Sakonnin Masu Karatu (2018) (3)

Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

190

Assalamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kanan lafiya.  Mene ne bambanci a tsakanin “GPS” da “GSM Tracker”?  Kuma mene ne amfaninsu a wayar salula ko kwamfuta? Daga Aminu Adamu Malam Madori Jihar Jigawa. aminuadamummr@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Aminu barka ka dai.  Wannan wata fasaha ce ta sadarwa da ake amfani da ita wajen gano hakikanin bigiren na’urorin sadarwa na zamani, ciki har da motoci da duk wani abin da aka makala masa wannan na’ura.  Da farko dai tukun, kalmar “GSM” na nufin: “Global System for Mobile Communication” ne.  Wato tsarin sadarwar wayar salula na zamani, wanda ke taimakawa wajen aikawa da karban sakonnin sauti da rubutu da bidiyo da hotuna, cikin sauki da rahusa.  Wannan tsari na amfani ne da manyan taurarin dan adam da aka cilla su cikin falaki, don aiwatar da aikin. 

Sannan akwai “GPS”, wato: “Global Positioning System,” wanda shi kuma tsari ne dake amfani da tauraron dan adam shi ma, wajen gano bigire a duniyan.  Ta amfani da wadannan fasahohi biyu ne aka samar da wata fasaha mai zaman kanta mai suna: “GSM Tracking System”  ko kuma “GPS Tracking System.” 

Wannan fasaha tana dauke ne da bangarori ko ginshikai guda uku.  Na farko shi ne na’urorin sadarwa, irin su wayar salula, ko kwamfuta ko motocin da ake son sanin bigiren da suke, ko ake son amfani dasu wajen gano bigiren da suke.  Sai bangare na biyu, wato manhajojin da ke aiwatar da sadarwa tsakanin na’urar sadarwa ko motar da ake son sanin inda take, da kuma tauraron dan adam dake harbawa cikin falaki yana aiko siginar bayanai don nuna bigiren.  Sai bangare na uku, wato tauraron dan adam din, wanda ke kawo siginar bayanan. 

A bangaren wayar salula, kusan dukkan wayoyin salula na zamani suna zuwa da wata ginanniyar manhaja a tare da ita, ko wacce zaka iya saukar mata, mai taimakawa wajen aiwatar da sadarwa ta amfani da siginar rediyo dake wayar (na GSM), da kuma tauraron dan adam din dake cikin falaki, don bayar da hakikanin bigiren da wayar take, a ko ina ne a duniya.  Wasu wayoyin kuma suna dauke da manhajar ‘GSP’, wacce ita ma dai aikin nata kenan. 

A bangaren kwamfuta kuma, ana amfani da wannan tsari don gano inda wasu kayayyaki da suka bace suke (kamar wayar salula, ko wasu barayi da suka yi batan dabo, ko wata mota da dai sauransu).  A zamanin yau ma abin ya kasaita, hatta gidajen yanar sadarwa a Intanet yanzu sunan nan birjik, masu taimakawa wajen gano wadannan abubuwa ta amfani da wannan tsari. 

Galibin kasashen duniya da hukumomin tsaronsu duk suna amfani da wannan tsari (bayan sun caccanza shi zuwa yanayin da zai taimaka musu wajen aiwatar da ayyukansu), a fannin tsaro da kiwon lafiya, da kuma shugabanci.  Da wannan tsari har wa yau jami’an tsaro na iya gano mabuyar miyagun mutane muddin suna dauke da wata na’ura mai amfani da siginar rediyo a tare dasu, irin su wayar salula dai sauransu.

A bangaren motoci kuma, ana makala mata wata na’urar ‘yar karama mai dauke da wannan tsari, wanda za a iya amfani da tsarin “GPS Tracking System” don gano inda motar take, da yanayin da take, a kuma halin da take.  Galibin kamfanonin motoci a duniya sun fara gina wannan tsari cikin motocin zamani ma yanzu, ba sai an lika wa motar wata na’ura ba.  Sannan jami’an tsawo da kamfanonin gano inda motoci suke a duniya suna amfani da wannan tsari wajen takaita tazarar mota, ko nisan da za ta iya yi a wani bigire na birni ko kasa.  Da zarar ta wuce iya tazarar da aka sa mata, ko dai motar ta mutu nan take, ko kuma nan take tsarin ya aika wa jami’an tsaro sako dake nuna cewa motar na sata ne, a tsare ta.

A wasu kasashe kuma hatta mutane ana lika musu wannan na’ura ko suna iya amfani da wayoyinsu na salula musamman idan suna aiki a wani wuri ne mai matukar hadari ga rayuwarsu.  Ta yadda da zarar sun hango wata matsala, za su iya aikawa da sakon neman ceta nan take, wanda zai isa ga jami’an tsaro, don a ceto rayuwarsu.  Sai dai wannan tsari ba haka kawai yake yiwuwa ba, sai da hadin gwiwan jami’an tsaro da kuma cewa lallai tsari ne da gwamnatin kasar ta amince dashi. 

A  Najeriya misali, baza ka iya amfani da wannan tsari ba wajen neman ceton rai, domin ba ya cikin abin da jami’an tsaron Najeriya suka assasa don yin hakan.  Don haka ko ka aika sakon ma, ba inda zai je.  Wannan ba ya nuna cewa jami’an tsaron kasarmu ba sa amfani da wannan tsari a wani yanayin daban.  Amma ta bangaren ceton rai kam, babu shi yanzu.  Amma suna amfani dashi wajen gano bigiren kayayyaki da na’urorin sadarwa da dai sauransu.

- Adv -

A takaice dai, tsari ne mai dauke da hanyoyin kariyar lafiya da tsaro da a halin yanzu ake amfani dashi a wasu kasashe a duniya.  Kuma wannan shi ne dan abin da ya samu na bayanai.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, jinjina gareka, Allah ya kara basira da ilimi mai amfani.  Allah ya daga darajar jaridar AMINIYA.  Sako daga Bello Mijinyawa Galadima Mayosir

Wa alaikumus salam, Malam Bello ina godiya matuka da wannan jinjina.  Allah saka da alheri, ya kuma kara zumunci mai dorewa a tsakaninmu, amin.  Aci gaba da kasancewa tare da AMINIYA.  Mun gode matuka.


Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki? Tambayata ita ce! Ina da waya nau’in “Tablet Tecno G9”, to amma ba ta hawa Intanet, kuma kamfanin layina sunturo mini da “Settings” amma sai dai ta rika nuna mini cewa “Data Service has bloked.”  Shi ne nake son dan Allah ka taimaka mini. Na gode. Daga Aminu Muhammad Kundila, Kano State.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aminu Muhammad.  Ga alama dai matsalar kusa take.  Watakila ka jefa ne a “Flight Mode”, ba tare da saninka ba.  Sai ka duba bangaren “Settings” daidai wajen “WiFi” ko “Wireless” ko “Network Settings.”  Idan har ba a “Flight Mode” take ba, zai yiwu akwai matsala babba dake hana ta hawa Intanet.  Domin a zamanin yanzu ma dai, muddin ka dora katin “SIM” dinka a kan waya ko “Tablet”, ba ka bukatar wani sakon “Settings” daga kamfanin waya. 

Idan har abin yaci gaba, kana iya kaita wajen masu gyara, kwararru.  Zan maimaita: kwararru. Don su duba maka ita.  In kuwa babu wasu bayanai masu tarin yawa a kanta, kana iya “Resetting” dinta kawai.  Komai zai koma yadda yake, kamar yanzu ka sayota.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, gaskiya ina karuwa sosai da rubuce-rubucenka musamman akan abin da ya shafi Kimiyyar Samaniya da sauransu.  Allah ya saka maka da alhairi, ya kuma kara maka ilmi da aiki na gari, amin.

Wa alaikumus salam, barka dai.  Ina godiya matuka da kaunarka gareni.  Allah saka da alheri, ya kuma bar zumunci a tsakaninmu.  Allah kuma yasa ana amfana da abin da ake karantawa.  Idan an ga kuskure a rika tunasar damu.  Na gode matuka.  Allah saka da alheri, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, Ina maka fatan alheri bisa wannan kokari da kake yi a kodayaushe. Da fatan Allah Ya saka maka da alheri ya kuma karo daukaka, amin. Daga Musa G. G. C. Kurna Kano.

Wa alaikumus salam Malam Musa.  Ina godiya matuka da yabawanku sanadiyyar dan abin da nake gabatarwa.  Allah amafanar damu baki daya, kuma bar zumunci.  Aci gaba da kasancewa tare damu a kodayaushe.  Na gode.  Na gode.  Na gode.  Allah saka da alheri, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.