Saƙonnin Masu Karatu (2022) (11)

Dalilan Rufe Shafi a Facebook

A ƙa’idar ma’amala da fasahar Facebook, yawan shiga zauruka da yawa, musamman marasa alaƙa da manufar mai yin hakan, laifi ne.  Idan a ƙarshe hasashen manhajar tantance mutane yayi ƙarfi, nan take sai dai kaji an yi waje da kai.  – Jaridar AMINIYA, ranar Jumma’a, 21 ga watan Oktoba, 2022.

298

Kamar makon jiya, yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu.  Kada a mance dai, muna bayani ne kan dalilan dake sa Facebook ke rufe shafukan mutane.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

——————-

Shiga Zauruka (Groups) Bila Adadin

Idan manhajar Facebook ta fuskanci kana shiga zaurukan Facebook (Facebook Groups) barkatai, ba-kai-ba-gindi, wannan na iya alamta mata cewa lallai akwai matsala.  A wajen fasahar Facebook fa, yawaita shiga zaurakan Facebook, ko yawaita aika saƙonni ga mutane, ko aika saƙonni iri ɗaya, ko yawaita shiga zauruka, duk alama ce dake nuna cewa mai yin hakan yana neman hanyoyin yaɗa saƙonnin bogi (Spam) ne ga jama’a.  Don haka, a hankali idan yaci gaba, watarana za a kulle shafinsa; komai daren daɗewa kuwa.

A ƙa’idar ma’amala da fasahar Facebook, yawan shiga zauruka da yawa, musamman marasa alaƙa da manufar mai yin hakan, laifi ne.  Idan a ƙarshe hasashen manhajar tantance mutane yayi ƙarfi, nan take sai dai kaji an yi waje da kai.  A wasu lokuta akan sanar dakai cewa dalilan da suka sa aka rufe maka shafi su ne “kaza da kaza”.  A wasu lokutan kuma sai dai ka nemi shafin ma ka rasa.  Hakan ya faru ne saboda girman laifin wannan aiki.

Wallafa Kalaman Tsana Ga Wasu

- Adv -

An samar da Facebook ne don bai wa kowa damar bayyana manufarsa ba tare da nuna bambancin launi ko al’ada ko jinsi ko addini ba.  A taƙaice dai, kafa ce don kowa da kowa, daga ko ina kake, kuma kowane irin launi ne kai.  Dalilin dai kenan; don bayyana ra’ayoyi da manufofi ba tare tsangwama ba.  Kuma hakan na cikin sharuɗɗan da dole sai kowa ya amince dasu kafin a bashi damar buɗe shafi.  A shekarar 2020, hukumar Facebook ta goge saƙonnin tsana da ƙiyayya sama da miliyan talatin da biyu (32 million).  Wannan ke nuna yadda kamfanin Meta (Facebook) ya ɗauki wannan lamari da mahimmanci.

Wannan yasa kamfanin Meta ya samar da hanyoyin iya tantance ire-iren saƙonnin dake ishara ga tsana da kiyayya cikin harsuna daban-daban.  Duk sadda kayi amfani da kalamai makamantan waɗannan, ko hotuna masu isar da irin wannan saƙo, ko saƙon bidiyo mai ɗauke da hakan, to, wannan manhaja na iya tantance su, kuma a ɗauki hukunci a kanka.  Idan kuma hakan bai faru ba, duk wanda yaga ire-iren waɗannan saƙonni kuma ya kai koke, ko da abin bai shafeshi ba, to, ana iya amfani da wannan koke don ɗaukan mataki kan wanda ya aikata wannan laifi; musamman idan masu aika koken ma sun yawaita.

Yawan Aika Saƙon Abota Bila Adadin

Babban manufar kafa kamfani da gidan yanar sadarwa na Facebook a shekarar 2004, shi ne don hada alaƙa tsakanin abokai da ‘yan uwa da suka san juna a zahirin rayuwa.  Ma’ana, ta hanyar makaranta, ko zaman anguwa ɗaya, ko dangi ɗaya, ko alaƙar aure ko kasuwanci da dai sauran dalilai, a zahirin rayuwa.  Don haka, shi yasa idan ka gama rajista a karon farko, za ka ga an bijiro maka da wasu mutane da ka sansu a zahirin rayuwa, don a hada alaƙa a tsakaninka da su, tunda ka shigo.  Wannan tsari suna kiranshi da suna: “Friends You May Know”, wato, ga wasu abokan da watakila ka iya gane su.  Kuma tabbas idan ka duba za ka ga lallai mutane ne da ka sansu, ta dukkan hanyoyin rayuwa, a Zahiri.  A farkon bayyanar wannan tsari wasu sun ta min tambayoyi kan wannan tsari:  “Shin, ta yaya Facebook ke iya gane ka san waɗannan mutane a zahirin rayuwa?”  Nakan basu amsa da cewa, ba maita bace.  Bayanan da ka wallafa ne sadda kake cika fam don buɗe shafi.  Da waɗannan bayanai suke amfani wajen hasashen alaƙa tsakaninka da waɗanda suka riga ka ko ka riga su yin rajista a wannan mahalli.

Zaman laifyarka a Facebook, wajen neman abokai, shi ne a ga kana neman abota daga wajen mutanen da zahirin a rayuwa ka taba haduwa dasu ko akwai sanayya a tsakaninku.  Ko kuma sun san wasu abokanka.  Suna hasashen cewa muddin ka hadu da wanda ya san abokinka, to, sanayya a tsakaninku ba zai yi wahala ba.  Wannan tsari shi suke kira: “Friends of Friends”.  Amma neman abota daga wajen waɗanda babu wata alaƙa ta zahirin rayuwa a tsakaninka dasu, ko alaƙar tarayya da kayi dasu wajen abota da wani, suna ganin kamar ba abu bane mai yiwuwa cikin sauƙi.

Don haka, shi yasa idan ka fara aika saƙon neman abota (Friend Request) barkatai ga mutanen da, ta la’akari da bayanan da ka bayar sadda kake buɗe shafinka, bai kamata ace ka sansu ba a zahirin rayuwa, wannan na iya zama alama ga fashar Facebook cewa ba abota ka shigo yi da mutane ba.   Kawai ka shigo ne don tara jama’a a shafinka don wata manufa ta kasuwanci ba ta hanyar da ta dace ba.  A zato da tunani na tsarin Facebook, babu inda ya dace ka tallata kanka, ko tallata hajarka ta kasuwanci, ko kungiyarka ta siyasa ko wani abu makamancin wannan, sai ta hanyar Shafin “Facebook Page”.  Don haka, a wajen hukumar Facebook, idan aka lura kana aika wa mutane saƙonni barkatai, kawai suna ɗauka kana amfani da kafarsu ne wajen aika wa mutane saƙonnin tallace-tallace da ba su suka buƙata ba, wanda suke kira: “Spam mails”.

Shi yasa idan kana yawan aika saƙonnin abota ga mutanen da ba ka da alaƙa dasu a zahirin rayuwa, ta la’akari da bayanan da kayi da rajista dasu, nan take za a fadakar da kai, ko a fara tambayarka: “Did you know Dangote personally?”  Ma’ana, shin, da gaske ka san wane farin sani?  Idan baka daddara ba da wannan, kaci gaba, nan take za su kulle ka.  Har sai ka tantance kanka cewa kai ba dan Ɗandatsa (Hacker) bane, wato wanda yazo don ya riƙa kutse cikin shafukan mutane.  Idan ka kasa bayani gamsasshe, shafinka zai zama a kulle da’iman, har sai ranar da ka tantance kanka da gamsassun bayanai da hujjoji.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.