Bunkasa Harshe da Al’ummar Hausawa: Daga Adabi Zuwa Kimiyya da Fasahar Sadarwa ta Zamani (2)

Ga kashi na biyu cikin jerin kasidun dake nazari kan rubuce-rubuce cikin harshen Hausa, da bukatar sauya salo zuwa wasu fannonin da ba na kirkirarrun labaru ba, don kara samar da wayewa ga al’umma.

485

Ilimin Kimiyya da Fasaha Cikin Harshen Hausa

Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, fannin rubutaccen adabin kirkirarrun labarai ne ke da kaso mafi tsoka cikin fannonin ilimi da muke dasu a rubuce cikin harshen Hausa a yanzu.  Wannan tsari idan muka duba za mu ga ba tun shekarar 1980 ya faro ba, a a, tun lokacin mulkin mallaka ya faro.  Su shugabannin mulkin mallaka sun karfafa tsarin rubuce-rubuce ne da tsarin rubutun latin, wato haruffan boko da muke amfani dasu a yanzu, don tabbatar da cewa sun kawar da tsarin rubutun ajami, wanda shi suka samu muna amfani dashi don tafiyar da tsarin mulki da koyon ilimi da addini da kasuwanci.  Wannan tasa za a ga galibin rubuce-rubucen duk labarai ne kirkirarru, wadanda aka shirya gasa don karfafa rubutunsu, ko kuma aka sanya wasu masana a lokacin (irinsu Malam Abubakar Imam da sauransu) su fassara daga wasu harsuna kamar turanci ko larabci ko kuma harshen Masar.

Don haka ba abin mamaki bane ganin yadda littafai suka yi karanci kan sauran fannonin ilimi, musamman na kimiyya da fasaha.  Tabbas akwai ‘yan kananan littafai da aka rubuta kan kimiyyar halittu, irinsu Halittun Gida da na Daji, wadanda hukumar mulkin mallaka ta dauki nauyin bugawa, ake karantar da su a makarantu, amma basu taka kara sun karya ba.  Haka bayan an samu ‘yancin siyasa, ba a samu yaduwar rubuce-rubuce a fannin kimiyya da fasaha ba.  Wani abin bakin ciki ma shi ne, wadanda aka rubuta a baya, sai aka tsayar da buga su.  Wannan tasa ire-iren wadannan littafai suka yi karanci a kasuwa da makarantu da dakunan karatu.

Wajen shekarun 1980 zuwa 1990 an samu dan motsi wanda yafi labewa, lokacin da masana kuma masu kishin bunkasa harshen Hausa irin su Farfesa Muhammad Hambali Jinju suka fara tayar da kaimi wajen ganin cewa an samu bunkasa harshen Hausa ta hanyar yawaita rubuce-rubuce a wasu fannonin ilimi, musamman ma fannin kimiyya da fasahar kere-kere (Science and Technology).  Alal hakika Farfesa Hambali Jinju bai yi kasa a gwiwa ba wajen wannan kokari nasa.  Domin bayan kasidu da yayi ta gabatarwa a tarurrukan kara wa juna sani don tallata wannan manufa mai matukar muhimmanci, ya rubuta wasu littafai biyu masu matukar fa’ida.  Littafin farko da ya rubuta mai suna Littafin Maganin Gargajiya, ya fa’idantar sosai.  Domin da dama cikin mutane sun amfana da shi ba a Nijeriya kadai ba, har ma da Jumhuriyar Nijar.  Samuwar wannan littafi na nuna cewa ashe ba sai fannin ilimin da mutane ke dauka na zamani ne kadai za a iya rubutu a kai ba, a a, duk wani abin da ka san ilimi ne, zai amfani al’umma, to taskance shi yana da muhimmanci.

Littafi na biyu kuma ya rubuta shi ne kan fannonin ilimi da dama, irin su fannin lissafi (Mathematics), da kimiyyar kididdigar lissafi da kiyasi (Statistics), da kimiyyar halittu (Biology), da kimiyyar sararin samaniya (Space Science), da kimiyyar kwamfuta da kere-kere (Computer Science Technology), da kimiyyar man fetur (Petroleum Engineering), da kimiyyar sinadarai (Chemistry) da dai sauran fannonin ilimi da dama.  Ya sanya wa wannan littafi suna: Garkuwar Hausa da Tafarkin Ci Gaba.  Sunan wannan littafi ya samu ne daga irin manufa da kuma kishin da wannan marubuci ke da ita wajen ganin dacewa da kuma yiwuwar amfani da harshen Hausa a matsayin harshen kasa, tsakanin Nijeriya da Jumhuriyar Nijar.  Yace dukkan wani ilimi da ka sani, ana iya taskance shi cikin harshen Hausa, kuma hakan, a cewar Farfesa Muhammad Hambali, shi ne abin da zai kawo mana ci gaba, musamman ta la’akari da saukin fahimta da kuma kishi da mutane zasu ji na ganin kare wannan harshe ta hanyar ingantawa da kuma bunkasa shi.

- Adv -

Har wa yau, a shekarar 1988, madaba’ar Triumph da ke gidan Sa’adu Zungur a Kano, ta samu masana kiwon lafiya sun rubuta wasu littafai kan lura da lafiya.  Littafan kashi-kashi ne; babban taken su dai shi ne: Aikin Likita – Ilimin Cuce-Cuce Na Jikin Mutum.  Kamfanin ya samu kwararru ne kan harkar lafiya suka rubuta wadannan littafai, wadanda suka shafi nau’i dabam-daban kan kimiyyar magunguna da lura da lafiyar dan Adam.  Cikin wadannan littafai akwai wanda Likita Muhammad Kabir ya rubuta mai suna: Yadda Magani Ke Aiki a Jikin MutumLittafi ne mai kyau da fa’ida, wanda ke dauke da bayanai kan yadda ake shan magani, irin maganin da ya kamata a sha, da kuma lokaci ko tsarin da ya dace a sha shi.  A cikin wannan dan karamin littafi har wa yau, yayi bayanin cututtuka dabam-daban, da kuma magunguna masu hadari ga jikin dan Adam, irinsu guba da sauransu.  Wani babban abin farin ciki shi ne irin usulubin da mawallafin yayi amfani da ita, wacce ta kumshi hotuna da taswirori da kuma gajarta bayanai ta yadda mai karatu zai amfana da ilimi mai yawa cikin kankanin lokaci da shafuka.

Cikin ‘yan shekarun da suka gabata har wa yau, akwai rubuce-rubuce da wasu suka yi kan wannan fannin na kimiyya da fasaha.  Misali, akwai littafi da wani bawan Allah ya rubuta kan kwamfuta da yadda ake amfani da ita.  Akwai kuma kananan littafai kan yadda ake amfani da wayar salula.  Bayan littafan da kamfanin Triumph ya dauki nauyin bugawa kan likitanci, akwai wasu kuma wadanda aka buga, kanana, masu bayani kan tsarin likitanci da magunguna a tsarin musulunci.  Ire-iren wadannan littafai sun kunshi bayanai ne kan tasirin zuma da yadda ake amfani da ita wajen kawar da cututtuka dabam-daban.  Da kuma wadanda aka rubuta kan yadda ake amfani da zaitun da habbatus-sauda, da tafarnuwa da sauransu.

Akwai sauran fannonin da ba ka samun wani labari kan rubuce-rubucen da aka yi, (idan ma an yi kenan), balle samun littafai kansu.  Misali, fannin lissafi cikin harshen Hausa.  Ban ci karo da wani littafi mai bayanin yadda ake warware matsalolin lissafi da kididdiga ba, wato Mathematics & Statistics, wanda aka rubuta cikin harshen HausaWanda kowa ya san muhimmancin lissafi a fannin kimiyya da fasaha.  Ba ka samun littafai kan fasahar kwamfuta da kere-kere, da yadda ake amfani da kayayyakin sadarwa masu alaka da su. Misali, zai yi wahala ka samu littafi kan yadda ake gyaran talabijin, duk da tsawon shekarun da muka yi muna amfani da wannan fasaha.  Ga shi kuma muna da kwararru masu gyaran talabijin.  Babu littafai kan yadda ake gyaran rediyo, duk da cewa muna amfani da rediyo sama da shekaru talatin a kasar nan.  Haka aikin walda (welding), babu rubutu kan yadda ake sina’ar walda.  Wacce sina’a ce mai matukar muhimmanci ga al’umma a ko ina take, musamman ma yanzu.  Balle kace kana neman littafai kan yadda ake gyaran mota da babur da keke.  Ko kuma yadda tsarin jirgin sama yake, ko yadda jirgin kasa ke aiki.  Duk da shaharar wayar salula da samuwar masu gyaran wannan fasaha a kasar Hausa, har yanzu babu wani littafi tsayayye wanda ya zurfafa bayanai kan yadda tsarinsa yake, balle yadda ake gyaransa.  Fasahar tauraron dan Adam ta dade da shigowa kasar nan, amma har yanzu baka samun littafi guda kan wannan fasaha.  Kuma ga shi muna da masu wannan aiki, kwararru a kai.  In kuwa kana son neman jidali, to ka nemi littafi kan fasahar makami ko makamashin nukiliyya a harshen Hausa, ka ga ko za ka samu.

Kai a takaice dai, duk wani fannin rayuwa da ka sani, muna da kwararru a cikinsa, amma me yasa har yanzu babu littafai da zasu share maka hawaye in ka tashi nema?  Yanzu idan wani ya shigo kasar nan, mai sha’awar bincike kan ci gaban al’umma da al’adunta, sai mu ji kunya.  Domin hatta sina’o’inmu na gargajiya da muka tashi muka samu ana yi, littafai basu yadu ba kan yadda ake yin su ko tafiyar da su.  Sai dai yaje inda ake yi, ya taskance bayanai da kansa.  Da zarar masu ilimin sun mutu, shikenan sai su tafi da iliminsu.  Somin hatta ‘ya’yansu, basu cika son koyon wadannan sina’o’i, wai don suna makarantun boko.  To wa yace maka wai don kana makarantar boko baza ka zauna don koyon wasu sina’o’in ba?  Mai yasa wasu sina’o’in suka mace?

Idan muka koma bangaren wadanda aka rubuta kuma, in ka kebe littafan da kamfanin Triumph ta dauki nauyin bugawa, da wadanda Hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyin bugawa cikin littafan Farfesa Muhammad Hambali Jinju, ban ci karo da wadanda wasu kamfanoni  ko hukumomin Arewa ko wata Jiha suka dauki nauyin rubutawa tare da bugawa ba.  Zai iya yiwuwa akwai, amma ni ban ci karo dasu ba.  Wannan ke nuna cewa, galibin kokarin duk daidaikun mutane ne ke yi don ganin sun sanar da al’umma abin da Allah Ya sanar da su.

Wannan ke nuna cewa, littafai ko kokarin bunkasa rubuce-rubuce a fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere cikin harshen Hausa, an barsu ne a hannun daidaikun mutane.  Wanda kawai ya ga dacewar yin hakan, don burgewa, ko kudi, ko kokarin ciyar da al’umma gaba, yayi.  Duk da yake sauran fannonin da rubuce-rubuce suka yadu a ciki ma haka abin yake, amma wannan bai dace ba.  Wannan ba zai kai mu ko ina ba.  In har muna son bunkasawa tare da ciyar da al’ummar Hausawa gaba ta fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, dole a samu wani tsari da zai kai mu ga gaci.  Kafin kawo bayanai kan hanyoyin kai wa ga gaci, zai dace mu tabo kadan cikin matsalolin da suka haddasa rashin bunkasar littafai cikin wannan fanni.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.