Sakonnin Masu Karatu (2008)

Ga wasikun masu karatu nan, tare da amsoshi.  Kamar yadda na sha sanarwa, idan akwai bukatar Karin bayanai masu tsawo, a rika rubutowa ne ta Imel, sai in samu damar bayar da gamsassun bayanai kan haka.  Muna mika sakon gaisuwarmu ga dukkan masu karatu a ko ina suke, musamman masu bugo waya, wanda adadinsu ba ya kiyastuwa.  Kada su ji ba a ambaci janibinsu ba.  Mun gode matuka.

101

Assalam alaikum, bayan gaisuwa mai yawa da fatan alhairi, na ga cewa wannan muhimmin shafi namu ya sami cika shekaru biyu, tun daga lokacin da ya fara fitowa.  Ina fata Allah ya kara wa marubcin wannan shafi lafiya, don ya ci gaba da ilmantar da mu kamar yadda ya saba. Ita kuma jaridar AMINIYA Allah ya kara bunkasa ta, amin summa amin.       -Muhammad Rabiu Isa Ayagi Kano; 08029157450 rabiuisaayagi@yahoo.com

Malam Rabi’u muna godiya matuka da sakonka, Allah saka da alheri, Ya kuma bar zumunci, amin.              –  Baban Sadiq


Assalamu alaikum, ina yi maka barka da aiki.  Suna na Auwalu Muhammad.  Ni ma’abocin karanta jaridar AMINIYA ne duk sati; ba ma kamar shafinka.  Dan Allah kaci gaba da yi mana bayani kan wadannan miyagun makamai na Nukiliya.  Na gode, sai ka sake ji na.   Auwal Muhammad, 08024898216              

Malam Auwal, mun gode sosai, kuma Allah saka da alheri.  Za mu ci gaba da bayanai kan makamin nukiliya, musamman ta fannin makamashi.  Mun gode. 


Assalam Baban Sadiq, don Allah nawa mutum zai tanada ya bude gidan yanar sadarwa (website)?  Sannan mene ne bambancin (da ke tsakanin) Yahoo da MSN?  –  Ahmad Muhammad Amoeva, 08066038946

Malam Ahmad, ya danganci kamfani ko wanda zai gina maka gidan yanar sadarwar. Babu wani tabbataccen farashi kan haka.  Yahoo! Gidan yanar sadarwar kamfanin Yahoo! Inc. ne, mai manhajar wasikar sadarwa ta Imel – yahoo.com.  Shi kuma MSN (Microsoft Network), gidan yanar sadarwar kanfanin Microsoft ne, mai dauke da manhajar wasikar sadarwa ta hotmail.  Da fatan ka gamsu.


Salam Baban Sadiq, ina godiya da gaisuwanka; jarabawa ne ya boye ni.  Shi yasa kaji  ni shiru.  Amma na kusa kammalawa.  Sai a sanya mu cikin addu’ar samun nasara.  – Muntaka, Zaria. 08036397682

Malam Muntaka Allah baka sa’a cikin jarabawanka, ya kuma sa mu dace baki daya, amin.  


(Tuna Baya): Salamu alaikum Baban Sadiq, a yi min bayani kan tsohuwar kyamara irin ta da mai hoto baki da fari (black & white); dauka yanzu hoto yanzu. Da kuma irin ta zamani wacce minti daya hoto (one minute picture).  Malam, sakamakon kimiyya da fasahar da aka samu yanzu a duniya na kere-kere da kwaskwarimar abubuwa; ga shi waccan ta shude shekaru aru-aru tun hoton iyaye da kakanni da muke gani.  Malam, a rika zakulo mana irin wadannan su ma, mu kara karuwa dasu.  Allah Ya taimakeka, amin.   –                     Aliyu Mukhtar Sa’id, Kano. 08034332200

Malam Aliyu muna godiya da wadannan shawarwari, kuma kamar yadda na sanar da kai ta text kwanakin baya, ina nan tafe da ire-iren wadannan, ba ma ga na’urar daukan hoto kadai ba, har da sauran kayayyakin fasaha irin na da. Mun gode.  


Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, Malam yaya kwana biyu?  Ina fata kana lafiya.  Ina tunanin ko ka mance da tambayata ta kwanakin baya, amma sai ga shi na ga amsar a jarida.  Gaskiya nayi murna.  Har yanzu kar ka gaji damu;  tambaya ta ita ce, kamar yadda ake zama a kalli tashoshin satelait, ana ganin duniya dabam-daban, haka shi ma kwamfuta ko laptop yake?  In haka ne, ana biya ko ba a biya?  Ina fatan Malam za ka bani amsa.  Nine dalibinka, Alhaji Mala.  08033598315

Alhaji barka da hutawa, ina kara godiya da gaisuwarka kamar kullum.  Kwamfuta ba kamar tashoshin satelait yake ba; sai idan ka jona shi da Intanet, zaka iya kamo tashoshin da ke gidajen yanar masu tashar, har ka kalli shirye-shiryen da suke yadawa.  A nan baza ka biya komai ba, sai dai kawai kaji da kudin jona ka da Intanet da aka yi.  Sannan, kwamfuta ana amfani da shi ne wajen rubutu da karatu da kuma adana abubuwa da dama.  Ba kallo kadai ake yi da shi ba.  Da fatan ka gamsu.


Malam, bayani kan tauraron dan Adam; ainihin tarihinsa tun tali-tali ya zuwa yanzu.  Kuma yana da ire-ire ne?  Wanne ne karami, kuma wanne ne babba a taurarin? Da kuma sunayensu?  Kuma wane irin gudunmuwa yake bayarwa a bangaren kimiyya da fasaha ga ‘yan Adam?  Daga: Aliyu Mukhtar Sa’idu, Kano.  08034332200

Malam Aliyu barka da kokari.  Na tabbata yanzu kam baka bukatar doguwar amsa, ga kasidu nan mun kwararo.  Sai mun samu wasu tambayoyin naka kuma.  Na gode.  


- Adv -

Malam barka da yamma, yaya kokari?  Allah yayi jagora, amin.  Malam, mu masu karatun shafinka na Kimiyya da Fasaha a jaridar AMINIYA mai albarka, za mu so mu san alakar da ke tsakanin makamin nukiliya da wutar lantarki.  Daga AbdurRahman Sa’ad, Kano.  08038272727

Malam AbdurRahman, kasida ko kasidu kan haka na nan tafe in Allah Ya yarda.   Na dan dakata ne don mazayawa zuwa wani fannin kimiyyar.  A dakace mu! 


Da fatan ka sha ruwa lafiya. Muna taya ku murnar cika shekara biyu da fara yada shirye-shiryenku a jaridar Amintattu.  Daga Sani Abubakar (Na ‘Yankatsare, Jos). 08026023796

Malam Sani muna mika dimbin gaisuwarmu ga dukkan ‘yan makarantarka, Allah bar zumunci amin.  


Salam, Malam Abdullahi ina maka fatan alheri.  Daga sabon dalibinka, Ashsharir.  08038443566

Malam mun gode da gaisuwa, muna kuma mika tamu fatan alherin zuwa gareka.  Allah bar zumunci, amin. 


Malam ya ibada? Allah karbi ibadarmu, amin.  Ni ma ina taya jaridar jaridu (AMINIYA) murnar cika shekaru biyu, musamman ma wannan shafi mai albarka na kimiyya da fasaha wanda yai daidai da wannan zamani.  Malam, kungiyar makarantar jaridar AMINIYA ta jahar Kano nake tambaya?  Domin kada ai nisa da darussa ban shiga ba.  Daga: Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT), Kano.  08034332200

Malam Aliyu har wa yau muna kara yabawa da kokarinka.  Allah saka da alherinsa, amin.  Dangane da abin da ya shafi hadin kan masu karatun AMINIYA a birnin Kano (da gewayenta), kana iya tuntubar Malam Rabi’u Isa Ayagi, akwai lambar wayarsa a wasikar farko da ke sama.


Malam Abdullahi ina fatan kana lafiya.  Ni kam wata tambaya zan maka:  idan nayi digiri a fannin Kimiyyar Fasahar Sadarwa (Information Technology), zan iya samun aiki dashi a fannin soji a Nijeriya?  – 07030875753

Kamar yadda na sanar da kai, kana iya samun aiki a dukkan ma’aikatar da ke mu’amala da kwamfuta a ko ina take a duniya, ba ma Nijeriya kadai ba.  Ilimi kan Kimiyyar Fasahar Sadarwa shi ne ke ci a halin yanzu, kuma duk wani fanni da kake kai, idan ka hada shi da wannan ilimi, sai kayi fice, nesa ba kusa ba.  Allah yai mana jagora, amin.


 Assalamu alaikum, sakon gaisuwa gareka mai tarin yawa, da fatan kayi sallah lafiya, amin summa amin.  Kuma ina addu’ar Allah Ya karbi ibadarmu, amin summa amin.  Daga:  Rufa’i Ibrahim Danyaro, 08023222864, ibrahimrufai2006@yahoo.com

Malam Rufa’i barka ka dai, kai ma da fatan kayi salla lafiya.  Muna kara mika godiyarmu gareka.  


Barka da yau Baban Sadiq, da fatan kayi salla lafiya, Allah yasa haka amin.  Ni daya ne daga cikin dalibanka daga Niamey a Jamhuriyar Nijer,  na gamu da makarantarka ce a irin yawon da nake a Intanet. Na yi matukar farin ciki da samun wannan makarantar.  Za ka rika ganin sakonni na akai-akai, dan neman karin bayani a kan wadansu mas’aloli. Daga: Hamza M. Djibo, Niamey, Nijer.  alhamza_mjn@yahoo.fr

Malam Hamza muna godiya da wannan kokari da kayi, kuma Allah saka da alheri da wannan sako naka.  Nai matukar farin ciki da ganin daga Jumhuriyar Nijar kake, kuma a ci gaba da ziyartar Makarantar Kimiyya da Fasahar Sadarwa da ke Intanet, za a rika cin karo da dukkan kasidun da ake bugawa a Jaridar AMINIYA da ke nan Abuja, Nijeriya. Mun gode matuka.   

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.