Gaskiya da Gaskiya (8): Kashe Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani

Allah jikan Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani, ya sa Aljannar Firdausi ce makomarsa, amin.

486

Sadda na farka a daidai karfe 1 na daren Lahadi, 2 ga watan Fabrairu, 2014, ina duba wayata sai naga sakon tes. Budewa ta ke da wuya sai naci karo da:

“Inna lillaahi wa innaa ilaihi raaji’oon. Sun kashe mana Malam Auwal Adam Albani, Zariya, tare da matarsa da yaro/yara cikin mota cikin daren nan. ‘Yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka aikata wannan. Jana’izarsa da safe aka ce. Allah gafarta musu, amin.”

Nan take na kidime, na hargitse, na rasa me ke min dadi. Shin, mafarki nake ne, ko dai da gaske ne? Zuciyata ta fara bugawa uku-uku; bacci ya washe daga idanuna. Na rasa wa zan kira cikin daren nan? Ina ta salallami dai har bacci ya sake dauke ni; ashe mafarki ne zanyi. Wallahi sai na kama mafarki: wai ga ni na kai masa (Malam Albani) ziyara a gidansa kamar yadda na saba, muna zaune a dakinsa muna ta hira. Bayan mun gama hira sai muka fito, ya mini rakiya har na shiga mota ta. Ina farkawa sai na fara shakkun ko dai tes din nan a mafarki na gani ne? Ina sake duba wayata sai na sake cin karo da tes din da aka aiko min. Nan na tabbatar lallai lamarin da gaske ne, mafarkin da nayi ne ke son ruda na.

Da iyalina ta tashe ni da misalin karf 5 daidai, nace ta barni kawai. Ina ta tunanin yaya zan sanar da jama’a a masallacin da muke sallah. Nan take na kira Ummu Abdillah, naji wayarta a kashe. Sai na kira Aliyu Danlabaran Zariya. Yana dagawa, nace: “Malam kayi hakuri na maka sammako, na tashe ka…” kafin in karasa sai yace: “Ai malam ko baccin ma ban yi ba.” Nace na ga tes ne…” Kafin in karasa zancen, yayi caraf yace: “Malam gaskiya ne, haka abin ya faru.” Ai sai idanu na suka cika da kwalla. Bayan sallar asuba na sanar da jama’a, wuri ya sake rikicewa da istirjaa’i. Ina kiran daya daga cikin limaman dake unguwarmu don inji ko ya sani, yana daga wayar sai kawai naji yana ta rusa kuka. Sai na yanke.

Jama’a, mu dawo cikin hayyacinmu.

Wadanda suka aikata wannan ta’addanci, ko kadan basu ci nasara ba. Faduwa ma suka yi, WALLAHI TALLAHI. Malam ne yaci riba, insha’Allah. Muna sa ran Allah ya karbe shi a matsayin shahidi. Nace basu ci riba ba, in sake maimaitawa, sai ma faduwa da suka yi. Mu dubi yadda lamarin yake mu gani.

Na farko, kashe Malam da suka yi na nuna cewa a gaba yake dasu, sun kasa dashi ne; a kowane bangare ne kuwa. Domin mai abin fada ba ya fada. Mara abin fada, shi ke fada. Don ya rasa abin fada, sai ya kare da fada. In suna da hujja kan abin da suke ganin Malam ya tsare musu, me ya hana su fuskanceshi? Wannan alama ce ta gazawa, da tsoro, da kuma tabewa; duniya da lahira.

- Adv -

Na biyu, idan suna ganin don Malam ya tafi, shikenan sun huta daga abin da suke ganin ya tsare musu, WALLAHI sun yi karya. Duk sadda wani babban malami ya rasu, ba za a rasa mai maye gurbinsa ba. Sadda aka kashe Malam Ja’afar (Allah rahamshe shi), an dauka labari ya kare. Ya zuwa yanzu kowa ya san cewa manufar da aka so a cinma, ba ita aka samu ba a matsayin sakamako. Idan an yi haka ne don magoya bayansa su tayar da tarzoma kasar ta rikice, WALLAHI ba a ci nasara ba. Don hakan bai samu ba. Idan an yi haka ne don a dakushe ci gaban SUNNAH, WALLAHI ba a ci nasara ba. Don yanzu ma aka fara. Haka ma lamarin yake a wannan karo.

Abu na uku, wadanda suka aiwatar da wannan ta’addanci tabbas sun jefa mu cikin bakin ciki, da damuwa, da firgici irin na zuci. Amma labarin ba zai tsaya a nan ba. Soyayyarmu ga Malam ce ta sa haka. Kuma na dan lokaci ne, domin dabi’a ce ta zuci. Amma duk yadda mutum ya kai da tsanar Malam Albani, WALLAHI ya san bai ci baya ba sanadiyyar wannan kisa da aka masa. In kuwa haka lamarin yake, to meye masu wannan ta’addanci suka cinma?

Abu na karshe, idan suna ganin kashe Malam ne zai sa duniya ta fahimci karyar da yake kai (a riyawarsu), to WALLAHI basu ci nasara ba. Domin duk wanda yaji labarin wannan kisa, muddin suna wurin, sai sunji abin da zai bata musu rai. Duniya bata fahimci abin da suka fahimta ba. In kuwa haka ne, to ashe su ne suka ci baya.

Don haka, wai don Malami na da’awa tsakani da Allah wasu sun kashe shi, wannan ba alamar tasgaro bane a wajensa. Domin ba shi bane farau. Wadanda suka fi shi daraja da yawan ilimi ma an kashe su. Wannan wata hanya ce da Allah ke amfani da ita wajen karrama bawansa. Ko kadan kada wani daga cikinmu yaji rauni a zuciyarsa, ko yayi laushi, ko ya nuna gazawa, ko mika wuya sanadiyyar faruwar wannan lamari. Sahabban Annabawan Allah ma sun sha samun kansu cikin yanayi irin wannan (kunci, da kwazzaba, da fitinar abokan gaba, da makirci da sharri), amma duk da haka:

“…Basu yi laushi ba ga abin da ya same su a cikin hanyar Allah, kuma basu yi rauni ba kuma basu sad da kai ba. Kuma Allah Yana son masu hakuri.” (Aal ‘Imraan: 146)

Muna rokon Allah, don sunayensa Kyawawa da Siffofinsa madaukaka, ya karbi Malam Muhammad Auwal Adam, da matarsa, da babban dansa Abdallah a matsayin shahidai a wajensa. Su kuma wadanda suka aikata wannan ta’addanci, ya saka musu da abin da suka cancanceshi, duniya da lahira.

Ya Allah! Lalle mu daga gare ka muke, kuma zuwa gare ka za mu komo!!!

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    Ai hakan da sukayi bai ragr mu da komai ba , face kara tsantsar kaunar Malam.

    Allah ya kai haske kabarin malam da iyalan shi, yasa mutuwa hutu ce a gare su

Leave A Reply

Your email address will not be published.