Bunkasa Harshe da Al’ummar Hausawa: Daga Adabi Zuwa Kimiyya da Fasahar Sadarwa ta Zamani (4)

Ga kashi na hudu kuma na karshe, cikin jerin kasidun dake nazari kan rubuce-rubuce cikin harshen Hausa, da bukatar sauya salo zuwa wasu fannonin da ba na kirkirarrun labaru ba, don kara samar da wayewa ga al’umma.

751

Hanyoyin Bunkasa Ilimin Kimiyya da Fasaha

Bayan takaitattun bayanai kan irin matsalolin da ke addabar ci gaban rubuce-rubucen ilimi musamman na kimiyya da fasahar sadarwa cikin harshen Hausa, a yau za mu kawo kadan cikin hanyoyin da idan muka dabbaka su, za mu samu ci gaba in Allah Ya yarda.  Akwai hanyoyin warware wannan matsala da dama, amma za mu takaitu kan muhimmai daga cikin su ne kawai.  Hanya ta farko ita ce ta hanyar yawaita rubuce-rubuce kan wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere.  Idan nace yawaita rubuce-rubuce, mai karatu ya daina tunanin rubuce-rubuce daga “kwararrun marubuta” kadai, kamar yadda abin yake a yanzu.  A a, ina nufin duk wani mutum da Allah ya sawwake masa kwarewa a fannin kere-kere ko kimiyya da fasahar sadarwa; ko da kuwa ba ya ji ko iya rubutu da harshen Turanci ko Hausan boko.

Idan mai gyaran mota ne kai, ka yi kokari ka rubuta wa al’umma irin hanyoyin da kake bi wajen wannan aiki, da irin nau’ukan matsalolin da motoci ke fuskanta, musamman ma wadanda ka ke iya gyarawa.  Idan likita ne kai, kai wa Allah ka taimaki al’umma wajen rubuta wani abu cikin harshen Hausa; nau’ukan cututtuka ne ko yadda ake tiyata, duk wanda Allah Ya hore maka, ka rubuta.  Idan kwararre ne kai a fannin hada magungunan zamani (pharmacist), ka rubuta mana bayanai kan matakan da kamfanonin da ke hada magungunan da muke ta sha, suke bi wajen yin hakan.  Idan sunayen saiwowi ko ganyayyakin ne baka sani ba a Hausance, akwai wadanda za su taimaka maka da bayanai.

Na tuna, shekaru kusan sittin da suka gabata, lokacin da Likita Bergery ya tashi rubuta Kamus din Hausa da Turanci a nan kasar, sai  da yayi kusan shekaru biyar suna kai-komo da wasu bayin Allah masana sunayen ganyayyaki da itatuwa a kasar Hausa.  Aikinsu kawai shi ne su rika gaya masa sunan itacen ko ganyen ko ciyawar, shi kuma yana rubutawa da Hausa.  Haka idan Allah Ya sawwake maka iya gyaran babur, duk ka agaza wa al’umma wajen taskance bayanan yadda kake aikinka.  Idan malamin makaranta ne kai da Allah Ya hore wa sanayya kan fannin lissafi, ka rubuta littafi guda kan yadda ake lissafi cikin harshen Hausa, da yadda ake warware dukkan matsalolin da suka shafi darussan da kake karantarwa.  Idan manomi ne kai, na zamani ko na gargajiya, duk kana iya taimakawa.  Haka idan mai gyaran kwamfuta ne ko wayar salula, ka rubuta littafi dan madaidaici, wanda zai sanar da masu mu’amala da wadannan kayayyakin fasaha hanyoyin da za su iya bi wajen warware ‘yan kananan matsalolin da ke addabarsu.

Kada ka dauka wannan zai rage maka yawan masu kawo maka gyara, a a, sai ma ya kara.  Don ka rubuta littafi kana bayanin ire-iren matsalolin da ke addabar kwamfuta ko wayar salula, da yadda ake hana faruwarsu ko ma magance su, ba shi zai sa a daina kawo maka gyara ba, sam. Kuma kada ka raina dan abin da ka sani.  Mai girma ne a wajen wanda bai sani ba.

Wannan hanya ta yawaita rubuce-rubuce a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na da muhimmanci ta bangarori biyu.  Na farko shi ne, za a samu yawaitan abin karatu a wannan fanni.  Na biyu kuma hakan zai cusa wa marubuta da dama sha’awar rubutu a fannin, maimakon takaituwa da nasu fannin kadai.  Ga wadanda basu fara ba kuma zai samar musu abin yi da kuma dogaro.  Haka kuma, za a samu tabbatacciyar tsarin rubutu cikin wannan fanni.  Wannan hanya na bukatar matukar bincike kan fannin, tare da yin amfani da kwarewar da marubuci ke da ita wajen siffata hanyoyi ko tsarin da ilimin ya kebanta da su.

Sai hanyar gyara ta biyu, wacce ta kumshi fassarawa ko tarjama littafan da aka rubuta cikin  wasu harsunan dabam, kan ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere.  Wannan hanya na da muhimmanci ita ma, kuma ita ce galibin daulolin da suka yi fice a fannonin rayuwa dabam-daban suka dauka wajen bunkasa al’ummar su.  Don haka, yana da muhimmanci a samu masana su fassara littafai da kuma rahotannin da ke dauke da sakamakon bincike kan nau’ukan ilimi masu yawa.  Wannan zai taimaka wajen kara samar da abin karatu cikin fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere.  Haka kuma zai kara habbakawa tare da motsa sha’awar marubuta a wasu fannonin.  Bayan haka, babban abin da hakan zai kara dasawa shi ne, kyakkyawar fahimtar yadda tsarin wadannan nau’ukan ilimi ke gudanuwa a kai.  Kamar yadda muka sani ne, duk yadda ka kai da fahimtar wani nau’in ilimi da aka karantar da kai cikin wani harshe, ba zai kai yawan fahimtar da za ka samu ba idan da harshenka aka karantar da kai.

Don haka samuwar littafai da aka fassara daga wani harshen zuwa Hausa, zai kara gyatta fahimtar masu karatu a wannan harshe, su fahimci abin daidai.  Domin a bayyane yake cewa galibin masu karatu cikin wadannan fannoni a halin yanzu cikin harshen Turanci, ba duk za su iya kwatanta maka ko karantar da kai ilimin da suka koya cikin harshen Hausa ba, har ka fahimce shi yadda ya kamata.  Duk kuwa da cewa su sun fahimci ilimin cikin harshen da aka karantar da su.  Idan aka bunkasa harkar tarjama da fassara, babu shakka tsarin ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da na kere-kere zai samu bunkasa shi ma.

Hanya ta gaba ita ce, a shigar da wadannan nau’ukan ilimi cikin abin da ake karantar da masu koyon harshen Hausa daga Firamare zuwa Jami’a.  Tirkashi!  Ba zan mance ba, lokacin da nake sakandare, an karantar da mu ilimin magungunan gargajiya, cikin harshen Hausa.  Wannan ya taimaka mani matuka wajen fahimtar abubuwa da dama.  Har nake tunanin cewa, da a ce za a dore da wannan tsari, ko da tun muna Firamare aka fara karantar da mu, da na dauki fannin ilimin sarrafa magunguna, wato Pharmacy a Jami’a.  Domin na samu kyakkyawar fahimta kan hakan.  Yin haka tun daga Firamare na da tasiri wajen cusa wa yara fahimtar tsarin da kayayyakin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere ke gudanuwa a kai.  Kuma na tabbata tun nan za a samu masu sha’awar wadannan fannoni; ko dai wajen karantarwa ko kuma karatu.

- Adv -

Shekarun baya da suka gabata, hatta harshen Hausa galibi da Turanci ake karantar dashi a jami’o’in kasar nan.  Wanda ya fara yin kuru wajen sauya wannan tsari shi ne Farfesa Muhammad Hambali Jinju.  Ga abin da yake cewa, lokacin da Jaridar AMINIYA ta yi masa tambaya kan hidimar da yayi wa harshen Hausa:

“…kokarin da nayi, shi ne kokarin da duk jama’a suka sani kuma suka shaida, kuma sun sani kuma suna fadi, musamman ma malaman Hausa, wadanda na karantar da su a Jami’o’i.  Na san dai nayi iyakan kokari na kan Hausa, yadda ta haka har ta samu ci gaba.  Idan zan ba ka misali, lokacin da naje Kwalejin Abdullahi Bayero, Kano, na iske duk kwasa-kwasan Hausa, da Turanci ake koya su.  Ni na yi kokarin aka maida koyarwa da Hausa.  A tsarin jami’a a lokacin, da Turanci ake koyarwa, amma ni da na je na rika koyarwa da Hausa.  Duk da na san laifi ne kuma kasada ce, sai kawai na canza zuwa tsari na.  Ni kai na ban san abin da ya ingiza ni na dauki wannan mataki ba.  Ko kishin Hausar ne, ko kuwa kuruciya ce, ni dai ban iya bambancewa ba.”

Hanya ta gaba mai kamar wuya, ita ce, a samu wata cibiyar bincike ko makaranta ta musamman, wacce za ta dauki nauyin karantar da ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere musamman, cikin harshen Hausa.  Ba kowa zai yarda da wannan shawara ba, amma kuma in har za a dabbaka ta, za a samu ci gaba.  A kasashen Larabawa (irin su Saudiyya da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa) suna da makarantu irin wannan.  (Duk da yake na san tsarinmu da nasu ya sha bamban, wajen shugabanci da kuma tsarin dokar kasa).  Akwai malamai kwararru kan ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, kuma masana kan harshen larabci.  Idan ka shiga makarantar, akwai kwasa-kwasan Turanci kam, amma galibin abin da za ka koya duk da harshen Larabci za a koyar da kai.  Wannan tasa a yanzu ake samun masana harkar likitanci da fasahar sadarwa kwararru.

Wannan har wa yau yayi tasiri wajen bunkasa tsarin rubuce-rubuce cikin wadannan fannoni da harshen Larabci.  Sai ka ga littafi kan ilimin kwamfuta da tsarin hada alaka a tsakanin kwamfutoci, wato Networking, an rubuta shi tsaf, da harshen larabci.  Ga hotuna da taswirori da komai da komai.  Ko ka ga littafi kan yadda ake warware matsalolin lissafi, duk cikin harshen Larabci.  Me zai hana mu samu wata hukuma ko gwamnatin jiha a Arewa, ko kuma wani mai kishin al’ummar Hausawa, ya bude mana irin wannan makaranta mai suna makamanciyar wannan: Hausa Institute of Science and Technology (Cibiyar Binciken Kimiyya da Fasahar Kere-kere Cikin Harshen Hausa)?  Wannan ba ya nufin mu daina amfani da harshen Turanci, maimakon haka ma, zai kara wa ‘ya’yanmu kwazo ne a makarantun da suke zuwa.  Wadanda basu kware a Turanci ba, zasu yi kokarin kwarewa, don sun san cewa duk abin da zasu rubuta ko karanta don karantarwa ko rubuta wani littafi a wannan fanni nan gaba ko a yayin da suke karatun, daga littafan turanci za su tsamo su.

Har wa yau, zai dace a samu mujallu da jaridu na musamman kan wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa, masu fitowa a duk mako ko wata.  Hakan zai kara cusa wa al’umma sha’awar abin, don za a samu marubuta masu yin bayani filla-filla kan fa’idojin da ke tattare da bunkasa wannan fanni, tare da yin sharhi kan muhimman ci gaban da ake samu a fannonin a duniya.  Tabbas muna sane da matsalar da ke addabar Arewa kan batun assasawa da kuma rike kamfanin jarida ko mujallu musamman a shekarun baya, amma yanzu an farfado, kuma ga dukkan alamu za a dore a haka in Allah Ya yarda.  Don haka samun ire-iren wadannan kafafen ilimantarwa zai taimaka matuka wajen bunkasa wannan fanni.

Abu na karshe da za mu kawo shi ne, a samu wani tsari na gamayyar masana harshen Hausa, da zai rika lura da kuma tantance kalmomi na musamman kan wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, ta amfani da harshen Hausa.  Domin rashin wannan tsari na cikin  abin da ya kara rage wa wannan fannin armashi.  Wasu na son su yi rubutu amma samun kalmomin da suka dace da abin da suke son rubutawa ko fassara shi ne babban matsalansu.  Misali, akwai karancin kalmomin Hausa na musamman cikin fannin ilimin kwamfuta, domin rubuce-rubuce basu yadu sosai a kan haka ba. Har wa yau, littafai irin su Garkuwar Hausa da Tafarkin Ci Gaba, wanda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya rubuta, da ma sauran makamantansu, na bukatar bita a kai a kai.  Saboda a kullum abubuwa na caccanzawa ne.  Duk wanda ya dauki littafin Farfesa ya san tabbas yayi kokari, nesa ba kusa ba, wanda kuma da a ce a yanzu ne ya rubuta littafin, da kalmomin da zai yi amfani dasu, da kuma fannonin da zai taskance sun fi wadanda ya zuba cikin littafin yawa.  Don yanzu an samu bunkasar dukkan fannonin da yayi nazari kansu.  Don haka a samu malaman jami’a, kwararru kan harshen Hausa, su rika kirkirar kalmomi na musamman ga dukkan fannonin da ke bunkasa a yanzu na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere.

Kammalawa

Kafin in karkare, yana da kyau in sanar da masu karatu cewa, daidai lokacin da nake wannan rubutu (bayan na fitar da kashi na daya da na biyu, an buga), sai na samu sakon wasu cikin masu karatu da ke jawo hankalina zuwa ga wani littafi da Malam Isa Musa ya rubuta, mai suna: Mu Koyi Gyaran Rediyo (1 – 2).  Wannan bawan Allah, a cewar masu wannan fadakarwa, ma’aikacin NEPA ne da ke zaune a Kano, dan garin Gumel da ke Jihar Jigawa.  Sun nusar da ni ne kan batun da na rubuta cewa duk da dadewar da rediyo yayi a kasar Hausa, har yanzu babu wani littafi da aka rubuta kan yadda yake aiki balle yadda ake gyaransa idan ya lalace.  Na fadi haka ne ta la’akari da rashin yaduwar ire-iren wadannan littafai.  Ban taba cin karo dashi ba, kuma ban taba samun labari kan littafin ba.  Wannan ba karamin kokari bane, zan kuma so in samu littafin don yin nazari kansa.

Haka kuma na sake samun labarin wani bawan Allah da yayi rubutu kan fannin Fiziya (Physics) da Hausa, duk da yake ba a riga an buga littafin ko ba.  Wannan abin farin ciki ne shi ma, kuma idan muka ci gaba da samun ire-iren su, babu shakka abubuwa za su ci gaba da gyaruwa.  Zan kuma ci gaba da sanarwa duk lokacin da na samu labarin wani kokari makamancin wannan, abin yabawa.  Wannan ita ce kasida ta karshe kan wannan fanni in Allah Ya yarda.  Idan Allah Ya kaimu wani mako za mu shiga wani fanni kuma dabam.  Muna mika sakon gaisuwar mu ga dukkan masu karatu, musamman masu bugo waya ko kira don tambaya ko neman karin bayani.

Allah bar zumunci, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Abubakar says

    Yaduwar harshe ta fuskar addini

Leave A Reply

Your email address will not be published.