi da tayi, Malama Alison Grace Johansen, kwararra kan ilimin dabi’u da halayya dake kasar Amurka, ta zayyana matsaloli da dama da mutum zai iya samun kansa a ciki idan aka sace masa zatinsa.  Ta kuma karkasa su zuwa bangare-bangare ne, don fayyace su dalla-dalla.  A wannan mako in Allah Ya yarda za mu yi sharhi ne kan wadannan matsaloli ko illoli da mutum zai tsinci kanshi ciki.  Ga su nan daya-bayan-daya.

Illolin Tattalin Arziki

A daya daga cikin makonnin da suka gabata sadda muke bayani kan nau’ukan hanyoyin satar zati, mun kawo nau’in satar zati na tattalin arziki.  Ma’ana, yan ta’addan dake aiwatar da wannan nau’i na satar zati suna yi ne don cinma manufar tattalin arziki, wato: samun kudade kenan da arziki.  Da zarar an sace maka zatinka, abu na farko da zai faru ga mutum shi ne rasa sirri kan harkokinsa na kudi.  Idan katin ATM dinka ne aka sace, har kuma aka ci nasarar isa ga taskar, to, ka rasa sirri ta wannan bangare.  Musamman idan baka san hakan ya faru ba.  Wannan dan ta’adda zai samu isa ga taskar ajiyarka ta banki, yaga nawa ne a ciki, nawa ka zuba kuma a wane rana ko lokaci,  su wa da w aka taba aika musu kudade, wa da way a taba aiko maka kudi, yaushe ka bude taskar, duk wadannan bayanan sun shiga hannunsa.  Wannan illa ta farko kenan.

- Adv -

Illa ta biyu a bangaren tattalin arziki ita ce, hasarar kudi da kaddarorin hannayen jari.  Abin da wannan ke nufi shi ne, da zarar an sace maka zatinka ta bangaren abin da ya shafi kudade, barawon, bayan yaga nawa ka ajiye a taskar, zai kuma iya kwashe nan take ya canza musu wurin zama – ta hanyar debe su a ATM ko sayan wasu hajoji dasu.  Sannan idan kuma bayanan katinka sun shafi kadarorin hannun jari irin na kasuwannin hannayen jari misali, nan take yana iya sayar dasu kai tsaye, ya zuba kudin a taskarka, sannan ya debe su nan take – ta hanyar ATM ko ta hanyar sayan hajoji a Intanet.

Illa ta uku a bangaren tattalin arziki ita ce, yanzu aiki ya sameka, wajen kokarin kubutar da kanka daga hukuma.  Domin, kamar yadda na zayyana a baya, cewa idan aka sace zatinka kuma aka je aka aiwatar da wani nau’in ta’addanci da bayananka, hukuma na daukar cewa kai ne ka aikata, bata san wani dan ta’adda ba, muddin baka sanar da ita ba daidai lokacin da abin ya faru.  Da zarar wani abu ya faru na ta’addanci kuma shedu suka nuna bayananka, to, hukuma bata san kowa ba sai kai.  Don haka kai za a nema.   Wannan zai sa dole kaje kabi hanyoyin da za ka tabbatar wa hukuma cewa ba kai bane da kanka, ko da yardarka aka aiwatar da wannan ta’addanci ba.  Wajen yin hakan kuma dole ne ka nemo lauya wanda zai tsara maka abin da za ka yi, na shawarwari da kuma wakiltarka a kotu da sauran wurare, don nemo bayanan da za ka gamsar da hukuma da jami’an tsaro cewa ba kai bane.  Wannan kuma na bukatar kudade masu dimbin yawa.  A wasu lokuta ma sai an nemi tallafin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda ke rajin kare ‘yancin dan adam.

Illoli Kan Dabi’a da Halin Rayuwa

Bayan hasarar dukiya sanadiyyar satar zati, wannan ta’ada har wa yau daga cikin illolinta akwai haddasa bakin ciki dawwamamme na abin da ya faru na hasarar dukiya, da kuma damuwa kan me zai kasance ga wanda abin ya shafa.  Wannan ita ce illa mafi muni daga cikin illolin dake samun wanda aka sace wa zati, musamman a kasashen Turai da Amurka.  Hakan kan haddasa rashin cin abinci, da rashin bacci, da rashin sukuni ko natsuwa irin ta zuci, da kadaici sanadiyyar bakin ciki da damuwa.

Bincike ya tabbatar cewa ta hanyar jin ra’ayin jama’a ya tabbatar da cewa, kasha 74 cikin 100 na mutanen da ake sace zatinsa na shiga halin mummunar damuwa.  Kashi 69 cikin 100 na samun kansu cikin damuwa mai dauke da tsoron talauci, saboda irin hasarar da suka tafka bayan sace zatinsu.  A daya bangaren kuma, kashi 60 cikin 100 na fama da tashin hankali.  A yayin da kashi 42 cikin 100 kuma ke fama da tsoron samun damar tallafa wa dangi, sanadiyyar hasarar da  su ma suka tafka.  A yanayi mafi muni kuma, binciken ya gano cewa a duk shekara ana samun kashi 8 cikin 100 dake kashe kansu idan suka samu kansu cikin wannan yanayi mafi muni na satar zati.  Duk da mai matsalolin na rataya ne ga tsantsar bakin ciki da damuwa na sanin madafa da sake fara rayuwa daga farko, idan aka shiga wannan yanayi.  Wannan ita ce illa ta farko a bangaren dabi’a da halin rayuwa.

Illa ta biyu  a wannan bangare ita ce bata suna, wanda ke haddasa mutum ya rasa aikinsa ma idan abu yayi tsanani.  Domin duk hukuma ko kamfanin da kake rike da wasu bayananta na sirri kan aikin da aka kallafa maka a matsayinka na ma’aikaci, sai aka sace zatinka, wanda sanadiyyar hakan bayanan suka bare, ba kai kadai abin zai shafa ba; har da hukumar ko kamfanin.  Kuma ida bincike ya nuna cewa da sakaci cikin lamarin, hakan na iya sa mutum ya rasa aikinsa, iya gwargwadon yadda yanayi ya kama.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.