Waiwaye Kan Darussan Baya (7)

Ga duk wanda ya saba bibiyar wannan shafi tun farkon farawa, ya san mukan yi zama lokaci zuwa lokaci, don yin nazari kan kasidun da muka gabatar a baya, da fa’idar da suka samar, da kura-kuran da aka nusar dani a kai in har akwai, da sakonnin masu karatu, sannan mu ga nan gaba ina muka dosa.    Zuwa makon gobe in Allah Ya so za mu kawo sakonnin da kuka aiko ta waya ko ta Imel.  Akwai sakonnin masu karatu da yawa a tare; wasu ta akwatin Imel ne, wasu kuma ta Facebook, wasu kuma ta wayar salula.  Idan Allah Ya kaimu mako mai zuwa duk za mu zazzago su.  Wannan ita ce marhala ta bakwai, tun farkon fara wanann shafi a shekarar 2006, cikin watan Nuwamba.  Babu wani tazara ko ma’aunin watanni da muka sa don haddade kowace marhala.  Mukanyi irin wannan zama ne kawai idan lokaci ya samu; iya gwargwadon hali.

187

Kasidun Baya

Kamar sauran marhaloli ko zangon da suka gabata, a wannan zango ma mun gabatar da kasidu kan fannonin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere daban-daban.  Wadannan fannoni kuwa sun hada da fannin kimiyyar sadarwa bincike kan tasirin hanyoyin sadarwa na zamani ga al’umma, da fasahar sadarwa irin sun fasahar Intanet, da Imel, da Dandalin Abota (Social Media).  Sai kuma fannin kimiyyar kere-kere.

Daga cikin kasidun da suka gabata a wannan marhala akwai kasida mai take: “Alakar Katin Shedar Zama dan Kasa da Cin Gaban Kasa,” wadda muka gabatar cikin makonni biyu.  Kasidar ta dubi yadda yin rajistar ‘yan Najeriya don samar da rumbun bayanan ‘yan kasa gaba daya, zai taimaka wajen ci gaba a fannoni da dama.  Sai kasida mai take: “Dabi’u Da Nau’ukan Sinadaran Dake Cikin Ruwa,” wacce ita ma cikin makonni biyu muka gama ta.  Wannan kasida dai ci gaba ce, ko karin haske kan kasidar da muka gabatar a marhala ko zango na shida, mai take: “Ruwa da Nau’ukan Sinadaran Dake Cikinsa.”  Daga nan muka yi sharhi kan wani rahoto dake nuna yadda nan gaba ci gaban kimiyyar sadarwa na iya bayar da damar a saci tunanin mutum daga kwakwalwarsa.  Taken wannan sharhi shi ne: “Hattara! Ana iya Satar Tunaninka Nan Gaba.”

Daga nan kuma muka shiga wani sabon babi kan fannin tsaron bayanai, wato “Information Security,”  inda muka kwararo kasida mai take: “Ka’idojin Mu’amala da Password.”  Wannan na daga cikin kasidun da suka shahara a wannan zango.  Musamman ganin cewa dalilin da yasa na gudanar da bincike don yin haka shi ne don yawan tambaya da neman karin haske da nayi ta samu daga masu karatu.  Wannan kasida dai ita ce kasida mafi tsawo a wannan zango.  Sai da muka yi makonni 11 muna bayani kan wannan maudu’i.  Da yawa cikin masu karatu, har da daliban jami’a sun ta aiko bukatarsu don mallakar wannan kasida a dunkule.  A halin yanzu kasidar ta kai shafuka 35!  Bayan nan, mun kawo labaru biyu masu mahimmanci a fagen sadarwa.  Na daya kan samuwar manhajar BBM ne a wayoyin salula masu babbar manhajar Android.  Na biyu kuma kan rasuwar mutumin da ya kirkiri na’urar Berar Kwamfuta, wato: “Computer Mouse.”

A fagen kimiyyar kere-kere kuma mun fassara wani sharhi mai tsawo da marubuci Steve Dent yayi kan nau’ukan motoci masu amfani da makamashin lantarki.  Taken wannan fassara shi ne: “Me Ka Sani Kan Motoci Masu Amfani da Makamashin Lantarki?”  Wannan sharhi ya dauke mu tsawon makonni uku ne.  A daidai wannan lokaci ne kuma masu ta’ammali da fasahar Intanet suka kai biliyan uku.  Wannan yasa na gabatar da sharhi mai tsawo, mai take: “Masu Mu’amala da Fasahar Intanet Sun Kai Biliyan Uku!” 

A bangaren kimiyyar dabi’u kuma, mun kwashe makonni 4 muna nazari kan yadda mafarki ke samuwa, da asalinsa, da binciken malaman kimiyya da na falsafa kan mafarki, a kimiyyance, da al’adance, da kuma addinance.  Taken wannan kasida shi ne: “Yadda Mafarki Ke Samuwa a Kimiyyance.”  Ita ma kasida ce dake biye da asalin kasidar da muka gabatar a zango na shida mai take: “Samuwar Bacci da Mafarki a Kimiyyance.”  A yanzu na hade dukkan kasidun waje daya.  Kuma sun kai shafuka 21.  Wasu daga cikin masu karatu sun bukaci a aika musu kuma na aika musu a lokuta daban-daban.  Wannan na daga cikin kasidu da suka shahara sosai, musamman ganin cewa na yada ta a shafina dake Dandalin Facebook, don samun gamammiyar fa’ida.  Bayan wannan kasida kuma daya daga cikin masu karatu, Malam Sadik Tukur Gwarzo ya aiko mana wani sharhi mai tsawo da yayi kan ra’ayoin wani daga cikin masu nazari kan fannin kimiyyar sararin samaniya a duniya.  Mun buga wannan sharhi nasa cikin makonni biyu.  Muna godiya kwarai da gudunmawarsa.

A bangaren kimiyyar kere-kere kuma mun dubi na’urar: Black Box, wacce ke makale jikin jiragen, don tantancewa tare da taskance ire-iren abubuwan dake faruwa a jirgin, daga tashi zuwa sauka.  Taken wannan kasida da muka buga cikin makonni 4 shi ne: “Tsari da Gudanuwar Na’urar Black Box.”  Dalilin gabatar da wannan bincike shi ne bacewar jirgin saman fasinja na kasar Malesiya, wanda har yanzu ba a san inda yake ba.  Bayan nan kuma sai muka koma fannin wayar salula, inda muka kwashe makonni 7 muna nazari da bayani kan babbar manhajar android dake dauke cikin galibin wayoyin salular kamfanonin waya a yau.  Wannan kasida mai take: “Tsarin Babbar Manhajar Android,” ta shahara kusan fiye da sauran kasidu a wannan zango.  Dalili shi ne galibin jama’a na amfani da wayoyin salula ne masu dauke da wannan babbar manhaja.  Kafin zuwan wannan kasida, tuni bayani yazo kan babbar manhajar kwamfuta, wanda muka kwashe makonni 5 muna kawowa.

Wadannan kasidu duk na dunkulesu wuri daya a halin yanzu; na babbar manhajar android ta kai shafuka 26.  Na babbar manhajar kwamfuta kuma ta kai shafuka 16.  Daga nan muka jirga zuwa fannin sinadaran halitta.

Idan masu karatu basu mance ba dai, a shekarar 2012 ne muka fara wata doguwar kasida mai matukar tsaurin fahimta saboda karancin bayanan da suka shafi fannin a harshen Hausa.  Wannan kasida kuwa ita ce wacce muka sa wa take: “Tsarin Gadon Dabi’u da Siffofin Halitta (Genetics).”  Abin da wanna kasida ke dauke dashi dai shi ne dalilan dake sa ‘ya’ya ke gadon dabi’un iyayensu wajen siffa na bayyane, da siffofi na boye, da kuma dandanon rayuwa.  Wannan fanni bai tsaya kan halittar mutum kadai ba, ya hada da dukkan wata halitta mai rai, hard a bishiyoyi da shuke-shuke.  A baya mun tsaya ne a kashi na 6.  A wannan zango da muke kuma mun gabatar da kasidu 3.  Mun dakata ne a fannin gadon dabi’u da ya shafi shuke-shuke, da irin mahawarar da ake tafkawa a yau kan dacewa ko rashin dacewar hakan, musamman kan nau’in irin abinci da kayan marmari.  Wadannan su ake kira: “Genetically Modified Crops” ko “GMC” a gajarce.

Daga nan muka koma fannin tsarin sadarwa inda muka yi nazari mai zurfi, cikin gundarin fasaha da kimiyyar dake cikin gudanuwar manhajar Facebook; yadda aka gina manhajar, da nau’ukan dabarun gina manhajar kwamfuta da akayi amfani dasu, da kwamfutocin dake dauke da bayanan jama’a na kamfanin Facebook, da kuma tsarin da kamfanin ke amfani dashi wajen baiwa jama’a damar isa ga bayanansu daga ko ina suke a fadin duniya, ba tare da tsaiko ba.  Mun gabatar da wannan kasida cikin makonni 5 ne.  Ina sa ran ci gaba da gabatar da bincike kan wannan maudu’i saboda mahimmancinsa wajen fahimtar wannan fasaha mai matukar tasiri, a bangaren binciken sadarwa.  Shafukan kasidar sun kai 15 a halin yanzu.  Sai kuma ‘yar gajeriyar kasida kan manhajar Whatsapp mai take: “Tsarin Manhajar Whatsapp,” da kuma kasida dake bayani kan dabarun da ake amfani dasu wajen neman bayanai ingantattu a Intanet.  Ita kuma takenta shi ne: “Tsarin Neman Bayanai a Intanet.”

A bangaren kimiyyar teku kuma, mun gabatar da doguwar kasida mai take: “Tsarin Tekunan Duniya da Abubuwan dake Cikinsu.”  Kasida ce da take nazari kan samuwar teku, da nau’ukan tekunan duniya, da bambancin dake tsakaninsu, da abubuwan dake dauke cikinsu na halittu da albarkatu, da kuma irin bulaguron da aka taba yi ta cikinsu a zamanin baya.  A halin yanzu mun gabatar da kashi daya zuwa na takwas.  Mun kuma dakata ne a bayanin tekun Atlantika da irin albarkatun dake dauke cikinsa.  Sai kuma kasida mai take: “Tsarin Sadarwar Wayar Iska (Wireless Communication).”  Wannan kasida dai karin haske ne da sharhi kan wannan maudu’i da ya gabata a doguwar kasidarmu ta wayar salula mai shafuka sama da 80!

A bangaren hirarraki kuma, sashen Hausa na BBC sunyi hira dani a ranar da kamfanin Microsoft ya kaddamar da sabuwar babbar manhajarsa mai suna: “Windows 10,” kuma na rubuce wannan hira cikin shafuka 7, inda aka buga su cikin makonni 2.  Sannan na rubuce hirar da shahararren dan jaridar BBC mai suna Peter Taylor yayi da Edward Snowden, cikin shafuka 11, aka buga cikin makonni 3.   Sai kasidar karshe da muke kai, wacce kashi na 6 ya gabata a makon jiya, wato kasidar da muke nazari kan fasahar sadarwa ta rediyo a mahangar gundarin kimiyya ba sadarwa ta yada labarai ba.  Taken wannan kasida dai shi ne: “Tsarin Fasahar Sadarwa ta Rediyo a Kimiyyance.” 

Mu’amala da Masu Karatu

- Adv -

Kamar sauran lokuta a baya, na samu sakonnin masu karatu sosai, fiye da lokutan baya.  Domin a wannan zango kadai, mun kwashi makonni sama da 20 ana amsa tambayoyin masu karatu, a lokuta daban-daban.  Tambayoyin masu masu karatu da amsoshinsu za su kai shafuka 50 ko sama da haka, a wannan zango kadai.  Wasu kan kira ni, duk da cewa na haramta kira.  Amma nakan amsa, sannan in sanar da cewa sakon tes kawai ake karba ta layin.  Wasu kan ji ba dadi, amma dole ayi ta hakuri da juna.  Domin idan nace kowa ya kira zan amsa, to, bazan samu lokocin da zanyi wasu abubuwa ba.  Don haka, duk mai tambaya ko neman karin bayani, don Allah a rubuto sakon tes ko a turo Imel, ko a aiko sako ta shafina dake Facebook, zan tara sakonnin in amsa su.  Idan na bukatar neman kasida ce, zan aika.

Bayan haka, akwai masu min filashin har yanzu.  Sannan akwai masu kira na cikin talatainin dare.  Wasu cikin karfe 2 na dare, wasu cikin karfe 1.  Ina ganin kamar hakan bai dace ba.  Sannan akwai wadanda suka turo sako suna neman in basu amsar tambayarsu kai tsaye.  Wasu nakan yi kokarin gamsar dasu, wasu kuma nakan basu hakuri idan sun kira, sanadiyyar jin shiru daga gare ni.  A yi hakuri, domin zai iya yiwuwa sadda sakon yazo ina cikin wani aiki, ko wani uzuri da bazan iya amsawa ba.  Ni dan adam ne, kuma tara nake, ban cika goma ba.  Tabbacin da nake baiwa masu karatu shi ne, duk wanda ya aiko sakon tambaya ko neman karin bayani ko bukatar kasida, zan amsa bukatarsa duk tsawon lokaci in Allah Yaso.  Idan banyi hakan cikin lokacin da mai bukata yafi bukata ba, ina ba da hakuri.  Wannan gazawa ce daga gare ni.

A daya bangaren kuma, akwai masu aiko sakonni irin wadanda basu danganci shafina ba.  Wasu kan kira ni ne kai tsaye su min tambaya kan abin da ba ni da masaniya a kai wanda aka buga a jarida kan wani maudu’i, wasu kuma kan turo sakon tes ne.  Misali, akwai masu turo sakon tes suna tambaya kan matsalolin cututtuka dake damunsu.  A tunanina wannan tambaya ce da ta danganci shafin Dr. Auwal Bala na Kiwon Lafiya.  Ire-iren wadannan tambayoyi ba ni da amsarsu don basu danganci shafina ba.  Wasu kuma kan kira ni suna tambayar farashin wata wayar salula da suka ga an sa hotonta a shafina.  Ya kamata jama’a su san cewa, duk wani hoto da ake bugawa a shafi, ana sanya shi ne don karin bayani saboda alakar dake tsakanin hoton da bayanin da ake yi a shafin, amma ba wani tallar abin da ke kan hoton ake yi ba.

Nan Gaba…

A marhalar dake gaba in Allah yaso, zamu ci gaba da kawo kasidu kan fannonin da muka killace.  Sannan daga ciki kasidun da bamu gama nazari ba, za mu ci gaba dasu.  Misali, kasidar dake bayani kan tsarin gadon dabi’a da siffar halitta (Genetics), mun dakata a kashi na 9 ne, za mu ci gaba.  Haka kasidar dake bayani kan teku da nau’ukan ababen dake cikinsa, mun dakata a kashi na 8 ne, za mu ci gaba.  Haka kasidar dake bayani kan tsarin sadarwa rediyo a mahangar kimiyya, mun dakata a kashi na 6 ne, za mu ci gaba.  Kasidar dake bayani kan tsarin babbar manhajar android ma akwai bashi a kanmu; mun dakata a kashi na 7 ne, saura kasida daya in Allah Ya so.  A takaice dai, duk wata kasida mai tsawo da bamu karasa ba, in Allah Yaso za mu ci gaba.

ALBISHIR

A daidai wannan gaba nake son yi wa masu albishir cewa, kasancewar wadannan kasidu na taruwa, kuma da yawa cikin masu karatu kan bukace su, har da masu gudanar da bincike don karasa karatunsu na jami’a (daga masu digiri na daya, da na biyu har digiri na uku), na yanke shawarar bude shafin yanar sadarwa na musamman (ban da Blog da muka dade muna amfani dashi), don taskance wadannan kasidu; duk mai bukata na iya shiga ya karanta, ko ya saukar ko ya dabba’a duk abin da yake so, kyauta.  A halin yanzu dai ana kan gina wannan shafi ne.  shafi ne na kashin kaina, wanda na dauki dawainiyar sayan adireshi, da ma’ada, da kuma dawainiyar kintsawa, da dorawa, da kuma lura da wadannan kasidu.

A halin yanzu kasidun da suka bayyana a wannan shafi, gundarin kasidu kadai ban da tambayoyi, sun kai 280.  A wannan gidan yanar sadarwa da nake ginawa, akwai bangarori daban-daban kan fannonin ilimi da na taba rubutu akai.  Sannan akwai bangare na musamman na jera wasikun masu karatu zalla, tare da amsoshin da na bayar.  Sannan akwai bangare na musamman da na shirya don adana kasidun da na taba gabatarwa a wasu tarurruka da aka gayyaceni.  Duk wannan na tanade shi ne don fa’idantuwar masu karatu.

Kamar yadda na fada, ana kan shirya shafin ne a halin yanzu ba a gama ba.  Da zarar an gama zan sanar da adireshin, da yadda za ayi mu’amala da shafin, da duk wani bayani da zai taimaka wa mai ziyara don samun abin da yake nema a shafin.

Afuwa…

A karshe, kamar yadda na sanar a sama, gamsar da kowa da kowa ba abu bane bai yiwuwa a gare ni.  Don haka, duk wanda ya aiko wasika na tambaya ko neman karin bayani ko bukatar wata kasida, amma yaji shiru zuwa yanzu, ya gafarceni.  Akwai abubuwa da yawa na harkokin rayuwa da nake tsundume cikinsu.  Kai, ko da ba na komai ma, dan adam ne ni.

Godiya…

A karshe, ina mika godiya ga hukumar Media Trust, da Editan Aminiya, Malam Balarabe, da Malam Abubakar AbdurRahman (Dodo), da Malam Salisu Makera, da Malam Ahmad Muhammad Garba, da Malam Bashir Yahuza Malumfashi, da sauran ma’aikatan jaridar Aminiya kan irin gudunmawa da suke bani na shawarwari da fadakarwa.  Allah saka musu da alheri amin.  Godiya ta karshe ga dukkan masu karatun wannan shafi.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu a kodayaushe.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.