Sakonnin Masu Karatu (2020) (9)

Tsarin Ginawa da Adana Gidan Yanar Sadarwa

An guba wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 11 ga watan Satumba, 2020.

342

Bayan gama jero bayanai kan fasahar AI da suka gabata cikin makonni 4, a yau za mu waiwaya jakar sakonninku ne don amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko. Idan muka gama sai muci gaba da kwararo bayanai kan Fasahar “5G” da muka faro a baya.  A sha karatu lafiya.

———————

Assalamu Alaikum, ina mika godiya ga Baban Sadik a kan ilmantar damu Hausawa game da ilimin kwamfuta cikin harshen Hausa. Don Allah yaya zanyi in samu wannan littafin da kayi sharhinsa?  Ina Agwara Local Government ne, a Jihar Niger: 08087607514, 081556174

Wa alaikumus salam, barka dai Malam, da fatan kana lafiya kai ma. Ina farin cikin jin cewa dan abin da nake rubutawa yana tasiri matuka wajen masu karatu.  Dangane da bayani kan littafin da nayi sharhi, ina kyautata zaton kana ishara ne ga littafin Malam Salisu Hassan (Webmaster), wanda aka kaddarar a garin Kaduna a farkon shekarar nan.  Kamar yadda na sanar da sauran wadanda suka bukaci bayani irin wannan, hanya mafi sauki na mallakar littafin ita ce, a tuntubi marubucin littafin kai tsaye a lambar wayarsa.  Na kuma aiko maka lambar wayarsa ta layukan wayarka da ka rubuta a karshen sakonka.  Idan ka tuntube shi, tabbas zai sanar da kai yadda za ka samu littafin cikin sauki.  Allah taimaka ya kuma amfanar damu abin da muke koyo na ilimi, amin.  Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik. Ga tambayoyina da nake neman karin haske kansu don Allah. 1) Wasu kalubale aka fi fuskanta a lokaci da kuma bayan gina website?  2) A bangaren rijistan adireshi kuma, shin, ana yin rijistane da wasu hukumomi ko kuwa? Na gode. Daga Magaji Aminu.

- Adv -

Wa alaikumus salam, Malam Magaji Bazazzagi barka ka dai.  Da fatan kana lafiya.  Da farko dai, Gidan Yanar Sadarwa dai shi ake kira: “Web Site”.  Shafuka ne dake dauke da bayanai rubutattu ko hotuna ko sauti ko kuma hoto mai motsi, wato bidiyo kenan.  Wadannan bayanai ana saka su ne, a zuba su cikin kwamfuta mai dauke da ka’idojin sadarwa tsakanin kwamfutoci da ake kira: “Hypertext Transfer Protocol” (HTTP).  Wannan kwamfuta ita ake kira “Web Server.”  Sai ayi rajistan adireshin da za a iya samun wannan kwamfuta mai dauke da bayanai, ta yadda da zarar an shigar dasu, za ta budo don a isa ga shafukan da ake nema. Wannan, a takaice, shi ne yadda tsarin shafukan Intanet ke aiki.  Kasancewar a halin yanzu abubuwa sun ci gaba sosai, akwai kamfanonin da ake biyansu don su adana maka shafukan Intanet; a duk sadda masu ziyara suka yi amfani da adireshin shafin, za a riskar dasu.  Wadannan kamfanoni su ake kira “Web Hosting Companies.”

Wannan ne ya kawo min amsar tambayarka ta farko, cewa: “Wasu kalubale ake fuskanta a lokaci da kuma bayan gina shafin Intanet?”  A gaskiya hakan ya danganta ne da ko kaine mai ginawa da kanka, ko kuma za ka biya wani ne ya gina maka.  Idan kai za ka gina da kanka, ka ga dole ya zama kana da kwarewa.  Sannan aiki ne mai dan karen wuya idan baka tsara shi ba tun farko.  Kamar gina gida ne a zahirin rayuwa.  Kana bukatar tsara yadda gidan zai kasance a takarda.  Sannan ka kiyasta abubuwan da ake bukata wajen gina gidan, kamar su bulo da siminti da kayan wuta da kofofi da sauransu.  A tsarin gida shafin Intanet, bayan ka gama zana yadda shafin zai kasance, sai ka tanadi abubuwan da za bukata a shafin iya yadda kake son ya kasance – kamar rubutattun bayanai, da hotuna, da bidiyo, da duk abin da ake so.  Wannan ba karamin aiki bane.  Idan kuma wani ne zai gina maka shafin, sai ka kwatanta masa yadda kake son shafin ya kasance, sai ya gina ka biya shi.

Babban kalubalen dake tattare da lura da shafin Intanet a matsayinka na mai shafin shi ne, dole ne ka rika sabunta bayanan dake ciki, wannan na cin lokaci musamman baka tsara yawan kwanaki ko watannin da za ka rika yin hakan ba.  Sannan akwai bukatar lura da sakonnin masu ziyara, musamman idan akwai abin da ka tanada don jin ra’ayoyi ko karban sakonnin masu karatu.  Dole ne ka rika duba sakonnin, sannan ka aika musu jawabi.  Bayan nan, akwai maimaituwan kudin adana shafuka, wato: “Hosting Fees” da za ka rika biya, a kowane shekara ko kowane wata; ya danganci yadda kamfanin ya tsara. Shi kanshi wannan kalubale ne, musamman idan shafin da ka bude don amfanin jama’a ne, ba don samun kudin shiga ba.  Sannan mafi girman kalubale shi ne ya zama a wasu lokuta a kasa samun shafin ma gaba daya.  Wannan kan faru ne saboda matsalar sadarwa da kamfanin ke samu.  Sannan idan jama’a suka yi yawa a kan shafin ma, ana iya samun tsaiko; sai shafin ya dauke gaba daya.  Kamar dai yadda ake samun matsala ne da yanayin sadarwar wayar salula (Network).  Babban abin damuwa dangane da irin wannan matsalar shi ne, ba ka iya yin komai a kai.  Idan shafinka ya dauke na tsawon awa guda ko tsawon yini, sai dai kawai ka rubuta wa kamfanin sako kan matsalar.  Kuma ba abin da za su ce maka sai dai: “kayi hakuri, muna aiki kan matsalar. Za mu shawo kanta nan kusa.”

Abu na karshe kuma shi ne, idan shafinka ba shi da Karin kariya na musamman, to, wani dan ta’adda na iya aiwatar da kutse a shafin, wato: “Hacking”, ya gurbata maka bayanan dake ciki, ko ma ya kulle shafin gaba daya a kasa hawa.  Kari a kan haka, akwai wadanda kuma bayan sunyi kutse cikin shafin, suna iya sace bayanan da suka shafi taskarka da ke kamfanin, suyi amfani dasu wajen sace maka adireshin shafin ma gaba daya.  Wannan ya yi daidai da irin yadda wasu ke iya sace maka layinka na wayar salula, ta hanyar “SIM Swap”.  Idan suka yi haka, nan take shafinka zai dauke, domin adireshin dake isar da masu ziyara ga shafin ya canza.

Sai tambayarka ta biyu, cewa: “shin, ko ana yin rajista ne da wasu kamfanoni?”  Eh to, ban fahimci irin rajistar da kake nufi ba.  Kana nufin rajista kamar irin wanda kamfanoni ke yi a hukumance?  In irin wannan ne, babu.  Amma kamar yadda na fada a baya, idan ka gina shafin Intanet dinka, dole ka sama masa adireshi.  Wannan adireshi shi ake kira: “Domain Name.”  Misali, shafin TASKAR BABAN SADIK, wanda ya kunshi makalolin da ake bugawa a wannan shafi a duk mako, adireshinsa shi ne: www.babansadik.com.  Da zarar ka shigar da wannan adireshi, nan take za a riskar da kai shafin kai tsaye.  Su wadannan bayanai ko haruffa dake adireshin, asalinsu lambar kwamfutar da ke dauke da shafin ne.  Wadannan lambobi su ake kira: “Internet Protocol Address” ko “IP Address”, a gajarce.  Rukuni ne na lambobi kamar haka: 192.168.10.3, misali.  Amma saboda hardace su abu ne mai wahala, sai a juyar dasu zuwa suna, don saukin mu’amala.  Kamar lambobin wayar abokanka ne dake wayarka ta salula; kowanne ka sanya masa suna. Idan ka tashi kira, ba sai ka latsa lambobin ba, sai dai kawai ka nemo sunan.  To, shi wannan adireshi, dole rajistansa ake yi.  Kuma dole ne ya zama suna ne da ko rukunin haruffa ne da babu wani shafin Intanet dake da adireshi irinsu.  Kamar dai yadda lambar wayarka, duk duniya babu wanda ke da lambar waya irin naka.  To, haka ma wannan.  Idan kayi rajistan adireshi, sai kuma yin rajista da kamfanin da zai adana maka shafin a Intanet, wanda za ka rika biyansa lokaci-lokaci.  Wadannan su ne nau’ukan rajista da za ka yi, wanda basu shafi gwamnati ba kai tsaye.  Allahumma sai in kamfaninka na saye da sayarwa ne, ko kuma kana son shafin ya zama kamfani na musamman wanda za ka rika amfani dashi wajen huldar kasuwanci tsakaninka da wasu, to, a nan kam dole kayi rajistan kamfanin da hukumar gwamnati dake lura da yin hakan.  Amma ba shafin Intanet din ba.

Wannan shi ne dan abin da ya sawwaka.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.