Bunkasa Harshe da Al’ummar Hausawa: Daga Adabi Zuwa Kimiyya da Fasahar Sadarwa ta Zamani (3)

Ga kashi na uku cikin jerin kasidun dake nazari kan rubuce-rubuce cikin harshen Hausa, da bukatar sauya salo zuwa wasu fannonin da ba na kirkirarrun labaru ba, don kara samar da wayewa ga al’umma.

607

Matsaloli

Akwai matsaloli da dama da suka haddasa karancin littafai ko rubutu cikin fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere a kasar Hausa.  Daga cikinsu akwai rashin tallafi daga hukumomi, musamman gwamnatin jihohin Arewa.  Da sun dauki wannan al’amarin da muhimmancin da ya kamace shi, da sauran kungiyoyi ko daidaikun mutane marubuta sun bi tsarin da suka assasa.  Amma sai ya zama da dama cikin gwamnatin jihohi basu ma damu da abin ba.  Ba ma ta wannan kadai ba, hukumar ilimi ma ba wani damuwa ake da ita ba balle wani fanni na musamman. Kamar yadda Farfesa Abdallah Uba Adamu yake nunawa ne kwanakin baya a hanyarsa ta dawowa daga kasar Jamus, bayan wani taro da suka halarta kan bunkasa harsuna da al’adu, (inda Ado Ahmad Gidan Dabino ya gabatar da wata makala kan harshen Hausa), cewa, da mun san yadda ake girmama harshen Hausa a sauran kasashen duniya, da mun daina masa irin wannan rikon sakainar kashin da muke masa.

Galibin Hausawa, ba ma gwamnatoci kadai ba, basu dauki harshen Hausa a bakin komai ba.  Matsala ta biyu kuma ita ce ta rashin sha’awar marubuta kan wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere.  A gaskiya galibin masu rubutu cikin harshen Hausa basu cika damuwa da wani fanni da ya wuce na kirkirarrun labarai ba.  Watakil saboda mutane sun fi sha’awar karanta labarai, wannan tasa kasuwar wadannan littafai tafi ci.  Don haka suna ganin idan sun yi rubutu, wa zai saya?  Wannan kuskure ne.  Domin su masu karatu fa cusa musu sha’awar ake yi.  Ya danganci tsarin rubutunka da kuma irin usulubin da kayi amfani da ita.  Matsala ta gaba ita ce ta karancin sha’awar masu karatu, kamar yadda bayani ya gabata a matsalar baya.

Sai kuma matsalar tsoron rashin kwarewa a ilimin zamani, wanda da dama cikin wadanda Allah Ya hore musu kudurar ilimin kere-kere suke fama da ita.  Ma’ana zaka samu mutum ya kware wajen iya kere-kere, ko wajen hada wasu sinadaran kimiyya masu amfanin al’umma, amma don tunanin cewa ba makarantar boko yaje ya koyo ba, idan kace masa ya taskance wannan ilimin nasa a rubuce don wasu su amfana, sai yace maka ai shi ba kwararre bane, don bai da shedar karatu kan kwarewar.  Wannan shi ma kuskure ne.  Domin zuwa makaranta don samun takardar gamawa fa sheda ce kawai, ba wai ilimin ba kenan.  Akwai da yawa cikin mutane masu ilimin da ke amfanar da jama’a, kuma ba makaranta suka je suka koyo ba.

Akwai misalai da dama, ba sai na kawo su daya bayan daya ba.  A takaice idan muka dauki Bill Gates, tsohon shugaban kamfanin Microsoft da ke kasar Amurka, kamfani mafi girma da dukiya a fannin manhajar kwamfuta a duniya, asalinsa bai taba zuwa makaranta don koyon ilimin kwamfuta da manhajojinta ba, har abada!  Lokacin da ya gama sakandare, mahaifinsa ya tura shi jami’a don karantar fannin tsimi da tanadi, watau Economics kenan, yana aji daya ya bar makarantar, don samun damar rubutawa da tsara manhajar kwamfuta ta farko; shekarunsa a lokacin basu wuce goma sha hudu ba.  Tun sa’adda ya bar makarantar, har yanzu bai koma ba.  Don daga can ya kafa kamfanin Microsoft, shekarunsa ashirin da biyar.  Amma ya kirkiro ilimin gina manhajar kwamfuta mai suna BASIC, wanda Allah kadai ya san miliyoyin mutanen da ke cin abinci sanadiyyar kwarewarsu da wannan fannin ilimi.  Kun ga ba makaranta yaje ya koya ba.  Allah cikin ikonsa ya yassare masa kwarewar.  Kuma akwai da dama cikin mutanenmu a nan cikin gida da waje, masu irin wannan mauhiba ta Bill Gates, amma zai yi wahala ka samu kashi hamsin cikin su da suka taskance iliminsu kan kwarewarsu.  Wannan ma illa ce mai zaman kanta.

Wata matsala har wa yau ita ce ta tsoron rashin kudurar rubutu da karatu.  Abinda wannan ke nufi shine, za ka samu mutum ya kware a wani fanni na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, amma saboda bai ma iya rubutun boko da karatu ba, haka wannan kwarewa zai tafi da zarar ya rasu, saboda ba zai taskance shi ba.  Don me?  Wai bai da kudurar rubutu da karatu!  A wasu kasashe irinsu Amurka fa akwai wadanda basu iya rubutu da karatu ba, kada ka dauka nan ne kadai muke da irin wannan.  Kuma mu daina daukan wannan tsarin rubutu da karatun boko a matsayin daya-dayan tsarin taskance ilimi, sam.  Idan muka yi la’akari da wakokin su Marigayi Aliyu dan Sidi, da Malam Aliyu Akilu, da sauransu, zaka samu duk da tsarin rubutun Ajami suka rubuta su. Daga baya aka zo aka mayar dasu zuwa tsarin rubutun latin, aka buga su a matsayin littafai, kamar yadda muke saya mu karanta a yanzu.  Kai ma kana iya rubuta abinda ka sani na ilimi ko kwarewarka ga wata sina’a ta kimiyya da fasaha cikin Ajami, ba a rasa wanda zai juya shi zuwa hausan boko.  Wannan shi yafi komai sauki ma.  Har wa yau, watakil kace ai kai baka iya rubutun Ajami ba, ko kuma makaho ne kai ko kurma, duk akwai yadda za a yi.  Kana iya karanto wa mai ji da gani da kudurar rubutu da karatu, ya taskance abinda ka sani.

- Adv -

Mu fa sani, galibin sahabban manzon Allah (SAW) masu ruwaito hadisai, basu iya rubutu da karatu ba.  Irin su Abu Hurairah, da Abdullahi dan Umar, duk ba su rubutu, amma ga ilimin da suka taskance a kwakwalwarsu ya same mu.   Haka ma galibin tabi’ai suke.  Littafin Al-Musnad na Imamu Ahmad dan Hambali, wanda a yanzu mujalladi talatin ne (sifili sittin), da ka yake halarto hadisan, ana rubutawa.  Littafin Adwaa’ul Bayaan, wanda tafsirin Kur’ani ne na babban Malami Aminud Deen Shanqeeti, dan kasar Mauritaaniya, da ka yayi tafsirin shi ma.  Mujalladi goma ne (sifili ashirin), aka taskance a kaset na rediyo, daga baya aka rubuce su tsaf!  Me yasa?  Don bai iya rubutu da karatu ba.  Idan ka rubuto masa wasika, sai dai a karanta masa.  Haka suke!  Sai dai su karanto abinda suka sani daga kwakwalwarsu, a taskance a rubuce.  Don haka matsala ce babba, kace sai ka iya rubutu da karatun boko sannan za ka yada abinda ka sani na ilimi ko kwarewar fasaha da kere-kere.  Wannan na cikin abinda ya dada dakushe karancin rubuce-rubuce a fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere a kasar Hausa.

Matsala ta gaba ita ce matsalar talauci.  Akwai da yawa masu so da kuma sha’awar rubuce-rubuce, ba a fannin kimiyya da fasahar sadarwa kadai ba, har da sauran fannoni, amma ba su da kudi da zasu buga ko yada littafan.  Wannan ma matsala ce, wacce da ace gwamnatocin Arewa na da wani tsarin tallafi, da an shawo kanta.  Akwai kuma matsalar rashin sha’awar rubutu daga kwararru.  Da ace duk wanda yaje ya koyo wani ilimi na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere dole ne ya rubuta littafi na musamman cikin harshen Hausa, wacce gwamnati za ta dauki nauyin bugawa, wallahi da al’amura sun canza.  Wannan shine galibin tsarin da wasu cikin kasashen Larabawa suke amfani da ita.  Idan kaje wata kasa ka koyo wani ilimi, kowane iri ne, da harshen turanci ko faransanci, dole ka rubuta littafi ko wata doguwar makala wacce ke bayyana nau’in ilimin da ka koyo, a kowane fanni ne cikin ilimin.  Na samu labarin cewa wannan shine tsarin da gwamnatin Iraki karkashin marigayi Saddam Hussein ke amfani da ita a baya, ban san yanzu ba.

Wannan na da muhimmanci, domin zai sanya sha’awa cikin zukatan kananan dalibai da ke sakandare, don sanin mahangar da zasu dauka da zarar sun shiga jami’a.  Kowa ya san tarin kwararrun da muke dasu a kasar nan, kan kowane fanni ne na kimiyya; daga likitanci zuwa fannin zane-zanen gidaje da kere-kere.  Mu kaddara ace kowanne daga cikinsu ya rubuta wani littafi cikin Hausa, kan fagen kwarewarsa, yaya?  Da yanzu muna da tafka-tafkan dakunan karatu a jihohi dabam-daban.  Allah kadai ya san tarin littafan da za a samu, da irin kwararrun da zamu samu, tare da samuwar ingancin ilimi a Arewa.

Domin idan rubuce-rubuce musamman irin na tsarin lissafi suka yawaita a Arewa cikin harshen Hausa, zasu sawwake da yawa cikin matsalolin da ke fuskantar ilimin ‘ya’yanmu na boko, wajen dasa kwadayin fannin lissafi da kuma sawwake shi.  A bayyane yake cewa tsarin ilimin kasar nan na tattare da matsala musamman na abinda ya shafi yadda ake bayar da ilimin.  Dalibai na koyon ilimin ne tare da koyon harshen da ilimin yazo dashi, duka a lokaci guda.  Dole su fahimci harshen sosai, idan suna son fahimtar ilimin da yazo dashi.  Ta la’akari da sauran matsalolin da suka shafi yadda gwamnati ke tafiyar da harkar ilimin, za a ga cewa samuwar kwarewa a fannonin biyu na samun matsala shi ma.

Matsalar karshe da zamu kawo, ita ce ta rashin bunkasar tsarin rubutu kan kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere.   Wannan na cikin matsalolin da Farfesa Muhammad Hambali Jinju yayi ta kokarin shawo kanta lokacin da yake koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello a Zariya, da Jami’ar Bayero da ke Kano, da kuma Jami’ar Danfodio da ke Sakkwato.  Tsarin rubutu kan kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere na bukatar samuwar sabbin kalmomi wadanda za a yi amfani dasu wajen aiyana wasu abubuwan da ake son siffatawa.  Har wa yau, yana bukatar dawo da wasu tsoffin kalmomin Hausa da aka daina amfani dasu a baya, don rayar da su.  A bangaren karshe kuma, yana bukatar wasu kalmomi da za a aro daga harshen da aka samo ilimin ta hanyarsa.  Domin aiki ne da ya kumshi fassara ko tarjama wasu littafai da ke dauke da wannan ilimi, daga wani harshen zuwa harshen Hausa.

Kasancewar harshen Hausa bai da wadatan kalmomi, kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya tabbatar kwanakin baya, musamman kan abinda ya shafi ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, dole a aro wasu kalmomin.  In kuwa haka ne, to wa zai tsara wadannan tsare-tsare?  Ko shakka babu, kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju yayi  a baya, hakkin hakan na kan Malaman Jami’ah ne su binciko hanyoyin yin hakan, ta hanyar kwarewarsu kan ka’idar kirkiran sabbin kalmomi da kuma sarrafa wadanda ake dasu, tare da fadada ma’anar masu rai.  Hakan kuwa, kamar yadda kowa zai sheda, ba ya samuwa ta yadda ya kamata.

Don haka duk mai sha’awar rubutu kan wannan fanni musamman ma a yanzu, dole zai ta cin karo da matsalolin da idan ba yayi hakuri ya kuma jure ba, sai ya ma fasa aikin.  Misali, shekaru uku da suka gabata lokacin da na yanke shawarar rubuta littafi kan yadda ake amfani da fasahar Intanet cikin harshen Hausa, na fuskanci wannan matsala.  Bayan karancin kasidu kan fasahar kimiyya da fasahar sadarwa (Information Technology), babu wani tsari ko wasu littafai da zasu sawwake maka hanyar sarrafa kalmomin don siffata abinda kake son siffatawa.  Sai makala guda da na samu wajen Farfesa Abdallah Uba Adamu da ke Jami’ar Bayero, wacce ke dauke da Tubalin Fahimta kan wasu kalmomi da suka shafi fasahar kwamfuta da Intanet.  A takaice dai, matsalolin suna da yawa, amma za mu takaitu da wadannan, don samun bayanin hanyoyin shawo kansu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.