Facebook Gidan Rudu: Abokai Marasa Fuska!

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook, a shekarar 2015.

199

Abokai Marasa Fuska!

Facebook dandali ne dake cike da rudu.  Daga cikin mafi girman aibu da matsalolin Facebook akwai “Rashin Hakika.”  Da yawa daga cikin shafukan mutane dake Dandalin Facebook ba su da hakika; ba su da zati; ba su da fuska; babu su –  sunaye ne kawai da hotuna ko rubutu daga wani kato ko wata katuwa ko wasu karti.

Kana iya ganin shafi mai suna: Alhaji Atiku Abubakar, ko HRH Sanusi Lamido Sanusi, ko Abdullahi Dikko Inde, ko Aisha Buhari, ko Ali Nuhu, ko Sani Danja, ko El-Rufai, ko Amaechi, ko Faefesa Attahiru Jega; duk karya ce.  Kashi 99 cikin 100 na ire-iren wadannan shafuka na shahararru ko manyan mutane, in dai a Dandalin Facebook ne, shafukan bogi ne; babu hakika a tare dasu.

Wata baiwar Allah ta kamu da son wani dan fim din Hausa, bazan fadi sunansa ba.  Haka ta dinga bibiyar shafi mai sunansa, tana ta masa inbox, da magiya, da tura lambar wayarta, da rokon ya amshe ta a matsayin abokiyarsa sannan ya bata lambarsa.  Abin haushi da mamaki, bata san cewa shafin iska bane.  Da kyar ya bata layin waya, ya kuma karbeta.  Da na binciki lambar da ya bayar, na sake neman shafi mai sunansa (akwai su da yawa), sai na ga lambar ta sha bamban da wannan.  Ba wannan kadai ba, akwai adireshin Imel dake shafin (wanda ya boye ba kowa ke iya gani ba), mai dauke da sunan wani kato; ko kadan ba abin da ya hada su.  Banza ta kori wofi kenan.

Na ga wata yar uwa tayi wa shafi mai suna Aisha Buhari inbox, da na karanta abin da ta rubuta, sai da na tausaya mata.  Gaisuwar ban-girma take ta mata, a duk kwana.  Tare da nuna godiya, saboda “uwar gidan shugaban kasa” ta karbeta a matsayin abokiya a facebook.  Da na kalli shafin dake dauke da sunan Aisha Buhari (akwai su da yawa sosai), shi ma nan ya tabbata shafin wani kato ne, tikeke kuwa!  Wallahi ban yi mamaki ba.  Na san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya.

- Adv -

Kwanakin baya wani kato mai suna Martins ya bude shafuka da sunan Amir na Kano, Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi II.  Yana ta yada sanarwa ta wata hanya a facebook, cewa Sarkin Kano ya samar da wani tsari na taimakon matsa da aikin yi.  Sai yace a tuntubeshi ta shafin da ya kaga.  Subhaanallah!  Wata ‘yar uwa ta kusa afkawa cikin tarkonsa.  Ta tura masa inbox, ya bata lambarsa ta Glo cewa a nemi Martins, a bashi CV.  Da zarar ka kira zai baka wani adireshin Gmail na bogi ka aika CV din.  Sannan sai ya sanar dakai cewa ka tura wasu kudade don a gama tsara maka lamarin.  Allah ya mata agaji, da kyar tasha.  Na rubuta sako kan tona wannan badakala, da kai karar shafuka masu sunan Sarkin Kano wajen hukumar Facebook, inda bayan ‘yan kwanaki suka rufe su.  To amma abin ka da takadari, an sake bude sababbi.  A fadaka, jama’a.

Darasi

Ka kiyayi abota ko tura abota ko karban abota daga shafuka masu dauke da sunayen manyan shugabanni ko shahararrun mutane.  Wallahi, tallahi, kashi 99 cikin 100 daga cikinsu ba su da lokacin hawa Facebook; shafukan ba nasu bane.

Idan kunne ya ji, gangan-jiki ya tsira!

Baban Sadik

03/12/2015, 4:44pm

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.