Manyan Fasahohi 5 Masu Tasiri a Duniya Waɗanda Har Yanzu Galibin Mutane Basu Fahimci Haƙiƙaninsu Ba a Aikace (2)

Fasaha ta biyu da galibin jama’a suka jahilci yadda take a aikace, ita ce fasahar “Metaverse”.  Wannan fasahar dai na cikin sababbin fasahohin dake ɗauke cikin sabon zubin “Web 3.0”; wato zubin giza-gizan sadarwa na uku, wanda muka yi nazari a kanta cikin shekarar da ta gabata in ba a mance ba. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 27 ga watan Janairu, 2023.

119

A taƙaice dai, duk wani abu da kake iya aiwatarwa a wayarka, ko kwamfutarka, tana iya sani.  Idan ma babu fasahar Intanet a kai sadda kake amfani da ita, da zarar ka kunna data, nan take za ta tantance abubuwan da kayi.  Duk wannan yana faruwa ne ta hanyar fasahar AI, musamman a wannan lokaci da muke ciki.

Wannan yasa da yawa cikin mutane, musamman a ƙasashen da suka ci inda harkar kasuwanci tafi shahara, sun cika da tsoron wannan tsari ko sabuwar fasahar sadarwa da ƙere-ƙere.  Wasu na ganin, ta la’akari da yadda wannan fasaha take, nan gaba komai zai koma hannun na’urori masu fasaha (Smart Devices).  Ɗan adam ba zai iya gudanar da komai ba sai dai na’urori da kwamfutoci kawai.  A tunaninsu, wannan zai haddasa rage ma’aikata a masana’antu da hukumomin gwamnati, sannan ya haifar da rashin aikin yi.

Sai dai wannan kuskurarriyar fahimta ce.  Fasahar AI dai ta zo ne don sawwaƙe rayuwa, tare da ƙayatar da tsarin gudanar da ayyuka cikin sauƙi kuma cikin ƙarancin kuskure.  Ta amfani da dokokin ƙayyade ma’amala da amfani da wannan fasaha, za a samu ci gaba sosai fiye da yadda ake zato.

Fasahar “Metaverse”

- Adv -

Fasaha ta biyu da galibin jama’a suka jahilci yadda take a aikace, ita ce fasahar “Metaverse”.  Wannan fasahar dai na cikin sababbin fasahohin dake ɗauke cikin sabon zubin “Web 3.0”; wato zubin giza-gizan sadarwa na uku, wanda muka yi nazari a kanta cikin shekarar da ta gabata in ba a mance ba.  Mun yi bayani kan fasahar AI, da fasahar EDGE Computing, da fasahar Blockchain, wanda a kanta muka dakata. Cikon ta huɗun ita ce fasahar Metaverse.

Kalmar “Metaverse” dai ta samo asali ne daga kalmomi guda biyu na harshen Latin.  Ta farko ita ce: “Meta”, wanda ke nufin “Waje”, ko “Na waje”.  Sai kalmar “Verse” dake nufin “Duniya”.  Idan ka haɗe su za su baka ma’anar “Duniyar waje”.  Sai dai kuma, a fannin kimiyyar sadarwa na zamani, “Metaverse” na nufin “wani mahalli ne da ake iya gudanar da harkokin rayuwa a yanayi mafi kusanci da irin yadda ake gudanar da su a zahirin rayuwa.”  Wannan sabuwar fasaha dai ta samo asali ne cikin shekarun da basu wuce biyar ba, duk da cewa akwai rubuce-rubuce da aka yi shekaru kusan 20 da suka gabata kan wata fasaha mai kama da wannan.

Dalilin samar da wannan sabuwar fasaha dai shi ne don samar da ƙarin inganci da tabbacin ma’amala a kafafen sadarwa na zamani, musamman Intanet.  Duk da ci gaban da aka samu a yanzu kan fasahar Intanet, da yaɗuwar kafafen sadarwa na sada zumunta da suka taimaka wajen haɗewa da game kan al’umma wajen sadarwa da kasuwanci da zumunci da samar da abubuwan yi don dogaro da kai, sai dai kuma a ɗaya ɓangaren an samu taɓarɓarewar tsaro ta hanyar sace-sace, da kutse, da satar zati waɗanda sun taimaka wajen zaftare wani kaso mai yawa na amincin da wannan ci gaba ya samar.

Bayan haka, tsarin alaƙar kusanci da nau’in hanyoyin sadarwa na yanzu suka samar na tattare ne da naƙasu ta ɓangaren nagartaccen sadarwa.  Ba ka jin akwai wani kusanci na haƙiƙa a yayin da kake magana da aboki ko ɗan uwanka ta hanyar bidiyo a Facebook misali, ko WhatsApp.  Sannan idan ma shagon sayar da kaya ko hajoji ka shiga a Intanet, sai dai ka ga hotuna da rubutattun bayanan hajojin; ba ka jin wani kusanci tsakaninka da mai shagon.  Haka abin yake a ɓangaren taro, ko tarurruka, ko bukukuwa, ko ziyara ta hanya da na’urar sadarwa ta zamani da ake amfani dasu a halin yanzu.  Rashin samuwar wannan yanayi na cikin naƙasun dake cikin tsarin da muke amfani dasu a halin yanzu.  Kuma shi ne gurbin da fasahar Meterverse tazo don ƙoƙarin cikewa.

A halin yanzu akwai kamfanoni sama da 20 da suke ta ƙoƙarin samar da wannan mahalli na sadarwa.  Fasahar Metaverse dai wani mahalli ne, ba wai duniya ce irin wannan da muke rayuwa a ciki ba; mahalli ne na sadarwa, amma ya sha bamban da irin wuraren da muke amfani dasu wajen sadarwa a yau.  A shekarar 2021 kamfanin Facebook ya sauya sunansa zuwa “Meta”, kuma ya sanar da cewa ya shiga cikin jerin kamfanonin dake hanƙoron samar da irin wannan mahalli.  To a ina wannan mahalli yake ne?

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.