Tsokaci Kan Sabuwar Dokar Ta’ammali da Kafafen Sadarwa na Zamani a Najeriya (2)

Su wadannan manyan kafafen sadarwa da adadin ‘yan Najeriya masu rajista dasu ya wuce dubu dari, dole ne suyi rajista da hukumar Najeriya; ma’ana ya zama suna da rajista a kasarmu kenan, kamar yadda suke da rajista a asalin kasar da suke da asali. – Jaridar AMINIYA ta Jumma’a, 7 ga watan Yuli, 2022.

276

Matashiya

A makon jiya masu karatu sun karanci kashi na farko kan tsarin sabuwar dokar dake gab da fitowa daga Hukumar Bunkasa Fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), inda bayani ya gabata kan bangarori mahimmai da wannan doka ta kunsa.  Mun yi bayanin bangaren “Manufa”, da “Hurumin Dokoki”, da kuma “Kafafen Sadarwa na Zamani”, kafin lokaci yayi mana halinsa. Karkashin wannan bangare na uku dake bayani kan dokokin da suka shafi kafafen sadarwa na zamani (wato kamfanonin sadarwa na zamani kenan, irin su Facebook, da Twitter, da Google da sauransu), mun kawo mahimman dokoki guda biyar.  Karkashin wannan bangare dai har wa yau, akwai wasu kare-karen dokoki wanda da bayaninsu ne za mu bude makalarmu ta yau.

Kari Kan Haka

Dokar tace wadannan kamfanoni masu dauke da kafafen sadarwa na zamani da ‘yan Najeriya ke amfani dasu, bayan dokokin da suka shafi mika bayanai ga hukuma ko ‘yan Najeriya suka bukata ta hanyar umarnin kotu, da kare ‘yan Najeriya daga kowane irin hadari ta hanyar kafafensu, kari kan haka, dole ne su rika sanar da ‘yan Najeriya masu rajista dasu kan tsari da dokokin amfani da kafafensu ta hanyar bayani cikin harshe mai saukin fahimta.  Na biyu, su rika fadakar dasu cewa su nisanci kirkirar bayanai masu haddasa cutar da  kananan yara ko sauran jama’a, ko kage, ko cin fuska ga wani, ko yada tsagwaron batsa, ko barazana ga rayuwar wani, ko tirsasawa, ko satar fasaha, ko yada sakonnin bogi ko yaudara, ko tayar da tarzoma ko husuma tsakanin ‘yan kasa. Na uku, su rika bitar yadda masu amfani da kafafensu ke ta’ammali da bayanai ko aiwatar sadarwa lokaci zuwa lokaci.  Na hudu, dole ne wadannan kamfanoni su rika aikawa da rahoto akai-akai ga hukumar NITDA kan adadin ‘yan Najeriya masu rajista, da adadin masu yawan amfani da shafukansu, da adadin shafukan da aka rufe, da adadin bayanan da aka cire ko sauke sanadiyyar umarnin kotu, da adadin wadanda aka rufe ba tare da sanar da masu shafin ba, da adadin bayanan da aka sake dorawa, da kuma adadin korafe-korafen da kamfanonin suka karba a baya.

Manyan Kafafen Sadarwa na Zamani

- Adv -

Karkashin wannan sashe, dokar ta kawo wasu kebantattun dokoki ne da suka shafi kafafen sadarwa masu dauke da ‘yan Najeriya sama da dubu dari a shafinsu, masu rajista.  Dokokin sashen da suka gabata kuma sun shafi dukkan kamfanonin ne; hada da wadanda adadin mambobinsu a Najeriya bai kai dubu dari ba.

Su wadannan manyan kafafen sadarwa da adadin ‘yan Najeriya masu rajista dasu ya wuce dubu dari, dole ne suyi rajista da hukumar Najeriya; ma’ana ya zama suna da rajista a kasarmu kenan, kamar yadda suke da rajista a asalin kasar da suke da asali.  Na biyu, dole ne su bude ofishi mai dauke da adireshi.  Ta yadda duk sadda ake bukatar tuntubarsu a zahirin rayuwa, za a iya ba tare da wani shan wahala ba.  Na uku, dole ne ya zama suna da jami’i, wanda shi ne zai rika kula da ayyukan kamfanin a Najeriya, kuma wanda duk sadda ake bukatar bayani, shi za a samu kai tsaye.  Na hudu kuma, shi wannan jami’i da za su ajiye, dole ya zama sun bashi damar karban sakonnin koke a rubuce, ko amsa koken mutane idan sun ziyarci ofishin, muasamman kan abin da ya shafi: neman bayanai kan abubuwan dake gudana a shafinsu, da neman bayanai kan dalilin dake sa ana samun bambanci kan nau’ukan sakonnin dake bayyana a shafukan masu ta’ammali da kafafensu, alhali dukkansu ‘yan kasa daya ne.

Madogaran Dokokin

Wannan shi ne sashe ko bangare na shida cikin wannan sabon kundi.  Bangaren na dauke ne da jerin dokokin Najeriya guda goma sha daya dake da alaka da kariyar bayanai, da sadarwa, da watsa labarai na rediyo da talabijin, da sadarwa ta kafofin wayar salula da tangaraho.  Jerin dokokin dai sun kunshi dokar Hukumar Sadarwar Wayar Salula ta kasa, wato:  “Nigerian Communication Commission Act” ko “NCC Act”, da dokokin da suka kafa Hukumar Yada Labaru ta Kasa, wato: “National Broadcasting Commission Act” ko “NBC Act”. Sai kuma Hukumar NITDA da dokar da ta samar da ita.  Da dai dukkan dokokin da ke da alaka da fannin sadarwa na zamani a Najeriya.

Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, dukkan wasu dokoki da aka samar a Najeriya masu alaka da harkar sadarwa, ko wadanda za a samar nan gaba, to, wannan sabuwar doka tana goyon bayansu, kuma tana umartan wadannan kamfanoni da su kiyaye su, don tabbatar da kyakkyawar alaka tsakaninsu da gwamnati da ‘yan kasa, da kuma samar da hanyoyin zaman lafiya da lumana a Najeriya baki daya.

A makon gobe in Allah Ya yarda, zan kawo bayani kan bangare na bakwai, wanda shi ne bangare na karshe da wannan sabuwar doka ta kunsa.  Aci gaba da kasancewa tare damu, kuma ayi Sallah lafiya.  Allah karbi kyawawan ayyukanmu baki daya, amin.  Barka da sallah.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.