Fasahar Sadarwa ta Bluetooth (2)

A makon jiya mun yi tattaki ne zuwa dakin bincike don tsamo bayanai da suka shafi ma’ana, asali, tarihi da kuma bunkasar fasahar sadarwa ta Bluetooth, in da a karshe muka karkare da cewa wannan fahasar sadarwa ta bunkasa ne saboda tasirin ta wajen sawwake aikawa da sakonni daban-daban ta hanya mafi sauki, ba sai an yi ta hakilon jona wayoyi a jikin kayayyakin sadarwa ba.  A yau za mu ci gaba da bayani kan nau’ukan kayayyakin da ke dauke da wannan tsarin sadarwa mai kwarjini, da kuma tsarin aikawa da sakonni ta amfani da wannan sabuwar fasaha. Idan hali yayi, za mu zurfafa bayani kan abin daya shafi “ka’idojin sadarwa” (Communication Protocols) da kuma zangunan da ke sawwake wannan tsarin sadarwa, a fasahance, wato Protocol Layers. A biyo mu.

342

Kayayyakin Sadarwa Masu Dauke Da Fasahar “Bluetooth”

A farkon al’amari galibin mu mun dauka wannan fasahar sadarwa ta Bluetooth na dauke ne cikin wayoyin salula kadai.  Amma ga duk wanda ya karanta kasidar mu ta makon jiya, ya san cewa akwai kayayyakin fasahar sadarwa da dama da ke dauke da wannan fasaha a halin yanzu.  Duk da cewa wayar salula ce nau’in farko wajen samun wannan fasaha a shekarar 2001.  To akwai ta cikin wayar salula, ‘yar madaidaiciya, ba yar karama ba.  Na tabbata nan da wasu ‘ya lokuta ko shekaru, za a fara shigar da ita cikin kananan wayoyin salula.  Idan ka samu wayar salula nau’in Nokia, SonyErricsson, Motorola, da dai sauran su, duk suna dauke da wannan hanyar sadarwa ta Bluetooth.  Bayan wayoyin salula, sai kuma kwamfuta, manya da kanana, wadanda ake kerawa a wannan zamani, duk suna dauke da wannan fasaha. Idan ka samu kwamfutar tafi-da-gidan ka, wato Laptop, za ka samu tana dauke da nau’in sadarwa ta wayar iska, wato Wireless Network, wanda ke sawwake mata saduwa da ‘yar uwanta ba tare da an jona mata wayar kebul ba, za ka kuma samu tana dauke da wannan fasaha ta BluetoothDon haka, za ka iya aikawa da jakan bayani na sauti (sound files), ko haruffa (text files) ko kuma hotunan majigi (video files).  Haka na’urar sauraron wakoki wato MP3 Player, irin ta zamani, duk akwai masu dauke da fasahar Bluetooth

Galibin mutane masu irin wannan na’ura na iya aikawa da wakoki zuwa dukkan wata kwamfuta ko wayar salula mai dauke da wannan fasaha ta BluetoothHaka radiyoyin mota irin na zamani su ma yanzu, galibi suna dauke da wannan fasaha.  Idan radiyon na kunne, za ka iya aikawa da waken da ake bugawa daga rediyon zuwa ga wayar salular da ke dauke da wannan fasaha, kai tsaye, ba tare da matsala ba.  Haka idan kana da na’urar sauraron wake irin ta kunne, wato Headset, galibi su ma suna dauke da wannan fasahar sadarwa.  Kana iya aikawa da wakoki daga nan zuwa kowace irin fasahar sadarwa ta zamani da ke dauke da fasahar BluetoothBayan haka, akwai nau’rar daukan hoto irin na zamani, wato Digital Camera, duk su ma sun samu shiga duniyar Bluetooth.  Idan ka dauki hotuna, baka bukatar sai ka jona ma kwamfutar ka wayoyi kafin aikawa da hotunan cikin kwamfutar.  Kawai sai dai ka kunna na’urar, don aikawa da su kai tsaye ba tare da matsala ba.

Idan muka koma kan na’urar kwamfuta ta kan tebur (Desktop) milsali, tana dauke da hanyar aikawa da sakonni ta Universal Serial Bus, wanda ake kira USB PortWannan hanya na dauke ne da ka’idar mu’amala da kwamfuta, kuma hakan na faruwa ne ta hanya makamanciyar ta ; ma’ana, akwai hanyoyin aikawa da sakonni masu irin wannan  nau’i, irin su Flash DriveA halin yanzu akwai irin wadannan kayayyaki da aka tsara su don baiwa kwamfutar da bata da wannan fasaha ta Bluetooth ginanne a cikinka, daman aikawa ko karban bayanai a wannan  tsari na sadarwa.  Ana kiran su Bluetooth USB DevicesBa a kwamfuta kadai ba, duk wani kayan fasahar sadarwa mai dauke da irin wannan nau’i na aikawa da karban bayanai, za ka iya lika shi a jiki, don aikawa da karban bayanai. Har wa yau, ta amfani da na’urar buga bayanai na kwamfuta, wato Computer Printer, za ka iya ba ta umarni don buga maka bayanai da ke dauke cikin wayar salular ka mai dauke da fasahar Bluetooth. 

Haka idan kwamfutar ka na dauke da wannan fasaha, ba ka bukatar sai ka jona na’urar buga bayanai (Printer) da kwamfutarka, a a, sai ka kunna Bluetooth din ka kawai, ka aika da shafukan da kake son a buga maka su cikin sauki.  A karshe, kamar yadda bayani ya gabata a makon jiya, cikin shekarar 2007 ne aka kirkiri akwatin talabijin mai dauke da wannan fasaha ta BluetoothAbin dawannan ke nufi shi ne, za ka iya aikawa da shirye-shiryen da ake yi a cikin talabijin dinka, kai tsaye zuwa cikin kwamfutarka ko wayar salularka, idan har tana da mizanin da zai iya daukan bayanan.  A karshen wannan shekarar ne har wa yau, aka kirkiri na’ur lasifika ta sauraron FM a cikin mota, mai dauke da wannan fasaha.  Wannan na’ura ana kiranta MotoRokr T505 Bluetooth In-Car Speakerphone Digital FM Transmitter.  Dankari!

Ta amfani da wannan na’urar jin rediyon FM, kana iya karban kiran da aka yi maka ta wayar salular ka, muddin mai kiran ka na dauke da fahasar Bluetooth a wayar sa.  Da zarar ya kira ka, maimakon wayar salular ka ta amsa, sai wannan na’ura ta lasisfika ta kashe kanta na wucin gadi, ta fara kara.  Za ka iya amsa kira ta lasifikar, da zarar ka gama sai ta ci gaba da watso maka shiri ko waken da kake ji kafin wannan lokaci.  Wannan na’ura akan sayar da ita ne a farashin da bai wuce dalar Amurka dari da arba’in ($140.00) ba, wajen naira dubu goma sha takwas kenan nairan Nijeriya.  Kamfanin sadarwa ta Motorola ce ta kirkiri wannan na’ura, amma nan da wasu ‘yan lokuta, za a samu irin sa daga kamfanoni irin su Jabra, Nokia Corporation da ParrotWadannan, a halin yanzu su ne galibi kuma shahararrun kayayyakin fasahar sadarwa da ke dauke da wannan fasahar aikawa da sakonni ta Bluetooth.  To sai me?

Tsarin Aikawa da Sakonni ta “Bluetooth”

Kafin mu yi bayani dangane da tsarin da kayayyakin fasahar sadarwa ke bi wajen aikawa da sakonni ta amfani da na’urar Bluetooth, zai dace mu dubi kadan cikin ka’idojin da ke sawwake wannan sadarwa a farkon lamari.  Idan mai karatu bai mance ba, mun sha kawo bayanai kan ka’idojin sadarwa a wannan shafi, kuma muka nuna cewa yardaddun ka’idoji ne da dukkan masu fada-a-ji a wannan fanni suka amince da su wajen sadarwa.  Wadannan ka’idoji da aka yarda dasu, su ake shigarwa cikin kayayyakin fasahar sadarwa a fasahance, yayin da ake kera su, don ya zama akwai “fahimtar-juna” a tsakanin su, idan aka tashi hada su alaka da ‘yan uwansu masu wannan sifa ginanniya. Idan muna son fahimtar wannan cikin sauki, mu dubi tsarin kai-komo cikin gari, a mota.  Duk mai tuka mota a cikin biranen mu a yau, ya san cewa, da zarar yazo wajen danja ya ga an nuna masa launi ja, to dole ne a gareshi ya tsaya.  Idan launin ja ta dauke, aka nuna masa koriyar launi, to sai ya ci gaba da tafiya.

Wannan ka’ida, sananniya ce wajen duk masu tukin motoci da ma masu tafiya a kafa.  To amma idan babu danja saboda daukewar wutar lantarki, sai duk wajen ya cakude, mutane su kasa fahimtar junansu; kowa so yake ace shi zai wuce ba dan uwansa ba.  Don me ? Don babu tsari, kuma babu ka’ida a tsakanin direbobi a yayin da aka rasa sananniyar ka’ida ; kowa ra’ayin sa yake bi.

- Adv -

Akwai ka’idoji masu dama da suka shafi wannan tsarin sadarwa ta Bluetooth, amma guda hudu kawai za mu kawo, don su ne masu siffata mana mafi karancin tsarin da ake bukata kafin hada alaka a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da BluetoothDa farko dai, wannan fasahar sadarwa na amfani ne da tsarin aikawa da sakonnin ta siginar rediyo, wato Radio Frequency Waves (RFW), wanda a iliman fasahar aikawa da sakonni ta zamani ake ma lakabi da Spread Spectrum. Wannan tsari na Spread Spectrum shi ne tsarin da ke aikawa da sakonni ta hanyar nemo siginar rediyo mai alaka da abokin huldan sa, daga mafi karancin zango, sai ya yalwata siginar zuwa zango mafi fadi don sawwake hanyar sadarwan.  Wannan tsari na dauke da manyan ka’idoji guda hudu da ke sawwake wannan sadarwa ; akwai  Baseband Protocol (BP), wato ka’idar da ke haddasawa ko kuma samar da siginar rediyo (Radio Frequency Waves) don tabbatar da yanayin sadarwa a lokacin da mai son sadarwa ke bukata.  Hakan kuma na faruwa ne daga lokacin da ka kunna na’urar Bluetooth da ke jikin wayar salular ka, don nemo abokin hulda da ke da wannan tsari a waya ko abin sadarwan sa.  Sai kuma Link Manager Protocol (LMP), wanda ke yin aikin sa da zarar Baseband Protocol ya gama nashi aikin.

Shi Link Manager Protocol aikin sa shi ne haifar da sadarwa a tsakanin wayar salula da wata wayar ko fasaha mai dauke da Bluetooth, don tabbatar da tsarin sadarwan.  Wannan ka’ida ce har wa yau ke tabbatar da tsaro ga jakar bayanai da ake son aikawa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwan biyu.  Daga nan kuma sai ka’ida ta gaba, wato Logical Link Control & Adaptation Protocol (L2CAP), wacce ke kacalcala bayanan da ake son aikawa daga wayar da ake son aikawa da su, zuwa irin yanayin da suka dace a aika dasu.  Idan masu karatu basu mance ba, wannan aiki shi kwamfuta ke yi a zangon Presentation Layer, kamar yadda bayani ya gabata a kasidar Tsarin Aikawa da Sakonni a Tsakanin Kwamfutoci (2).  Za a kacalcala bayanan ne, don sawwake tsarin aikawa dasu.  Da zarar sun isa masaukin su a daya bangaren, akwai ka’idar da za ta gyatta su zuwa yanayin su na asali.  Har wa yau, wannan ka’ida ce ke tabbatar da samun yanayin aikawa da sako mai inganci.

Sai kuma ka’ida ta karshe, wato Service Discovery Protocol (SDP), wacce ke zakulo maka dukkan wata wayar salula da ke dauke da fasahar Bluetooth da zarar ka nemo, ta kuna nuna maka sunan da mai wayar ya bata ko kamfanin da ta kirkiri fasahar ta bata.  Wannan ka’ida ce ke hada alakar idan ka zabi wacce kake son aika mata.  Misali idan akwai wayoyin salula guda biyar masu kunne da Bluetooth din su a yayin da kake neman abokin huldan ka, za ka ga dukkan su, da sunayen su, sai ka zabi wacce kake son hulda da ita.  Idan ka zaba, wannan ka’ida ce ke yiwo maka barbaran wacce kake nema, kai tsaye.  Wadannan, a takaice, su ne shahararrun ka’idojin aikawa da kuma karban sakonni ta hanyar sadarwa ta Bluetooth, a fasahan ceA yanzu ga yadda yanayin ke kasancewa, a zahirance.

Aikawa da Sakonni

To kamar dai yadda muka saba ne, idan kana son aikawa da sako ta Bluetooth, abu na farko shi ne “neman” wayar salular da kake son aika mata da sakon.  Wannan shi ake kira Searching, a turancin fasahar sadarwa.  Da zarar ka yi wannan, ka’idar da ke lura da wannan aiki zata nemo maka wadanda ta hararo maka su, kai tsaye.  Dole ya zama suna tazarar da bai wuce taku talatin ba (30 Feets) ko mita goma (10 Meters) daga inda kake.  In sun wuce wannan tazara, ba za ka taba hararo su ba.  Idan aka hararo maka su, za ka samu bayanan da suke dauke dasu, ko kuma sunayen da masu su suka basu.  Da zarar ka nemo wayar da kake son hulda da ita, sai ta sanar da mai wayar cewa ana neman sa, idan ya amince, ta hanyar matsa Accept”.  Idan ya matsa, sai wayar ka ta nemo ka’idojin da suka dace tabi wajen aika sakon, ta kuma lika ma wannan waya da ta barbaro alamar da zata sheda ta wajen aika mata da sakon.  Daga nan, sai kuma ta kara binciko cikin wancan wayar, don tabbatar da dacewa da wannan alama da ta lika mata.

A ka’ida, dukkan wayar salula  ko kayan fasahar sadarwan da take iya saduwa da wata ta wayar iska, na dauke ne da suna da ke cikin rukunin lambobi, wanda ta kebanta dasu.  To idan wayar ka ta nemo sunan wannan waya da take son saduwa da ita, ta tabbatar da sunan ta, sai ta bata suna na musamman, sannan sai ta nemo kogo (Port) mafi sauki da zata iya aikawa da sakon, ba tare da mishkila ba. Da zarar ta nemo, sai ta fara Barbara, don sheida ma wancan wayar salula, cewa ‘gani nan tafe’.  Idan aka amsa mata, sai ta fara aikawa, kai tsaye.  Idan ta gama aikawa, sai ta rufe wannan hanya, tare da yanayin sadarwan. Ita kuma wacce ake barbara, da zarar sakon neman alfarma ya zo mata, sai ta taimaka wajen nemo ka’idar da za ta yi wannan aiki na karban sako. In ta nemo, sai kuma ta zabi kogon (Port) da zai karbi wannan sako, don shigar mata.  Da zarar ta gama wannan aiki, sai ta fara sauraron sakon.  Da zarar an turo, sai ta karba, kai tsaye.  Idan sakon ya shigo kogon da aka tanada masa kafin zuwa, sai ita wannan waya da ta karba, ta rufe kofofin da ta bude da farko, don cika sadarwa.

Duk wannan na faruwa ne lokacin da bai wuce dakiku ashirin ba.  Illa kawai aikawa da sakon ne ya danganta da yawan mizanin sakon ; idan mai yawa ne, zai dan dau lokaci.  Idan kuma kadan ne, nan da nan sai a gama.  Wannan tsari na aikawa, a yayin da ake aikawa din, shi ake kira Pairing, ko kuma Point to Point Communication (ko P2P, a lafazin ilimin aikawa da sako ta zamani).

Kammalawa

A karshe, za mu dakata a nan, kuma da fatan an gamsu da wannan takaitaccen bayani mai rikitarwa.  Idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa, za mu kawo bayani makamancin wannan dangane da fasahar sadarwa ta Infra-Red, wacce ta gabaci zuwan Bluetooth.  Na samu sakonnin tambayoyi kan alakar da ke tsakanin Bluetooth da Infra-Red, duk mu yi hakuri.  Bayanai na nan tafe.  Idan akwai neman Karin bayani, sai a rubuto ta 08034592444, ko kuma a aiko sakon Imel ta fasaha2007@yahoo.com. Haka ma ana iya ziyartan Mudawwanar da ke dauke da dukkan kasidun da ke bayyana a wannan shafi, a http://fasahar-intanet.blogspot.comIna mika sakon gaisuwa ta ga masu karatu, musamman masu aiko sakonni ta text ko Imel ko kuma bugo waya.  A dai ci gaba da kasancewa tare da mu.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA says

    JAZAKALLAHU KHAIRAN!!!

Leave A Reply

Your email address will not be published.