Kamfanin “Etisalat” Ya Iso Birnin Abuja

An samu kari daga cikin kamfanonin sadarwa na wayar salula masu lasisi a kasarmu Najeriya. Amaryar da muka yi ita ce: “Etisalat”, daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa da ake ji dasu a kasashen larabawa.

320

Idan ba a mance ba, cikin shekarar 2006 ne gwamnatin tarayya karkashin shugabancin tsohon shugaban kasa Obasanjo, ta baiwa kamfanin Etisalat lasisin fara hada-hadar sadarwar wayar salula nau’in GSM a Nijeriya gaba daya.  Wannan lasisi ya fito ne daga Hukumar Bunkasa Harkar Sadarwa ta kasa, wato National Communications Commission (NCC), wacce ke da alhakin sanya farashi da kuma ka’idojin da duk wani kamfanin sadarwa zai biya ko bi, don samun gabatar da harkar sadarwa a Nijeriya.

Bayan lasisin da aka baiwa kamfanin a shekarar 2006, ya dau tsawon shekara daya da rabi yana ta tsare-tsaren kafuwa don fara tafiyar da harkokinsa a kasar; ta hanyar kafa cibiyoyin sadarwa masu dauke da na’urorin sadarwarsa, da mallakar ofishi a wurare irin su Legas da ma wasu manyan biranen kasan.  Bayan haka, kamfanin yayi ta maza wajen biyan kafafen yada labarai don tallata hajojinsa kafin wannan lokaci.  Har wa yau, kamfanin bai tsaya  a nan ba, yayi amfani da kafar hanyar sadarwa ta Intanet, wato ta hanyar gidan yanar sadarwarsa da ke http://www.etisalat.com.ng, don soyar da hajojinsa ga masu sha’awar hulda dashi, ta hanyar yin tayin kyautar lamba ta musamman (special number) ga duk wanda ke so.

Yadda abin yake shi ne, za ka shiga gidan yanar sadarwar ne a adireshin da ke http://www.etisalat.com.ng, sai kaje kai tsaye zuwa shafin da ke maka wannan tayi, wanda ke zauren gidan yanar (Homepage), ka shigar da lambar da kake amfani da ita a yanzu a wayar salularka.  Sai ka matsa alamar “send”, wacce za ta cillo maka wasu lambobi guda biyar nan take, da ake son ka shigar cikin shafin da ka aika da lambarka.  Kana gama shigarwa, sai ka matsa alamar “confirm”, wacce a karon karshe za ta aiko maka da lambar da kamfanin ya tanada maka ta musamman.  Za a zaftare lambobi ukun farko ne na lambarka, sai a bar maka sauran.  Misali, idan kana da lamba kamar haka 080-247-88040, sai su baka lamba makamanciyarta, kamar haka 080-987-88040.  A cikin sakon, akwai wasu lambobi guda bakwai, wato pass cord, wadanda ake son ka taskance a cikin wayarka.  Da zarar kamfanin ya fara aiki (kamar yadda ya fara yanzu), sai kaje ofishinsu ka nuna musu lambar da aka tanada maka, tare da wadannan lambobi na pass cord.  Da zarar ka je, zasu karbi lambobin, su shigar cikin kwamfutarsu, don tabbatar da cewa lallai haka ne.  Sai su baka katin SIM din kamfanin.  Idan ka samu lamba ta wannan hanya, kamfanin zai rika baka kyautar dakiku dari uku (30 seconds), ko mintuna biyar a kowace rana, kyauta; ka buga zuwa duk jihar da kake so a Nijeriya.  Sannan kana da damar zaban garuruwa goma da kake son a rika maka sauki yayin da ka buga waya zuwa wadannan wurare.  Wannan tsari na zaban garin da kake son a maka saukin caji, shi suke kira Home Zone. 

- Adv -

Wannan kamfani na Etisalat dai babban kamfanin sadarwa ne na wayar salula da ke da rassa a kasashe sama da goma sha-hudu a Gabas-ta-Tsakiya.  Daga cikinsu akwai irinsu Saudiyya da Kuwait da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa, wato United Arab Emirates.  Kamfanin ya fara aiki ne a birnin tarayyar Abuja cikin makonni uku da suka gabata, kuma katin SIM dinsa naira dari biyu ne.  Da zarar ka saya ka sanya, kana iya amfani dashi a dukkan kasar da kamfanin ke aiki.  Kana iya mu’amala da fasahar Intanet muddin wayar salularka ta mallaki fasahar yin hakan, ka aika ko karbi sakonnin text.  Haka idan ka kashe wayarka, duk wanda ya bugo alhalin wayar na kashe, za a sanar dashi halin da wayar ke ciki, sannan da zarar ka kunna, za a aiko maka da sakon text cewa “wane . . .ko kuma lamba kaza da kaza sun bugo lokacin da wayarka ke kashe”.  Idan kana son ganin lambarka kai tsaye daga wayar salularka, akwai lambobin da za ka matsa, sai lambar ta bayyana nan take.  Wannan duk kyauta ne!  Bayan wannan, kamfanin na da wasu hajojin sadarwa masu kayatarwa da babu wani kamfanin sadarwa mai irinsa  a nan Nijeriya.  Kuma farashin cajinsa kusan daya ne da na kamfanin MTN, amma ya sha bamban da kamfanin MTN wajen yawaitan hajoji masu sawwake farashi ko kuma masu kayatarwa, wadanda kyauta za ka same su ba tare da ka kashe kwabonka ba.

Ko shakka babu, bayyanar kamfanin Etisalat a sahun kamfanoni masu hada-hadar harkar sadarwa a Nijeriya zai kara haddasa saukin farashin caji da wasu kamfanonin ke yi mara misali, ya kuma sa wasu hajojin su samu inganci.  Misali, sanin kowa ne cewa daya daga cikin babbar matsalar da kamfanonin sadarwar wayar salula ke addabar masu mu’amala dasu itace rashin ingancin yanayin sadarwa, wato Network Service.  Duk wanda yayi amfani da tsarin sadarwa ta Etisalat, zai samu bambanci nesa ba kusa ba.  Duk da yake ta haka kowane kamfani ya faro, amma daga baya idan rumbun bayanansa suka cika da lambobi, sai a fara samun matsala.  Sai dai, galibin masu amfani da layin Etisalat a kasashe irin su Hadaddiyar Daular Larabawa, musamman birnin Dubai, sun shaida cewa lallai yanayin sadarwar kamfanin na da inganci da aminci.  Amma, kamar yadda muka sani ne, komai na Nijeriya ya sha bamban da sauran kasashe.

Fatanmu dai shi ne jama’a su samu ingantacciyar yanayin sadarwa, da farashi mai sauki da kuma mu’amala mai kyau daga wajen ma’aikatan kamfanin Etisalat;  ba ayi ta cika maka kunne da kade-kade ba duk sadda ka bukaci a warware maka wata matsala.  Barka da zuwa Nijeriya, ITTISAALAAT!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.