Abubuwan Lura Cikin Sabuwar Dokar NITDA (2)

Duk da cewa abu ne da zai iya daukan lokaci, amma tattaunawa da masana kan harkar sadarwa na zamani zai taimaka matuka wajen samar da gamayyar ra’ayoyi masu samar da fa’ida.  A tare da cewa ba dole bane dauka ko karban dukkan ra’ayoyi da shawarwarin da zasu bayar ba, hadakar ra’ayin na da mahimmanci. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 12 ga watan Agusta, 2022.

301

Sauran Matakan Gyara

Bayan shawarwari kan yadda za a dada inganta gundarin wannan doka, ya kamata kuma hukuma ta sake bin wasu matakai wanda su ne galibin matakan da wasu kasashe suka bi wajen samar da ire-iren wadannan dokoki.  Wannan zai taimaka wajen samar da natsuwa a zukatan ‘yan kasa, da kamfanonin sadarwa, da kuma kungiyoyin sa kai dake kokarin tabbatar da ‘yan cin fadin albarkacin baki.

Domin a kasashe masu tasowa, duk sadda hukuma tayi yunkurin samar da irin wannan doka a wannan zamani, ana masa kallon wani yunkuri ne neman toshe kafar ‘yan fadin albarkacin baki.  Ko kokarin amfani da doka wajen muzguna wa ‘yan hamayyar siyasa, musamman ganin lokacin gudanar da manyan zabuka ya gabato, sannan da wadannan kafafe ne ake amfani wajen yada manufofin Takara da tsare-tsaren zabe.  Don haka, kada hukuma tayi gaggawa. Ga dai wadannan matakai nan kamar haka:

Tattaunawa da Masana Harkar Sadarwa

Duk da cewa abu ne da zai iya daukan lokaci, amma tattaunawa da masana kan harkar sadarwa na zamani zai taimaka matuka wajen samar da gamayyar ra’ayoyi masu samar da fa’ida.  A tare da cewa ba dole bane dauka ko karban dukkan ra’ayoyi da shawarwarin da zasu bayar ba, hadakar ra’ayin na da mahimmanci.  Yin wannan zai kara tabbatar wa ‘yan kasa har wa yau cewa da gaske hukuma take, ba wai siyasa ce ko son zuciya ba.

Tattaunawa da Masu Ruwa da Tsaki

Masu ruwa da tsaki a wannan bangare sun hada da dukkan kamfanonin sadarwa da wannan doka zai iya shafa, musamman kamfanonin wayar salula, da kamfanonin sadarwa daban-daban, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.  Wannan zai samar da gamayyar fahimta a bangaren sadarwa da kasuwanci.  Domin galibin dokokin nan sun shafi wadannan kamfanoni ne, ko dai kai tsaye ko a kaikaice.  Misali, duk wanda ke amfani da wayar salula wajen ta’ammali da fasahar Intanet a Najeriya, yana yin hakan ne ta hanyar kamfanonin wayar salula, irin su MTN, da Airtel, da 9Mobile da dai sauransu.  Har zuwa yanzu, hukumar NITDA bata sanar da yanayin wannan hadaka da tace ta kintsa ba, balle a san yanayin tattaunawar.

- Adv -

Wayar da Kan ‘Yan Kasa

Wannan doka da hukumar NITDA take kokarin fitarwa za ta shafi dukkan ‘yan Najeriya ne da ke amfani da fasahar Intanet; ko dai ta wayar salula, ko ta kwamfuta, ko kuma duk wani nau’in na’urar fasahar sadarwa na zamani.  In kuwa haka ne, kowane dan Najeriya na da hakkin sanin abin da ke ciki, da kuma hanyar da wannan doka za ta shafe shi; ko dai kai tsaye ko a kaikaice.  Sai dai kuma, hakan ba abu bane mai yiwuwa ta sauki.  Hanya mafi sauki ita ce ta amfani da kafafen sadarwa don wayar da kan jama’a dangane da tanade-tanaden wannan sabuwar doka.

Matakin wayar da kan jama’a zai iya zuwa kafin rattafa hannu kan dokar, da kuma bayan an rattafa hannu.  Wayar da kan jama’a kafin rattafa hannu kan dokar zai taimaka wajen sanar da mutane irin tanade-tanaden dake ciki.  Duk wanda ke da wata shawara, zai iya tuntubar hukumar NITDA don ba da nasa shawarar.

A daya bangaren kuma, bayan an rattafa hannu kan wannan doka, wayar da kan jama’a kan abin da ke kunshe ciki zai baiwa kowa damar sanin tanade-tanaden dake ciki, cikin sauki.  Wannan za isa kowa ya kiyaye.  Idan ma mutum bai kiyaye ba, a takaice dai ya san abin da ke jiransa idan ya saba doka.

Cire Son Zuciya

Daga cikin abin da yafi maimaituwa a bakin masu nazari kan wannan sabuwar doka da ake gab da fitarwa, shi ne tsoron amfani da dokar wajen muzguna wa abokan hamayyar siyasa, musamman ganin ana gab da kakar zabe.  Kamar yadda na sanar a baya, wannan shi ne tunanin galibin mutane a kasashe masu tasowa; cewa ‘yan siyasa na amfani da ire-iren wadannan dokoki ne don cin ma burinsu na siyasa, ba wai don kawo gyara a cikin al’umma ba.  hanya mafi sauki wajen tunkude irin wannan tunani ita ce, bibiyar matakan da suka kamata, ta hanyar bibiyar dukkan masu ruwa da tsaki kan al’amari, da bai wa ‘yan kasa damar sani da fahimtar abin da hukuma ke kokarin fitarwa na dokoki don maslaharsu, da kuma yin bayani filla-filla, sanka-sanka.  Hakan zai samar da natsuwa a zukatan mutane, tare da fahimtar hakikanin manufar hukuma wajen samar da dokar ko tsare-tsaren da ake da kudurin samarwa.

Har wa yau, wajibi ne hukuma ta san cewa dokoki irin wadannan fa, manufar samar dasu shi ne su dore, don tabbatar da gyara cikin al’umma.  Kuma babu abin da ke sa a samu dorewar tsari da doka a kasa, irin kyakkyawar manufa, wanda ya samo asali daga bin tsari da matakan da suka dace, don dora al’umma kan turba mai dorewa.

A mako mai zuwa, kamar yadda nayi alkawari a baya, zan kawo mana misalan ire-iren wadannan dokoki daga wasu kasashe.  Wannan zai kara haskaka mana wajen kara fahimtar wannan sabuwar doka ta NITDA, da gano abubuwan da suke daidai da wadanda suke bukatar karin bayani ko karin haske dangane da tanade-tanaden dokar.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.