Facebook Gidan Rudu: Gabatarwa

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook a shekarar 2015.

215

Jama’a da dama suna mamakin wannan kalma dake sama, wacce na rubuta  jiya da rana a shafina.  Me yasa Dandalin Facebook ya zama “Gidan Rudu”?   Bayan ga karantarwa da fadakarwa, da tunatarwa, da sasantawa, da daidaitawa, da hankaltarwa, da nutsarwa, da fahimtarwa duk ana yi a ciki?  Wannan zance haka yake.

Sai dai na kalli wannan dandali ne ta dayan bangaren. Bangaren hauka da rashin hankali.  Bangaren shirme da shiririta.  Bangaren tsoro da tsoratarwa. Bangaren wauta da wawanci.  Bangaren tufka da warwarewa.  Bangaren yaudara da yaudaruwa.  Bangaren batsa da ashararanci.  Bangaren sakaci da rashin sakankancewa.  Bangaren shirka da kafircewa. Bangaren bidi’a da tasgaron aikin lada.  Bangaren hadari da halaka.

- Adv -

Wadannan na cikin abubuwan da ba kowa ke lura dasu ba, lura na neman hanyar mafita da samun sauki da salama.   Wanda shi ne abin da zan rika dubawa, duba na fahimta, ta hanyar misalai masu tabbaci (labarai da ganin ido), don samun mahanga mai warkarwa ga rayuwa da imani.

Ina fatan masu karatu za su kasance dani, ta hanyar karin bayani cikin abin da na fada, ko neman haske cikin abin da ya buya musu, ko fadakarwa cikin kuskuren da za su ci karo dashi.

Fatan Allah ya bamu mafita baki daya, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.