Fasahar 5G: Jita-Jita Da Karerayi Kan 5G (3)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 8 ga watan Janairu, 2021.

352

Fasahar 5G Makircin Yahudawa Ne

Wannan daya ne daga cikin manyan karerayi da ake ta yadawa, amma ta fi karfi a kasashe masu tasowa, musamman kasashen da musulmi suke da yawa.  Suka ce so ake a mallake tunanin mutane da sanin halin da suke ciki ta hanyar lika musu wata na’ura a jikinsu nan gaba, wacce Bill Gates ke Shirin samarwa.  Suka ci gaba da cewa wani shiri ne tsararre da ake ta yunkurin yinsa tsawon lokaci don manufar mallake duniya.  Duk da cewa akwai masu wannan tunani  a kasashen turai, amma an fi yarda da ita a kasashe masu tasowa, musamman kasashen musulmi.  Saboda na farko dai Yahudawa daman mutane ne makirai, tun asalinsu.  Kuma ba wanda Allah ya bashi labarin badakalarsu a fayyace irin Musulmi, a cikin Kur’ani mai girma.  Wannan yasa duk abin da aka ce Yahudawa ne suka kirkira ko asalinsa daga wajensu yake, to, musulmi kan yi dari-dari dashi.  Idan wata tsiya ce aka ce ya yi, nan take za a yarda.

Kuma duk da cewa Allah ya sanar da mu cewa Yahudawa makiran mutane ne, wannan bai nufin kowace karya aka debo aka ce su ne, kawai ka yarda.  Domin Allah ya sanar damu cewa akwai mutanen kwarai a cikinsu.  Ya kuma fadi hakan ne a cikin Kur’ani mai girma.  Don haka, bincike ya tabbatar da cewa kasar Isra’ila ba ta cikin kasashen da suka yi fice wajen samar da wannan fasaha.  Wannan tsagwaron karya ce.

Fasahar 5G Ce Ke Yada Cutar Korona

Akwai ra’ayoyi guda biyu mabanbanta kan wannan jita-jita.  Na farko na cewa, birnin da wannan cuta da Covid-19 ta bulla na cikin biranen da kasar Sin tayi gwajin fasahar 5G a cikinsu.  Wannan birni shi ne garin Wuhan.  Bayan ta yi wannan gwaji ne, sinadaran hasken sadarwa mai guba ya kashe dabbobin masu dimbin yawa a inda aka yi gwajin.  Guban dake cikin wadannan matattun dabbobi ne kuma ya yadu cikin birnin, ya haddasa cutar da yanzu ta addabi duniya, wato: “Covid-19”.  Ra’ayi na biyu kuma cewa yayi, wai makamshin hasken sadarwar da wannan fasahar 5G ke yadawa ko bazawa don baiwa masu na’urorin sadarwa damar aiwatar da sadarwa cikin sauki, yana dauke ne da sinadaran dake karya garkuwar jiki.  Kuma duk wanda ya kasance a mahallin da na’urorin yada yanayin sadarwar wayar salula masu amfani da fasahar 5G ke aiki, to, a hankali hakan zai kashe masa garkuwan jikinsa.  Shi yasa, duk wadanda garkuwar jikinsu take da rauni, nan take suke kamuwa da cutar Covid-19.  Wasu ma suka kara da cewa, a cikin makamashin hasken sadarwa na fasahar 5G, akwai wasu sinadarai dake bazuwa su shiga jikin mutane, kuma illarsu ba ta bayyana sai bayan lokaci mai tsawo.

- Adv -

Wanda yake kan gaba-gaba wajen yada wajen tsagwaron karya dai shi ne Dr. Sasha Stone, wani dan kasar Burtaniya.  Shi ne wanda ya shirya shahararren Shirin nan da yayi ta yawo a duniyar Intanet, ana ta yada shi musamman a shekararun 2019 da 2020, mai take: The 5G Apocalypse.  Wannan shiri na musamman (Documentary), ya kai makura wajen tsorata mutane saboda irin yadda aka tsara shi, aka yi hira da masana masu tunani irin na masu shirya fim din.  Sannan aka dauko wasu zantuka masu kama da gaskiya, wadanda ba don wannan munasaba aka fade su ba, duk aka shigar dasu cikin fim din.  Hatta wasu tarurruka da aka gudanar shekarun baya, sadda ma ko tunanin bullar wannan fasaha ba a yi ba, duk aka dauko su aka yada, don dai mai kallo ya yarda cewa wannan fasaha ta 5G yaudara ce, kuma makirci ce.  A gaskiya, duk wanda ba shi da juriya da kuma zurfin bincike, idan ya kalli wannan shiri, zai yi wahala ya samu natsuwa da wannan fasaha, balle ma har ya yarda cewa tsari ne kawai na sadarwa.

Masu wannan shiri sun ci gaba da yada jita-jitan dake wannan shiri a kafafen sada zumunta, da wasu daga cikin jaridu shahararru na kasashen Turai da Amurka, don kokarin gamsar da mutane da kuma jefa tsoro a zukatansu.  Ta wani bangare dai sun ci nasara takaitacciya.  Domin nan take mutane suka kama zanga-zangar dakatar da wannan tsarin sadarwa a kasashe da dama, ta dalilin cewa tsari ne batacce mai dauke da makirci ga lafiya da al’umma baki daya.  Zanga-zanga kadai bai isa ba, a kasar Burtaniya nan take jama’a suka kama kona na’urar fasahar 5G da aka girke a unguwanni, wato: “5G Masts”.  A wasu wurare irin su Liverpool, an kone tare da hankade wannan na’ura babu kakkautawa.  Abinka da jahilci ma, da yawa cikin wadancan na’urori da aka Konawa ma na fasahar 4G da 3G ne; ba su da alaka da fasahar 5G.  Sannan aka ta bin ma’aikatan dake aiki a kamfanonin sadarwar wayar salula, wadanda ke aikin gyara wa jama’a na’urorinsu idan sun samu matsala, ana razanar dasu cewa idan suka kuskura suka ci gaba da aikin nan, za a kashe su.

Wannan jita-jita ya samu karin tagomashi sosai inda da yawa cikin shahararrun ‘yan fina-finai, da ‘yan kwallo, da zakarun dambe, da shahararrun mawaka suka rika taimakawa wajen yada wadannan karerayi a shafukansu na sada zumunta.  Da yawa daga cikinsu a yanzu ba su iya Magana, saboda daga baya sun gano cewa sun yi saurin yanke hukunci, ko kuma anyi amfani da shahararsu ne wajen yada karya.

Dukkan wannan dambarwa ta auku ne daga sadda cutar Covid-19 ta fara yaduwa zuwa cikin watan Yuni na shekarar 2020.  Tsakanin watan Fabrairu zuwa watan Afrailu kadai, an kona na’urar sadarwar Intanet sama da 20 a kasar Burtaniya.  A yayin da aka kai farmaki kan guda 29 a kasar Holand.  A kasashen Ireland, da Amurka, da Suwidin, duk an samu aukuwar wannan nau’in ta’addanci ga na’urorin sadarwa.  A kafafen sada zumunta na bidiyo irin su Youtube da Vimeo kuwa, an samu bidiyo na karya masu dimbin yawa da aka zuba su.  Galibinsu duk suna dauke ne da ire-iren wadancan karerayi masu jefa tsoro da rudani a zukatan mutane.

A karshe dai an gano cewa kashi 60 cikin masu wannan ra’ayi sun samu wannan fahimta ce daga dandalin Youtube.   Na take hukumar Youtube ta fara bin ire-iren wadannan bidiyo masu dauke da karerayi, wadanda kuma suka saba wa ka’idar yada sakonni a kafar, suna goge su, ko suna boye ga idanun jama’a.  Wasu nau’ukan bidiyon kuma, ko ka binciko su ba ka samu, duk da cewa suna kan runbun bayanansu.  Domin wani bidiyo mai dauke da bayani kan fasahar 5G, kuma yake da dauke da Kalmar “Coronavirus”, to, sun cire shi.  Sun yi haka ne don rage yawan wadannan jita-jita mara asali, da rage yaduwar karerayi, a lokacin da ake bukatar kwantar da hankulan jama’a don mayar da hankali kan abu daya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.