Sakonnin Masu Karatu (2018) (1)

Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

136

Salaamun alaikum Baban Sadik, Ina da kwamfuta nau’in MacBook Air: 11inch, Mid 2011, Processor – 1.8GHz Intel Core i7, Memory – 4GB 1333 MHz, OS – XLion 10.7.5 (11G63). Babbar manhajar kwamfutar ta daina daukan yawancin manhajojin da nake loda mata. Don Allah yaya za’ayi inyi upgrading zuwa recent OS? Ina zaune nan Kano ne. Na gode.  Bashir Sanusi:  sanusibashir@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Bashir.  Idan na fahimceka, babbar manhajar kwamfutarka ba ta daukan wasu manhajoji ne a halin yanzu.  Sai dai kuma baka yi bayanin wani nau’in babbar manhaja bace a kan kwamfutar.  Duk da cewa kamfanin Apple ne ya kera kwamfutar, amma kwamfutocin na zuwa ne da nau’ukan babbar manhaja guda biyu.   Ko dai ya zama asalin babbar manhajar kwamfuta na kamfanin Apple ne, wato: “MacOS”, ko kuma na kamfanin Microsoft, wato: “Windows” kenan.

Idan na kamfanin Apple ne, kana iya sabunta babbar manhajar, duk da cewa ta la’akari da bayanan da ka bayar, tsohuwar kwamfuta ce da aka kera tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011, amma har yanzu kamfanin Apple na bayar da damar sabunta babbar manhajar da ke tsakanin wadannan shekaru, kyauta. Cikakken bayani na dauke a shafin dake wannan adireshi na gidan yanar kamfanin, a: https://www.apple.com/lae/macos/how-to-upgrade/.  Don haka,  sai ka garzaya shafin ka karanta cikakken sharhi da hanyoyin gudanar da hakan cikin sauki.  Wannan zai taimaka maka wajen sabunta babbar manhajar, tare da inganta hanyoyin mu’amala da kwamfutar gaba daya.

Idan kuma tana dauke ne da babbar manhajar Windows na kamfanin Microsoft, in dai “Windows 7” ko “Windows 8”, kana iya sabunta su da babbar manhajar “Windows 10”.   Za ka iya samun cikakken bayani kan haka a shafin kamfanin Microsoft dake: https://support.microsoft.com/en-us/help/12435/windows-10-upgrade-faq

Wannan shi ne bayani a takaice kan hanyoyin da za ka iya bi wajen gudanar da wannan al’amari.  Amma kafin nan, ka tabbatar ka kwashe bayanan dake kan kwamfutar gaba daya a halin yanzu, ka zuba su a wata ma’adana amintacciya, don kauce wa matsala a yayin sabunta babbar manhajar.  Ina maka fatan alheri, Allah kuma yasa a dace, amin.


Asslaamu alaikum Baban Sadik, na karanta amsosin da ka bayar a jaridar AMINIYA ranar 25 ga watan Agusta, 2017.  Allah ya saka maka da alheri ya kuma kara ilimi da basira, amin.  Sako daga Alhaji Musa Garba, Kafin Madaki, Ganjuwa LGA, Bauchi State

Wa alaikumus salam, Alhaji Musa barka da warhaka.  Ina godiya matuka da wannan addu’a taka, tare da rokon Allah ya datar damu baki daya, tare da amfanar damu da abin da muke karantawa na ilimi a wannan jarida mai tarin albarka, amin.  Na gode matuka, Allah saka da alheri.


Assalamu alaikum, Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Ina yi maka fatan alhairi. Tambayata ita ce: wasu irin kwamfutoci ne ke lura da manhaja idan an kirkireta   ta salula ko kuma ta kwamfuta? Sako daga Abdoul Madjidou, Tripoli, Libya:  abouzeidiaffagar@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Abdoul Madjidou, ina godiya matuka.  Yaya mutanen kasar Libya?  Da fatan kana lafiya.  Idan na fahimci tambayarka sosai, kana son sanin a ina ake adana manhajojin da ake ginawa na kwamfuta ko wayar salula kenan.  Su manhajojin kwamfuta ko na wayar salula ko na Intanet (“System Application”, “Mobile Application”, ko “Web Applications”) idan an gina su, dole su zama a cikin wasu kwamfutoci a ajiye, ko a wata ma’adana ta musamman (Storage Device).  Ka sani, wadannan manhajoji wasu ne ke gina su, idan kuma sun gina su suna adana su ne a inda za a iya kaiwa garesu don ayi amfani dasu.

- Adv -

Misali, idan maginin manhajar kwamfuta ya gina wata manhaja ta Intanet (Web Application), don sayarwa ko rabawa kyauta, dole ya dora manhajar a inda masu ziyara ko masu saye za su iya gani kuma su sauke (Downloading).  Wannann wuri kuwa dole ya zama a kan gidan yanar sadarwa ne ko kuma a kan wata kwamfuta da za a iya riskar abin da ke cikinta ta hanyar gidan yanar sadarwa kenan.  In kuwa kwamfutar ba a jone take da Intanet ba, to, sai dai ya dora manhajar a kan faifan CD ko ma’adanar Flash Drive, don rabawa ko sayarwa ga masu bukata. 

Don haka, babu wasu kwamfutoci na musamman da su ne kadai ake amfani dasu wajen lura da manhaja ko adana su.  Kawai ya danganci zabi da halin wanda ya gina su, da kuma manufarsa; sayarwa ko rabawa kyauta.  Ita manhaja ta kwamfuta, dole ya zama a kan kwamfuta kadai ake iya dora ta.  Haka manhaja ta wayar salula, ita ma dole ne ya zama a kan wayar salula take.  Kowane abu na gudanuwa ne a mahallinsa.

Wannan shi ne dan takaitaccen bayanin da zan iya yi, idan har na fahimci tambayarka kenan.  Allah sa mu dace baki daya, amin.


Salamun alaikum Baban Sadik, ina miko gaisuwa tareda fatan Allah ya kara dauka ka. Sako daga mai jin dadin shirin Kimiyya Da Fasaha. Safiyanu Baban Annur

Wa alaikumu salam Malam Safiyanu, barka dai.  Na gode matuka da wannan addu’a taka.  Da fatan ana fahimta tare da amfanuwa da irin abin da ake karantawa a shafin namu.  Allah saka da alheri ya kuma sa mu dace baki daya, amin.


Assalamu alaikum. Da fatan kana cikin koshin lafiya. Ina bin ka sau da kafa.  Kwana biyu na ga kamar an tsere mini a shafin Kimiyya da Fasahar Kere-kere.  Ko zan iya samun duka jawabai dangane da  Hacking?  Shin, akwai damar na saka Imel dina wacce zan rika samun sakonninka kai tsaye? Na gode. Imran Ibrahim Ubale. iiajingi@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Imran barka da rana.  Lallai anyi nisa kuwa, domin mun dakata a kashi na hudu ne a fannin “Ethical Hacking.”  Bayan wannan darasi, duk da cewa bamu dauko wani darasi na musamman ba, mun kwashi kusan watanni uku ne yanzu muna ta amsa tambayoyi.  Wanda kuma na san akwai fa’idoji da dama a karkashinsu.  Idan har kana bukata, kana iya garzayawa zuwa babbar Taskarmu dake https://babansadik.com don karanta sababbin kasidun da na dora.

Idan kana bukatar shiga sahun wadanda za a rika aiko musu sakon sababbin kasidu kai tsaye, da zarar ka hau babban shafin, ka gangara can kasa za ka ga inda za ka shigar da adireshin Imel dinka.  Idan kayi haka, duk sadda na dora sabuwar kasida, nan take za ka samu sako a akwatin Imel dinka da ke sanar dakai hakan, da kuma adireshin da za ka bi don isa ga kasidar kai tsaye.

Da fatan ka gamsu.  Allah sa mu dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.