Gaskiya da Gaskiya (7): Amfanin Ilimi, Aiki!

Idan babu aiki da kamantawa, duk yawan ilimi ya zama hutun jaki da kaya. Allah ka bamu ikon kamanta abin da ka sanar damu, amin.

307

Mu sake komawa majalisar Babban Malami AbdulRahman bn al-Jawzee (Allah Rahamshe shi), shehun Malami a birnin Baghdaad cikin ƙarni na biyar bayan Hijrah. Kafin in ce komai, bari in hakaito mana abin da ya faru, wanda ke da alaƙa da zancenmu na yau.

Watarana wani Bawa (slave) yazo wajen Malam, sai yace: “Akaramakallah, Uban gidana yana cutar da ni matuka; yana dora mini ayyuka masu wahalar gaske. Ina shan wahala ainun. Me zai hana kayi wa’azi kan muhimmancin ‘yanta bayi, watakila wannan Uban gidan nawa zai ji, hakan tasa ya ‘yanta ni in fita daga cikin wannan ƙangi?” Yana gama wannan zance, sai Malam yace: “Zan yi, in Allah Ya so.”

Wannan bawa ya je wajen Malam ne ranar Juma’a, yana ta sa ran yaji Malam ya yi wa’azi ko huɗuba mai zafi (kamar yadda muke cewa yanzu), amma shiru. Gari ya waye, shiru. Gari ya sake wayewa, shiru! A taƙaice, sai bayan mako guda, zagayowar wata juma’ar, sannan Malam ya ƙwanƙwashi zukatan jama’a, ya kwaɗaitar, ya kuma tsoratar kan muhimmancin ‘yanta bawa, da illar cutar dasu ko gallaza musu a ɗaya ɓangaren. Ana tashi daga wajen wa’azi, Uban gidan wannan bawa na komawa gida, sai kawai ya ‘yanta shi. Kwamfa! Ai sai murna wajen wannan bawa. Ya taso a guje, sai wajen Malam.

Yana zuwa sai ya fara gabatar da godiya kan wannan ‘yanci da ya samu, sanadiyyar biyan buƙata da Malam ya masa. Sannan yace: “Amma Malam ya aka yi baka kwaɗaitar ba sai bayan mako guda?” Faɗin haka ke da wuya sai Malam yace masa:

“Sadda kazo ka same ni ka mika buƙatarka, a lokacin ba ni da kuɗi. Ni kuma ba zan iya umartan jama’a su aikata wani aikin da ni ban aikata shi ba. Don haka na jira, har sai da na samu kuɗi na sayi bawa na ‘yanta shi, sannan na hau minbari nayi wa’azi kan muhimmancin ‘yanta bayi.”

- Adv -

Yanayi makamancin wannan ya faru ga Mujaddadi, Shehu Usman ɗan Fodio, Allah rahamshe shi. Ga yadda abin ya kasance.

Ɗaya daga cikin Malamaina muna karatu watarana sai bayani kan muhimmancin aiki da ilimi ya faɗo cikin karatu. Sai ya bamu labarin cewa watarana Mujaddadi na gabatar da karatu, sai ɗaya daga cikin dalibansa, wanda tun ƙanana suke tare, yace masa:

“Akaramakallah, wani abu na bamu mamaki dangane da lamarinka. Na ga tun yarinta tare muka fara karatun nan, amma yanzu tsakanin ƙarya da gaskiya ka rikiɗe ka zama malaminmu.” Sai Mujaddadi ya kada baki yace:

“Ai tun a littafin Ahlari na wuce ku. Tun da muka karanta inda Malam ke cewa: “Kuma ƙarya ya haramta ga baligi,” tun sannan ban sake ƙarya ba. “…da giba…” tun sannan ban ƙara giba ba….”.

Jama’a, yanzu irin wannan karatun muke yi ko kuwa karatun ƙure, da son jiyarwa, da nuna isa? Manya daga cikin darusan da na koya sanadiyyar kurakuran da na tafka a baya wajen neman ilimi, su ne: Iklasi, da Tawali’u. Rashin waɗannan sinadarai a rayuwar musulmi na sa ya wahala, daga farko har ƙarshe; a matsayinsa na malami ne, ko ɗalibi.

Allah, ga mu gare ka!

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    MASHA ALLAH

  2. Haruna Isah Idris Faskari says

    Allah ya jikan malam,shekara bakwai da watanni kenan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.