Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya: Wa Ke Samar Da Tunani? (8)

Ga kashi na takwas kuma na karshe, kan binciken da muke yi wajen kokarin fahimtar bangaren dake samar da tunani, tsakanin kwakwalwar dan adam da kuma zuciyarsa. Da fatan masu karatu sun amfana da dan abin da na gabatar. A sha karatu lafiya.

628

Alaka Tsakanin Zuciya da Kwakwalwa

Sakamakon bincike na hudu da muka gano shi ne, akwai alaka mai karfi irin na sadarwa, a tsakanin zuciya da kwakwalwar kowane dan adam.  Wannan tsarin alaka na samuwa ne ta hanyar “musayar bayanai” a tsakaninsu, abin da malaman kimiyya suke kira “The Heart-Brain Synchronization” ko kuma “The Heart-Brain Connection.”  Wannan sabon fannin bincike na musamman an faro shi ne cikin shekarar 1991, kuma shi ake kira “Neurocardiology”, wato fannin bincike kan alakar da ke tsakanin zuciya da kwakwalwa. Wannan fanni ne ya tabbatar mana cewa akwai musayar bayanai nau’i uku da ke faruwa tsakanin zuciya da kwakwalwa.  Akwai nau’ukan bayanan da zuciya ke aika wa kwakwalwa, akwai kuma wanda kwakwalwa ke aika wa zuciya, sannan akwai musayar bayanai ta “ba-ni-in-baka” a tsakaninsu.  Dangane da wannan tsarin alaka ne kasidarmu ta yau, wadda ita ce ta karshe, za ta ba mu damar yanke hukunci kan wannan dogon bincike da muka faro.

 

 

Abu na farko da aka gano shi ne, zuciya ce ke taimaka wa kwakwalwa wajen tafiyar da ayyukanta a galibin lokuta; daga abin da ya shafi aika mata da jini – wanda da zarar ya dauke, kwakwalwa na iya daina aiki – zuwa aika mata da bayanan da take sarrafawa ta hanyar siginar sadarwa.  Hakan na faruwa ne ta hanyar “Gamammen tsarin aika bayanai na jiki,” wato “The Central Nervous System” wanda shi ne matsayin eriyar jikin dan adam wajen sadarwa.  An kuma gano cewa da zuciya da kwakwalwa suna musayar bayanai a tsakaninsu ta hanyar sinadaran maganadisun lantarkin kowannensu.  Amma sai dai kuma, bincike ya nuna cewa lallai sinadaran da zuciya ke samarwa don yada bayanai, sun fi karfin na kwakwalwa da wajen kashi 60 cikin 100.  Wannan na cikin sakamakon binciken da Cibiyar “HeartMath” ya tabbatar. Da kuma sakamakon binciken Dakta John da Beatrice Lacey da ke Cibiyar “Fels” (Fels Research Institute).

Abu na biyu shi ne, bincike ya tabbatar da cewa bayanan da zuciya ke aika wa kwakwalwa ya fi wanda kwakwalwa ke aika wa zuciya, nesa ba kusa ba.  Sannan kuma, bincike ya dada tabbatar da cewa galibin bayanan da zuciya ke aikawa zuwa kwakwalwa suna yin tasiri mai karfi wajen taimaka wa kwakwalwar yanke hukunci, da aiwatar da shawarwari, da hazaka, da kuma ji irin na tausayi.  Wannan ya saba wa tsohuwar fahimtar malaman kimiyyar zamanin baya, inda ra’ayinsu ya raja’a kan cewa kwakwalwar dan adam ce ke sarrafa sauran bangarorin jikinsa.  A yanzu bincike ya nuna karara, cewa zuciya ce ke sarrafa sauran bangarorin jiki.  Domin kashi 80 cikin 100 na bayanan da ke shigowa kwakwalwa daga sauran sasannin jikin dan adam, daga zuciya suke, kuma suna isa cikin kwakwalwa ne ta hanyar da ke karban bayanan da suka shafi zuciya, da huhu, da hanji, da tumbi, wanda ake kira “Nervus Vagus” a turancin malaman kimiyya.  Wannan na cikin sakamakon binciken da Cibiyar “HeartMath” ta fitar, da wanda Dakta Rollin McCraty ya tabbatar cikin kasidar sakamakon bincikensa mai take: “The Relationship Between Heart-Brain Dynamics, Positive Emotions, Coherence, Optimal Health and Cognitive Functions.”  A daya bangaren kuma, bincike ya nuna cewa idan kwakwalwa ta tattaro bayanai kamar yadda ta saba ta hanyoyin ji, da gani, da yanayin jiki ko mahallin da take ciki, ta tura wa zuciya don aiwatarwa, zuciya bata cika karban sakonnin dari-bisa-dari ba.  Sai ta tace, sannan ta zabi wanda yayi mata, in akwai kari ta kara a sama, sannan ta mayar ma kwakwalwa.  Da zarar ta tura wa kwakwalwa, kwakwalwa kan karba dari-bisa-dari ba tare da wani ja-in-ja ba. Haka sako idan daga zuciya yake kai tsaye, nan take kwakwalwa take sarrafa shi ta aiwatar.  Wannan na cikin sakamakon binciken da Dakta John da abokiyar bincikensa Beatrice Lacey da ke Cibiyar Bincike na Fels, wato “Fels Research Institute,” ya tabbatar.  Wannan ke nuna mana gamammiyar tasirin zuciya kan kwakwalwa.

Abu na uku shi ne, an gano cewa idan dan adam na cikin yanayin cikakkiyar natsuwa, tsarin bugun zuciyarsa kan yi tasiri sosai wajen samar masa da lumana.  Amma idan yana cikin bacin rai, sai bugun zuciyarsa ya sukurkuce, ya kasa samun natsuwa.  Wannan zai sa ya kasa sukuni, al’amuransa su shiririce.  Da bincike ya tsawaita, sai aka gane cewa wannan bugu na zuciya da ake kira “Heart Rhythm”, shi ne ke musayar bayanai da bangaren kwakwalwa da ake kira “Thalamus”, wato bangaren da ke samar da wayewa ko fahimtar dukkan bangarorin ji da gani da hankalta a jikin dan adam, kuma wannan alakar musayar bayanai ne ke samar da cikakkiyar natsuwa ga dan adam. Idan aka samu matsala bugun zuciya bai isar da sako daidai ba, ko yanayin bugun zuciya ya sukurkuce, to, kwakwalwa ba ta iya gudanar da ayyukanta. Wannan zai sa dan adam ya samu kansa cikin “kullewar kai”, ya zama kamar motar da ke kan tafiya, sai aka taka burki da totur dinta a lokaci guda. Wannan shi ne sakamakon binciken Dakta Rollin McCraty cikin kasidarsa mai shafuka 8 da na ambaci takenta a baya.

Abu na hudu shi ne, an gano cewa zuciya ce ke aikawa da siginar bayanan da kwakwalwa ke sarrafa su a nahiyarta da ake kira “Prefrontal Cortex”, wadda aka fi sani da bangaren da ke samar da tunani a kwakwalwar dan adam, kamar yadda bayani ya gabata a baya. A baya mun tabbatar da cewa malaman kimiyya a bincikensu na baya sun nuna cewa kwakwalwa ce ke yin tunani, ta amfani da bangaren da ake kira “Prefrontal Cortex.”  Amma wannan sabon bincike na nuna cewa bayanan da kwakwalwar ke sarrafawa a matsayin tunani, daga zuciya suke zuwa.  Bayan haka, a baya an dauka cewa hanya daya ce kadai zuciya ke iya aika wa kwakwalwa da sakonnin sigina, wato ta hanyar “Thalamus,” shi kuma ya rarraba sakonnin zuwa bangarorin kwakwalwa, dangane da yanayinsu da tsarinsu.  Wannan fahimta ta ilmi ita ake kira “Micro-pattern Model.” A yanzu bincike ya dada tattabar da cewa akwai wasu hanyoyi guda biyu kari, da zuciya ke aika wa kwakwalwa sakonni daga gare su.

Wannan sabuwar mahangar bincike ita ake kira “Macro-scale Model,” kuma wadannan hanyoyi su ne: ta bangaren kwakwalwa mai lura da nau’ukan dabi’u ko ayyukan zuci da na huhu, wadanda dan adam bai da kudura wajen sarrafa su.  Wannan bangare shi ake kira “Medulla Oblongata.”  Daga nan sai “Medulla” ya sadar da sakonnin ga bangaren kwakwalwa da aka sani da yin tunani, wato “Prefrontal Cortex.”  Sai hanya ta biyu da ake kira “Brain Rhythm”, wato bugun kwakwalwa; an lura cewa akwai nau’ukan musayar bayanai da ke samuwa tsakanin kwakwalwar da zuciya.  Wannan na cikin sakamakon binciken Dakta Rollin McCraty wanda yayi shi kadai, da wanda suka yi na hadin gwiwa da Dakta Mike Atkinson, da Dana Tomasino, da kuma Reymond Trevor Bradley, dukkansu kwararru ne kan harkar zuciya da kwakwalwa. Sai kuma sakamakon binciken Dakta John da Beatrice Lacey na Cibiyar Fels, shi ma ya tabbatar da haka.

Abu na biyar da aka gano shi ne, dangane da yanayin aikinta da kuma sakonnin da take karba daga zuciya da na sauran sasannin jiki, bincike ya nuna cewa kwakwalwa ba za ta taba iya rayuwa ba tare da samuwar alaka ta dindindin tsakaninta da zuciya ba, musamman. A daya bangaren kuma, zuciya na iya rayuwa ita kadai ba tare da ta dogara ga kwakwalwa ba.  A sakamakon bincikensa, Dakta Rollin McCraty dai har wa yau, ya nuna cewa: mutumin da kwakwalwarsa ta mace (Braindead) ko wanda ke halin suma (Comatose), kwakwalwarsa a tsaye take cak.  Amma zuciyarsa na karban sako, tana sarrafa su, sannan tana bugawa, tare da aikawa da sakonni ta hanyar sinadaran maganadisu (Electromagnetic Waves).  Dalilin faruwan hakan na cikin sakamakon binciken Dakta Andrew Armour ne, kwararre kuma shahararren masanin ilmin fannin zuciya da kwakwalwa da ke Jami’ar Halifax na kasar Kanada, wanda ya fitar a shekarar 1991.  Shi ne masani na farko da sakamakon bincikensa kan alakar da ke tsakanin zuciya da kwakwalwa ya zama turba a fannin ilmin likitanci.

- Adv -

Bincikensa ya tabbatar da cewa: zuciya na da nata tsarin sadarwa na musamman da take iya tunani da shi; mai kama da wata ‘yar karamar kwakwalwa mai zaman kanta. Domin akwai tarin jijiyoyin sadarwa (Heart Neurons) sama da dubu 40 a cikin zuciya, da kwayoyin halitta masu harban sinadaran lantarki daga zuciya, wato “Neurotransmitters”, da sinadaran kara kuzari ga kwayoyin halittar zuciya (Heart Proteins), da kwayoyin halitta na musamman masu isar da sakonni  a yanayin sinadarai, wato “Heart Cells”.  A karshe ya tabbatar da cewa zuciya na iya rayuwa ba tare da taimakon kwakwalwa ba, tana kuma iya tunani, da koyon ilmi, da taskance ilmi, da tuno abubuwan da ta haddace, da fahimtar mahalli da yanayin jiki.

A nasu sakamakon binciken, Dakta Gary Schwartz da Linda sun gano cewa, yadda kwakwalwa take da jijiyoyin sadarwa tsakaninta da sauran sasannin jiki, haka zuciya take dasu, kuma tasirin zuciya wajen sarrafa jiki ya shallake na kwakwalwa nesa ba kusa ba. Shi yasa idan zuciya ta fahimci wani abu ba tare da sanin kwakwalwa ba, kafin kasa da dakika guda, jini ya kai sako ga kwakwalwa nan take.  Sannan bincike ya nuna cewa, akwai lokutan da zuciya kan yanke hukunci kan abin da ya bayyana mata cikin gaggawa, wanda a cewar masana, ba ya bukatar ta sanar da kwakwalwa don hakan zai jawo bata lokaci.  Da wannan ne wasu masana ke ganin cewa lallai zuciya ita ma tana tunani wajen zartar da ayyukanta ba tare da sani ko taimakon kwakwalwa ba a wasu lokutan.  Karin tabbaci kan haka na cikin sakamakon binciken Dakta Rollin McCraty, cewa akwai wani nau’in tunani na dabi’a da zuciya ke da shi, wanda ba ya bukatar wani bayani daga kafofin ji, da gani, da hankalta kafin ya darsu a cikinta.  Wannan nau’in tunani shi  masana ke kira: “Intuition”, kuma shi ne ke taimaka wa zuciya hararo hatta abin da bai riga ya faru ba kafin faruwarsa, saboda tasirin wani boyayyen yanayin “Hankalta” ko “Fahimta” da Allah kadai ya san yanayinsa.

Wannan ya dada tilasta ni kara bincike don gano tabbacin “tsarin tunanin zuciya” a aikace. Da na koma dakin bincike sai na samu bayanai da ke nuna cewa, galibin wadanda ake musu dashen zuciya, idan suka warke, sukan dabi’antu da dabi’un masu asalin zuciyar da aka dasa musu.  Labari irin wannan ruwan dare ne a kasashen da ake yawan dashen zuciya.  Wasu kan zama mashaya giya, bayan a baya ba dabi’arsu bace.  Sannan na samu misalai na wasu da aka dasa musu zukatan wasu, suka kama tunani irin na masu asalin zuciyar. A ka’idar dashen zuciya ba a baiwa mara lafiya labarin wanda za a dasa masa zuciyarsa; wani irin cuta ya kashe shi?  Kuma me yayi ajalinsa?  Duk ba a gaya musu.  Amma akwai wanda aka masa dashen zuciya, cikin dare ya kwanta sai ya kama mafarki, inda ya farka yana ambaton sunan mai asalin zuciyar, alhali bai ma taba saninsa ba.  Da ya farka sai ya kira Likitan da ya masa dashen, ya tambaye shi sunan da yake furtawa, da likitan yaji asalin sunan mai zuciyar ne, sai ya fahimci abin da ya faru, nan take yayi ta lallabansa kan ya daina tunani kan haka.

Abu na shida kuma na karshe shi ne, an gano cewa, dangane da yadda kwakwalwa ke sarrafa bayanai musamman wajen samar da tunani, hakikanin bayanan ko tunanin ne take jerawa, da tsarawa, da kuma hada alaka a tsakaninsu wajen rarraba su.  Misali, idan bayanai nau’uka daban-daban suka shigo cikin kwakwalwa daga zuciya da sauran sasannin jiki, suna zarcewa zuwa bangaren “Thalamus” ne, wanda shi ne kamar “karen mota” ko “yaron motar” kwakwalwa.  Ma’ana, shi ne yake aikin rarraba bayanan zuwa sassan kwakwalwar da ya kamata su je.  Idan ya tura, sakamakon da aka samu daga sauran bangarorin kuma suna dawowa gare shi ne.  Shi yasa ma su Dakta McCraty a cikin wancan doguwar kasida mai shafi 103 suka mayar da raddi ga wadanda ke siffata kwakwalwar dan adam da masarrafar kwamfuta ta zamani.  Ga abin da suke cewa a shafi na 47: “An dade ana kwatanta aikin kwakwalwa da masarrafar kwamfuta. Sai dai kuma, idan muka yi la’akari da yadda kwakwalwa ke sarrafa bayanai, ko kadan bata yi kama da na’urar kwamfuta ta zamani (Digital Computer) ba.  Domin (kwakwalwa) ba ta tsara tunani da fahimta ko hankaltar yanayi a irin tsarin da kwamfutar zamani ke yi, dangane da bayanan da ake shigar mata.  Sai dai, ta fi kama ne da masarrafar sarrafa bayanai na kwamfutocin zamanin da (Anologue Processor), wacce ke sarrafa bayanai ta la’akari da alakar da ke tsakaninsu. (Kwakwalwa) kan yi la’akari da “kamaiceceniya” ne,  da “bambance-bambance” ko “alakar” da ke tsakanin bayanan (da aka turo mata) wajen sarrafawa.”  Wannan ke nuna sarkakiyar da ke cikin tsarin samar da bayanai tsakanin zuciya da kwakwalwa.

Duk da cewa har yanzu ba a gama bincike ba, alamu ne da ke nuna cewa tsohuwar mahangar malaman kimiyya na zamanin baya da ke nuna cewa kwakwalwa ce ke samar da tunani, tana fuskantar barazana matuka.  Ga abin da Sascha Kyassa ta mujallar “Conscious Times” take cewa, bayan ta gama ta’aliki kan sakamakon binciken da Cibiyar “HeartMath” ta fitar: “Binciken baya-bayan nan kan alakar da ke tsakanin zuciya da kwakwalwa na nuna mana ne cewa, lallai har yanzu akwai abubuwa da dama da bamu sansu ba dangane da abin da ya shafi sassan jikin dan adam.  Sakamakon irin wannan bincike ya canza mahangar tunaninmu kan karfi da kudurar da Allah ya halitta a sassan jikin dan adam. Sabon mahangan da muka samu kan hakikanin zuciya da yadda take aiki ya canza mana tsohuwar mahangarmu da ke cewa: kwakwalwa ce ke sarrafa sauran bangarorin jiki, zuwa wacce ke cewa: zuciya ce ke sarrafa kwakwalwa, kwakwalwa kuma ta sarrafa sauran bangarorin jiki.”

Hukuncin Karshe

Dangane da bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa zuciya tana da tasiri mai gamewa kan sauran sasannin jikin dan adam, musamman kwakwalwarsa.  Saboda tasirinta da kuma matsayinta wajen hada alaka tsakanin bawa da Ubangijinsa, shi yasa ambatonta a cikin Kur’ani ya shahara, sabanin kwakwalwa wacce a zahiri ba a ambace ta ba.  Wannan ba mantuwa bane daga Allah, sannan hakan ba ya nuna rashin muhimmancinta kwakwalwa ko kadan.  Illa dai mafi muhimmanci aka duba.  Sai kuma hikima ta Ubangiji, wacce shi kadai ya barwa kansa sani.  Har wa yau, sakamakon binciken da muka samu na nuna mana cewa, wannan zuciya da ke kirjinmu na da tasiri na zahiri wanda ido ke gani, da kuma wanda ido ba ya gani. Sannan, Malaman musulunci basu damu da gudanar da bincike a kimiyyance ba, ba don gazawa ba, sai don ganin cewa alfanun da ke cikin yin bayanai a shari’ance, yafi na kokarin gudanar da bincike a kimiyyance nesa ba kusa ba.  Domin, kamar yadda muka ambata ne a farko, Allah bai saukar da Kur’ani don karantar da ilmin likitanci ba, sai don ya zama shiriya ga bayinsa baki daya.  Amma idan suka yi amfani da basirarsu wajen fahimtar wani ilmi daga gare shi kuma, wannan ya zama ribar kafa.  Shi yasa littafin yake a tsarin sura-sura, ba babi-babi ba, sabanin yadda littattafan da muke rubutawa suke.

Wannan bincike ya tabbatar mana cewa akwai nau’ukan tunani iri biyu; da wanda ke samuwa ta hanyar kwakwalwa, amma asalinsa daga zuci yake, kamar yadda muka gani a misalin da masana suka bayar kan kamaiceceniyar da ke tsakanin kwakwalwa da kwamfuta.  Abin da kwakwalwa ke yi shi ne, karban bayanai, da rarraba su zuwa inda ya kamace su.  Sai dai kamar yadda muka gani, har yanzu bincike na kai dangane da wannan mahanga.  Shi yasa har yanzu ake a kan ra’ayin farko, cewa kwakwalwa ce ke tunani.  Amma a hakikanin gaskiya idan muka duba za mu ga cewa akwai alamun nan gaba wannan mahanga za ta canza.  Sai nau’in tunani na biyu, wanda ke samuwa a zuci, don gudanar da ayyukan da suka kebance zuciyar ita kanta. Sakamakon binciken malaman kimiyya da zai zo nan gaba ne zai tabbatar da “hakikanin” wanda ke samar da tunani, tsakanin zuciya da kwakwalwa. Allah shi ne mafi sanin hakikanin al’amura!

Kammalawa

A karshe, muhawara kan wannan maudu’i ba zai taba mutuwa ba. A baya an sha gwabzawa, nan gaba ma za a ci gaba da yi.  Natsuwa dai na cikin ilmi ne, ba tsantsar baki da misalai da al’ada ba.  Nan gaba zan kawo muku amsoshin da na samu a dandalin Facebook, da wadanda masu karatu suka aiko ta tes, da wadanda na samu ta hanyar Imel. A gafarce ni saboda tsawaita bayani da nayi.  Na yi haka ne don kaiwa makura ga tunanin mai karatu iya gwargwado, amma ba don kure binciken masu bincike ba.  Cikin binciken da nayi, abin da na kalato muku duk bai shige kashi 40 cikin 100 ba.  Duk da cewa na yi kokarin samar da gamewa wajen kawo hujjoji. Allah saka wa wacce tayi wannan tambaya da alheri, tare da dukkan masu sanya ni cikin addu’o’insu, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Abdul Nass says

    Allah ya saka ma da Alkairi wallahi na ji dadin karanta wannan Muqala

Leave A Reply

Your email address will not be published.