Gaskiya da Gaskiya (5): …Sai an Tsangwameka!

Duk yadda ka kai da kintsuwa, da hakuri, da juriya, da kyautatawa, sai an tsangwameka. Wannan sunna ce ta rayuwa, don haka ba abin mamaki bane. Idan kaga haka, ka nemi tsarin Allah daga kasawa, da rashin juriya, da kuma sharrin mai hasada, yayin da ya tashi hasada.

119

A cikin shahararren littafinsa mai suna “Laa Tahzan” (Dont Be Sad), Dakta Aa’idh ibn Abdillah Al-Qarnee ya kawo wani karin magana na Larabawa dake cewa: “Mutane ba sa shurin mushen kare.” Yace muddin za ka yi tasiri a rayuwa, sai an tsangwameka. In ka ga anyi shiru a kanka, duk abin da kake yi ba a cewa komai, a boye ko a fili, to shirme kake yi. Wannan dabi’ar jama’a ce.

Dakta Abdullah al-Qarnee ya sake kawo kissar Imam Ahmad ibn Hambal (Imamu Ahlus Sunnah wal Jama’a), sadda gwamnar lokacinsa ya sa aka kama shi, aka masa bulala zafafa, sannan aka sarkafe shi cikin sarka, aka tasa keyarsa za a kai shi gidan kaso, don ya fadi GASKIYA, YA KUMA KI YIN TAQIYYA CIKIN ZANCE DON YA KUBUTA DA RAYUWARSA. Ana cikin tafiya dashi sai suka yi kacibis da wani mashayin giya shahararre, wanda shi ma an kawo shi, bayan haddi na bulala da aka masa masu zafi.

Wannan mashayi na haduwa da su sai ya kalli fuskar Imam Ahmad bn Hambal ya ganta a murtuke, cikin bakin ciki da damuwa. Nan take sai wannan mashayi yace masa:

“Akaramakalla kada ranka ya baci. Idan ni, a matsayina na mashayi, an min bulala a karon farko, na jure. Na sake sha, aka sake min bulala a karo na biyu, na jure. Na sake sha, aka sake min bulala a karo na uku, na sake jurewa, to don me kai ba za ka jure ba, kai da kake kan gaskiya?”

Nan take sai Imam Ahmad ya ji kamar an kara masa kaimi, wajen hakuri, da juriya, da mika lamari ga Ubangiji.

- Adv -

Ita gaskiya daya ce, kuma muddin za ka fade ta, sai an jarrabe ka ta hanyar tsana, da tsangwama, da zargi, da tuhuma, da kwarododo. Mu tuna mana. Manzon Allah (SAW) kafin ya zama Annabi, kowa a Makka na ce masa “Al-Amin” ne. Amma daga lokacin da yazo yace Allah daya ne, ba a bauta wa kowa sai shi, tun sannan alaka ta lalace tsakaninsa da jama’a, sai ‘yan kadan da suka yi imani da shi.

Wannan kwantar da hankali ne ga duk wanda ke fadin gaskiya, ko yake aikata gaskiya amma ake zarginsa ko ci masa mutunci ta wata hanya, a boye ko a fili. Kamar yadda wani bawan Allah ke cewa:

“Kai dai ka fadi gaskiya; kada ka damu da masu karyata ka.”

Abin da za ka tabbatar shi ne: shin, gaskiya ce nake kai? Shin, aiki ko akidar da nake kai gaskiya ce? In eh, to, kayi irin na gayu:

“…SHARE SU KAWAI!

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    👍👍👍👍

Leave A Reply

Your email address will not be published.