Sakonnin Masu Karatu (2018) (2)

Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

177

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan aiki yana tafiya cikin koshin lafiya. Yaya zanyi amfani da manhajojin wayar salula?  Kuma wane shafi zanje domin saukar dasu?  Ka huta lafiya. Naku Abdullahi B. Anka zamfara: 08060809091

Wa alaikumus salam, barka dai takwarana.  Su manhajojin wayar salula dai kayan aiki ne.  Duk wanda ka ga ya neme su, to yana da abin yi ne dasu.  Muddin kaga mutum ya saukar da wata manhajar wayar salula a kan wayarsa, alamar yana da abinyi ne dasu.  Don haka, kana iya amfani da manhajar wayar salula ne ta la’akari da bukatarka.  Sannan duk manhajar da ka saukar, amfani da ita ba shi da wahala.  Abin da kake bukata dai shine fahimtar yaren da manhajar ke amfani dashi.  Wasu manhajojin ma ba ka bukatar iya yaren da aka gina su a kai, saboda samuwar alamomi masu maka ishara da yadda zaka sarrafa su.

Da fatan ka gamsu da wannan gajeren bayani.  Allah sa a dace, amin.


Salamun alaikum, barka da dare da fatan kana lafiya. Dan Allah Baban Sadik ina son a dan mini karin bayani akan shafin “Paypal”. Daga Usman Aliyu Kano: 08133533448: usmanaliyu89@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Usman.  Ina godiya matuka da addu’arka gare ni.  Ina rokon Allah yasa muyi tarayya cikin alheri baki daya, amin.  Dangane da tambayarka, shafin “PayPal” dai shafi ne dake baiwa mutane daman aiwatar da cinikayya ta hanyar biyan kudaden hajojin da suka saya a shafukan Intanet cikin sauki, tare da basu dama har wa yau wajen aika wa ‘yan uwansu kudade kai tsaye, watau “Instant Money Transfer” kenan.  Idan kana da rajista da wannan shafi har wa yau, za ka iya karban kudaden cinikin da kayi na hajojin da kake tallatawa idan kana da shafin sayar da kayayyaki a Intanet.  A takaice dai, kamfanin “PayPal” dai dillalai ne kan hada-hadar kudi a duniya ta hanyar Intanet.  Ba wai banki bane mai zaman kansa.

Asalin wannan shafi dai ya faro ne daga babban shafin sayar da hajoji a Intanet mai suna: “Ebay,” daga nan ya fara hada-hadar kudi ta hanyar baiwa jama’a masu sayan hajoji a shafin “Ebay” damar biyan kudin hajoji, da kuma baiwa ‘yan kasuwa damar karbar kudaden da ake biyansu na hajojin da suke sayarwa a shafukansu na Intanet.  Daga nan wannan shafi ya habbaka.  A halin yanzu dai akwai masu rajista sama da miliyan 188 a duniya. 

- Adv -

Kuma shafin na samun kudaden shiga ne ta hanyar cajin hidima da yake wa masu rajista dashi.  A karon farko dai kamfanin yakan tara kudaden da yake karba a madadin masu rasjita dashi ne a bankuna, yana karbar kudin ruwa kai tsaye daga bankunan, tunda suna aiwatar da kasuwanci da kudaden, kamar yadda yake a tsarin hada-hadar kudade na zamani a kasashen Amurka da Turai.  Daga baya da masu rajista da wannan shafi suka gano haka, sai suka ta rufe “account” dinsu suna ficewa.  Domin wannan, a tunaninsu, ci da ceto ne.

Wannan bore da jama’a suka yi ne yasa kamfanin ya canza tsarinsa.  Inda ya rika dora wa masu rajista haraji kan dukkan hidimar da ya musu.  Harajin masu sayar da hajoji daban da na masu karba ko aika kudade ga ‘yan uwa ko abokansu.  A halin yanzu da wannan tsari dai kamfanin ke rayuwa.  Idan ka kebe kasashen Indiya, da Ghana, da Japan, da Afghanistan, da Crimea, da sauran kasashen da kasar Amurka ta sanya wa takunkumi, duk sauran kasashen duniya na mu’amala da wannan shafi.  A halin yanzu an kiyasta cewa, shafin PayPal na iya karba tare da aika takardun kudade sama da 25 daga cikin nau’ukan kudaden duniya.

Yin rajista a shafin PayPal ba wahala.  Bayanan da za ka bayar sun hada da sunanka cikakke, da adireshin Imel, da adireshin inda kake zaune, da kasar da kake zaune, da lambar wayarka, sannan da lambobin katin ATM dinka.  Kana iya tambayar ko dole ne sai mutum na da taskar ajiyar banki sannan zai iya karba ko aika kudi?   Amsar ita ce: eh!  Domin za a bukaci lambobin katinka na ATM, wanda ta hanyar lambobin ne za a iya zuba maka kudade a taskarka ta banki da ke kasar da kake.  Ni kaina ina amfani da wannan tsari wajen sayen manhajojin kwamfuta a Intanet.  Hatta wasu manhajojin da nake amfani dasu wajen tafiyar da shafin Taskar Baban Sadik dake: https://babansadik.com, irin su “Elementor Pro” da sauransu, duk da wannan tsari na biya kudadensu.

Wannan shi ne takaitaccen bayani kan shafin PayPal.  Idan kana bukatar gamsassun bayanai, kana iya ziyartar shafin kamfanin dake: www.paypal.com.  Da fatan ka gamsu.


Salaamun alaikum Baban Sadik, yaya aiki da kuma hakuri damu? Don Allah ina so ka turo mini kasidun da kayi akan yadda ake amfani da manhajar Google wajen neman bayanai, ta email dina dake: shamsudeenkabir92@gmail.com.  Allah ya kara basira da daukaka.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Shamsud Deen.  Lallai akwai kasidu biyu da na gabatar kan yadda ake neman bayanai da kalmomin da ake amfani dasu wajen neman bayanai a Intanet.  Sai dai tuni na dora su a kan shafinmu dake Intanet, kuma za ka iya samunsu kai tsaye, don karantawa ko ma saukar dasu kan waya ko kwamfutarka.  Ga adireshin da zaka bi wajen isa ga kasidar da nasan ita ce kake ishara gare ta:  https://babansadik.com/tsarin-neman-bayanai-a-intanet-2

Ina fatan wannan shi ne abin da kake nema.  Allah amfanar dakai ya kuma sa albarka cikin abin da ake koya a wannan shafi namu mai albarka, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.