Gaskiya da Gaskiya (6): “Ghost Workers”

Da yawa cikin ma’aikatan da gwamnatin tarayya da na jihohi ke biyansu albashi, babu su a hakikanin rayuwa. Sunaye ne kawai sasu suka rubuta, don karban kudin da ba nasu ba.

81

Matsalar “Ghost Workers” ko kace “Ma’aikatan Bogi” na daga cikin manyan matsalolin da kawar dasu a kasar nan sai an zubar da jinin wasu azzalumai. Idan kana neman cutar da taci har ta kusan cinyewa a kasarmu, to wannan matsala ce ta “Ma’aikatan Bogi.” Labaran suna da yawa.

Akwai jihohin da za ka samu asibiti mai kyau, dauke da ma’aikata, da motocin zirga-zriga, da komai da komai. Duk shekara sai an masa kasafi cikin kasafin kudin shekara (Budget). Duk wata sai an raba albashi da na ma’aikatansa, amma a zahirin gaskiya, babu shi. A takarda ne kadai ake da asibitin, amma idan bincike ya tashi, ba za a gani ba. Wasu ne ke dure kudaden a aljihunsa. Laa haula walaa quwwata illa billah! Wannan fa a arewacin najeriya yake faruwa; kasar Hausawa, kuma Musulmi.

Babu kashiya na Jiha ko Karamar Hukuma da ba shi da ma’aikatan bogi da yake dure albashinsu a aljihunsa, a duk karshen wata. Babu wani Sakataren karamar hukuma, ko HOD, wanda bai da ma’aikatan bogi, wadanda yake dure albashinsu a aljihunsa a karshen wata. Wai ina za mu ne? Duk abin da muke tarawa ina muke kaishi? Me mukai wa al’umma bayan mun sace? Kara aure? Ko sayan mota? Ko gina sabon gida? Ko sayan fulotai ta hanyar zalunci? Ko baiwa karuwai? Ina muke zuba su? Ya salaam!

- Adv -

Labaran da yawa, ‘yan uwana! Kwanakin baya ake ban labarin wani Darakta da dansa yayi hatsarin mota, bayan ya gama aikin hidimar kasa (NYSC) yana dawowa gida. Ana masa ta’aziyya sai kecewa yake da kuka babu kakkautawa. Da aka dame shi da ban hakuri, sai yace shi damuwarsa ita ce, tun yaron nan yana dan sakandare ya sa sunansa a jadawalin ma’aikatansu (Payroll), duk wata sai ya ja albashi, har ya gama jami’a. Yace ga shi daidai lokacin da yaro ya gama, zai nema masa aiki ya ci gaba da ja, sai ya mutu! Zancen banza! Bakin cikinsa shi ne, yaro bai rayu har ya kama aiki ba. Ina za mu?

Akwai wanda aka ce min dukkan iyalan gidansa (da manyan ‘ya’ya, da matansa), duk suna cikin jadawalin albashin ma’aikatar da yake aiki. Suna cin bulus!!! Anya bulus ce kuwa???

Akwai wanda yake da ma’aikata 15, wanda yake dure albashinsu a aljihunsa duk wata. Sai da ya gama karbar na watan da ya kare har ya cinye, sai ya tuna ashe akwai bikin ‘yarsa na tafe. Yaya zai yi? Sai ya “kashe” daya daga cikin 15 din na (ya rubuta takarda cewa ya mutu), aka hado masa dukkan kudaden hidimar mutuwa (burial expenses), da giratuti, da fanshon shekaru 5 na mataccen ma’aikacinsa. Ina zai kai wannan matsala ranar kiyama?

Wai su waye azzaluman na hakika ne? Kananan ko manyan?

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.