Intanet Da Rayuwar Hausawa

Wannan ci gaba ne daga kasidar da ta gabata a makon jiya, kan yaduwar harshen Hausa a Intanet, da irin huldodin da al’ummar Hausawa ke gudanarwa a Intanet.

426

Mukaddima

A makon da ya gabata mun yi tattaki zuwa dakin bincike don sanin alakar da ke tsakanin fasahar Intanet da harshen Hausa, da kuma lokaci ko shekarar da wannan fasaha ta samu riskuwa da kasar Hausa.  Daga karshe kuma muka kwararo bayanai kan yaduwar shi kanshi harshen Hausan cikin duniyar gizo; har muka gabatar da sunayen wasu daga cikin gidajen yanan sadarwan da aka gina su cikin harshen Hausa.   Da wannan, watakila wani zai yi tunanin ko fasahar Intanet ta shafi rayuwar al’ummar Hausawa a halin yanzu.  Wannan shi ne abin da muke son dubawa a wannan mako.  Bisimillah, wai an hada malamai fada:

Alal hakika samuwan daidaikun gidajen yanan sadarwa na harshen Hausa da kuma yawan mashakata tsallake-tsallake a biranen kasar Hausa ba shi ne ke nuna cewa fasahar Intanet ta shafi rayuwarsu ba, ko kadan.  Duk da yake fasahar sadarwa ta Intanet na iya shafar rayuwar al’umman Hausawa ta bangarori da dama, amma samun hakan a halin yanzu na da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa.  A wannan kasida zamu dubi dalilan da suka sa hakan ba zai yiwu ba a yanzu, da kuma abin da ya kamata a yi don samuwar hakan  Sai dai kafin nan, ga wata ‘yar gajeriyar shimfida don munasaba.

A kasida ta biyu cikin jerin kasidun da muka gabatar a wannan shafi, mun nuna amfanin Intanet ga kowace al’umma, musamman ga al’ummomin kasashen da suka ci gaba a fannin tattalin arzik’in kasa, wadanda kuma ta nan ne Intanet ya samo asali da bunkasar da yake kan yi a halin yanzu.  Gabatar da harkokin kasuwanci da siyasa da ilimi da bincike da sauran harkokin ci gaban rayuwa duk abubuwa ne da a wadannan kasashe ake iya yinsu ta hanyar sadarwa ta Intanet.  Bayanai har wa yau sun nuna cewa wadannan huldodin ana yin su ne cikin manyan harsunan duniya, irinsu Turancin Ingilishi da harshen Mandarin (na kasar Sin) da yaren Hindu (na kasar Indiya) da Jafan da Dutch da Rashanci da Faransanci da Italiyanci da kuma Larabci.  Wannan, a takaice, na yiwuwa ne saboda samuwar abubuwa guda uku, dangane da wadannan harsuna, a cikin Intanet.  Da wannan zamu iya cewa Intanet ya shafi rayuwarsu gaba daya, don babu wani bangare na huldodin rayuwa wanda basu iya yinsa ta Intanet, illa nadiran. 

Wadannan hanyoyi guda uku kuwa sune: samuwar haruffan wadannan harsuna (fonts) cikin masarrafan kwamfuta, da yawaitan gidajen yanan gizo na harkokin rayuwa – hajoji da sauransu – na wadannan harsuna cikin Intanet da kuma uwa uba samuwar babban manhajar kwamfuta cikin wadannan harsuna, wanda hakan ta sa suka zama kamar sune yaren Intanet (Web Browser) yayin da Intanet din ya habbaka.  Yadda za ka shigar da kalmomin turanci cikin Intanet ka nemo bayanai masu dimbin yawa, haka za ka sanya haruffan Hindu don nemo bayanai.  Har wa yau, a kasar Sin (China) bayanan baya bayan nan sun nuna cewa Sinawa (Chinese) sun fi amfani da haruffansu da kuma gidajen yanan neman bayanai na harshen Mandarin don neman bayanai da kuma saye da sayarwa da sauran huldodin rayuwa fiye da yadda suke amfani da kalmomi ko haruffan turanci don gabatar da irin wadannan huldodi ta hanyar gidajen yanan turanci irinsu Yahoo! da Google da Hotbot da sauransu.

A sharhinta na ranar Asabar, 14 ga watan Janairun shekara ta 2005, tashar talabijin CCTV9 na kasar Sin, ta nuna cewa kashi arba’in da biyar cikin dari (45%) cikin Sinawa na amfani ne da gidajen yanan neman bayanai da saye da sayarwa na harshen Mandarin, yayin da gidajen yanan turanci irinsu Yahoo! da Google dsr suka kwashi sauran kason.   Wannan, har wa yau, tasa gidajen yanan sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine) da saye da sayarwa irinsu Yahoo! da Google suka shahara, saboda suna da sashen harsuna da dama irinsu Mandarin da Hindu da Jamusanci dsr.  A takaice dai, ba komai ya sa harkokin hada-hada suka yawaita cikin wadannan harsuna ba sai don samuwan wadannan abubuwa uku cikin masarrafan kwamfuta wanda ko dai sun samu ne ta hanyar kamfanin Microsoft (a matsayin babban manhajar kwamfuta – Operating System cikin wannan harshe) ko kuma ta gidajen yanan sadarwa na Yahoo! da Google na shafukan da suka kirkira cikin wadannan harsuna a Intanet.

Dangane da bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa yaduwan harshen Hausa a Intanet, bai da wani tasirin da za a iya gwama shi da sauran harsunan da muka kawo misalansu a sama.  Wannan ya faru ne saboda harshen Hausa bai samu irin gatan da wadannan harsuna suka samu ta hanyoyin nan guda uku ba.  Duk da yake akwai bayanai da shafukan yana na harshen Hausa cikin Intanet.  To amma ba wasu shafuka bane da suka kai suka kawo.  Tunda ba za ka iya saye da sayarwa ba cikin harshen Hausa a Intanet.  Ba za ka iya samo bayanan Hausa ba zunzurutu ta amfani da haruffan Hausa cikin Intanet, kamar yadda za ka iya in da haruffan turanci kayi amfani.  Duk wadannan na bukatan wanzuwar bakaken Hausa cikin masarrafan kwamfuta a karo na farko.  Sai samuwar babban manhajar kwamfuta cikin harshen Hausa (operating system). A karo na uku kuma yawaitan gidajen yana ya Allah na saye da sayarwa ne ko na huldodin rayuwa kowace iri, cikin harshen Hausa.  Wannan  zai ba duk mai mu’amala da wannan harshe daman yin duk wata hulda na rayuwa cikin harshen Hausa a Intanet.   Za ka nemi duk irin bayanan da kake so ta amfani da haruffan Hausa ka samu.

- Adv -

A kasidarsa mai take: Hausa and Information and Communication Technologies, wacce ya gabatar a taron kara ma juna sani kan adabi da al’adun Hausa, wacce Sashen Nazarin Harsunan Najeriya dake Jami’ar Bayero ta shirya daga 13 – 16 na watan Disamba, 2004, Farfesa Abdallah Uba Adamu yayi doguwar bita kan irin kokarin da suka yi ta yi wajen ganin harshen Hausa ya samu hawa wadannan martabobi guda uku, don samun yaduwa da bin sahun sauran harsunan duniya a duniyar Intanet.  Duk da yake an samu ci gaba ta wasu bangarori, har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ma na abin da ya shafi yaduwar gidajen yanan gizo na hada-hadan kasuwanci da neman bayanai cikin harshen Hausa.

Gidajen yanan da muke dasu cikin harshen Hausa a yanzu duk da karancinsu, na al’adu ne da adabi da kuma addini.  Wasunsu ma masu su ba a nan Najeriya suke ba.  Wasu kuma  ma, kare da karau, masu su Turawa ne masu sha’awan harshen Hausa; malamai a Jami’o’in Turai da Amurka.  A bangaren Majalisun Tattaunawa kuwa, cikin Majalisu sama da dubu daya da ake dasu a Yahoo!, wadanda al’umman Hausawa suka bude suke tattaunawa cikinsu duk basu wuce hamsin ba.  Duk da haka ma, cikin kasa da hamsin din nan, wasu daga cikinsu da Turanci ake tattaunawa dasu ba da Hausa ba – duk da yake masu tattaunawan Hausawa ne galibinsu.

A bangaren dora harshen Hausa cikin babban manhajar kwamfuta (Operating System) kuwa, shima ba a kai ko ina ba.   Duk da yake kamar yadda Farfesa Abdallah Uba Adamu ya nuna ne cikin kasidarsa, cewa babbar matsalar da wannan aiki ke fuskanta shi ne na rashin tallafin kudi da kuma cikakkiyar mayar da hankali musamman a bangaren wadanda suke da halin yin hakan; ko dai saboda rashin kasancewarsu a nan gida Najeriya ko wasu dalilai na daban.  Cikin shekaran 2004, wani bawan Allah mai suna Muhammad Alimu ya farkar da wani kokari da aka assasa tun shekarn 1994, na samar da allon rubutun kwamfuta cikin harshen Hausa wanda ya sanya ma suna HausaWord 1.6, wanda yayi amfani da iliminsa na manhajar kwamfuta, watau Computer Programming, wajen samar dashi.  Kamar yadda shima Farfesan yayi nashi kokari wajen karasa ko dora haruffan Hausa (irinsu K’, B’, TS, D’ dsr) cikin tsarin masarrafan kwamfuta.

A halin yanzu ya samar da wannan tsari wanda ya sanya ma suna Abdallah TTF (watau True Type Font).  Ina daya daga cikin wadanda suke amfani da wannan tsari a halin yanzu.   Har wa yau, kamfanin Microsoft ta fara aiki kan kirikiro babban manhajarta na Windows, cikin harshen Hausa.  Wannan aiki ya kankama a halin yanzu.  Haka kamfanin Google ita ma.  Wannan na kunshe ne cikin  shirin da ta ke yi na dora dukkan harsunan duniya a masarrafansu.  Nan gaba zamu kawo bayanai kan wannan kokari da take yi, da kuma hanyoyin da take bi wajen cin ma burinta kan hakan.

Bayan samuwan wadannan kuma har wa yau akwai wani abu guda da ya kamata harshen Hausa ya samu, watau daidaito.  Da akwai bukatan daidaita Hausa cikin Intanet kamar yadda aka yi a rubuce, don dukkan mai neman bayanai ya samesu a fuskar da suka kamata.   Don haka ya zama dole a samu kungiyoyi da masana da kuma  gwamnatocin Arewa su hada kansu wajen ganin cewa Hausa ya samu hayewa matakan da suka kamata don tabbata a duniyar Intanet.  Don dukkan kokarin da na zayyana mana a baya, ko dai mutum daya ne ya zauna yayi ko kuma k’ungiya ce ta masana, kamar yadda su Farfesa Abdallah suka yi, wajen shigar da haruffan Hausa cikin masarrafan kwamfuta.  Babu inda zamu je in har abin ya ci gaba da zama a haka.  Dole sai an samu masu daukan nauyi da kudi da kuma wadanda za su zage dantsensu wajen yi ma Hausa gata a wannan zamani da kowace al’umma ke kokarin ganin an santa ta kowace fuska.

Duk da kokarin da kamfanoni irinsu Google da Microsoft  da Wickipedia, duk da haka ina ganin bai kamata mu shantake ba da wannan.  Don na farko, su wadannan kamfanoni suna kokarin yin hakan ne don habbaka kasuwancin hajojinsu, kuma ba lalai bane Hausa ya samu dukkan gatan da yake bukata, misali, na abin da ya shafi daidata lahaja, dole sai mun shigo ciki da dai sauran abubuwa da suka kamata mu yi ma kanmu. Babban misali ma shi ne kan abin da kamfanin wayar salula na NOKIA ta yi, wajen shigar da harshen Hausa cikin kananan wayoyin tafi-da-gidanka, watau NOKIA 1600.  Gurbataccen lahajar Hausa ce a ciki, duk da cewa sun yi kokari su ma.  Don haka ban gushe ba wajen kira ga Gwamnatocin Arewa – Kano, Katsina, Kaduna, Sokoto, Kebbi dsr – wajen ganin sun kai ma Malam Muhammad Alimu da sauran masu himma ta wannan fuska, dauki.

Allah Ya datar damu, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.