Yaduwa da Munanan Tasirin Labaran Bogi (Fake News) a Kafafen Sadarwar Zamani (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 10 ga watan Satumba, 2021.

309

Hanyoyin Gane Labaran Bogi

Labaran bogi, kasancewar labaru ne na karya, suna da siffofin da idan ka natsu, za ka iya gane su kafin su maka illa ko al’umma baki daya.  Da farko dai galibi suna dauke ne da take mai jan hankali, musamman wadanda suka shafi wani tashin tashina.  Ko dai takensu ya zama cikin manyan haruffa, sannan masu ma’anar dake jan hankalin duk wanda ya gani.  Wasu ma kaga an sa musu alamar “Da Dumi-dumi”, wato: “Breaking News” kenan.  Na biyu, za ka samu ba daga wata sananniyar kafar yada labarai bane, wadanda ke da rajista.  Sai dai ya zama daga wani shafin yanar sadarwa, ko wani ne ya zauna ya kitsa rubutun.  Na uku, galibin labaran bogi na dauke ne da kura-kuran rubutu, wanda kana karantawa zaka gane ba kwararre bane a harkar yada labarai ya rubuta.  Misali, za ka ga rubutun cakude da kanana da manyan haruffa, a inda basu dace a hada su ba.  Ko ma daga farkon rubutun har karshe, kaga babu alamomin rubutu, irin su wakafa (Comma), ko aya (Fullstop).  Sannan za ka gansu da alamar motsin rai (Exclamation mark) musamman a takensu, don jawo hankalinka.

Siffar labaran bogi na hudu ita ce, daga farkon labarin har karshe, baza kaji inda aka nakalto zancen wani, kalma da kalma ba, don tabbatar da gaskiyar labarin.  Galibi sai dai ance ance.  Siffa ta biyar, labarum bogi galibi kan zo ne da hotuna masu motsa rai ko tayar da hankali, don kokarin razanar da mai karatu da nuna masa “girma” ko “mahimmancin” lamarin da labarin ke dauke dashi.  Ko kuma hoton bidiyo mai dauke da wani kazamin lamari.  Ko sakon sauti mai dauke da muryar wani ko wata da ake kokarin jingina zancen gareshi ko gareta, wanda in da za a bincika, za a samu karya ne labarin.  Siffa ta shida, kana iya gane labaran bogi ne ta hanyar rashin adireshin wanda ya aiko, ko sunansa, ko kuma kasa tantance adireshin da aka jingina labarin gare shi.  Siffa ta bakwai ita ce, labaran bogi na dauke ne da abubuwa masu ban mamaki ko al’ajabi, wadanda a tsarin tunani da hankali, ta la’akari da halin da ake ciki, ba abubuwa bane da ya kamata a yarda dasu.  Misali, cikin makon jiya naga wani sako da aka tunkudo wani zauren WhatsApp, dake cewa wai zuwa karshen watan Agusta, Shugaban kasa yace farashin man fetur zai koma Naira 96, da sauran karerayi.  Amma zuwa karshen labarin, bayan ka gama sakin jiki da dadin karerayin dake sakon, sai marubucin sakon yace wai wasa yake yi.  Ya fadi haka ne don saka nishadi.

Siffa ta karshe ta shafi sakonnin bogi ne masu alaka da addini, musamman na musulunci.  Akwai sakonnin karya da yawa da ake danganta su ga Manzon Allah (SAW).  Su kuma zaka samu ba da larabci ake rubuta su ba; ko da kuwa hadisai ne.  Domin hadisai ne na karya.  Sannan babu sunan mai ruwayan hadisin, ko kuma babu sunan littafin da aka ciro hadisin; kawai zallar rubutu ne zaka gani, har sai ka gaji da karantawa.  Sannan, saboda rashin mutunci, sai ace maka wai Manzon Allah yace, duk wanda ya karanta bai aika wa mutane kaza ba, to, matsala kaza da kaza zasu same shi.  Duk wani sako da ka gani da irin wannan lafazi, to, kai tsaye karya ne.

- Adv -

Munanan Tasirin Labaran Bogi

Illolin dake tattare da samarwa da yada labaran bogi suna da dimbin yawa, ba za su kiyastu ba.  Amma muna iya dunkule su zuwa bangarorin rayuwa.  Na farko, samarwa da yada labaran karya na taimakawa wajen rura wutar fitina a cikin al’umma, musamman a lokacin da ake halin zaman dar-dar.  Kamar irin halin da aka shiga a makonnin baya a arewacin Najeriya, musamman.  Illa ta biyu, samarwa da yada labaran karya na tsirar da rashin yarda a tsakanin al’umma.  Wannan ya kebanci galibin labaran karya da ke da alaka da manufofin siyasa ko bambancin addini ko kabila.  Musamman idan sakon na dauke da kankanta wata al’umma a siyasance ko kabilance ko addinance.

Illa ta uku cikin manyan illolin samarwa da yada sakonnin bogi ita ce illar dake shafar lafiyar jama’a.  Wannan ya fi shahara a zaurukan WhatsApp, inda za ka sakonnin da ake tunkudowa masu cewa idan kana fama da ciwon ido, ka samu ganyen kaza ka shafa.  Ko idan kana fama da cutar gyambon ciki (Ulcer), ka samu garin kaza da kaza ka hada, za ka samu sauki.  A ka’idar rayuwa, duk masana sun tabbatar cewa cututtuka, ko da sunansu iri daya ne, sun sha bamban wajen yadda suke shafan jama’a.  Ba lalai bane maganin da ya magance mini cutar da nake tare da ita, ya zama kai ma zai magance maka naka; saboda bambancin yanayin jikinmu.  Amma masu aiko ire-iren wadannan sakonni, ko da ma gaskiya ne labarin ko sakon, to bai dacewa da kowa.  Yayin da wani ya amfana, wani cutuwa zai yi.

Illa ta hudu mafi girma, ita ce wacce ke haddasa hasarar dukiya.  Nau’in labaran bogi dake wannan dabaka su ne wadanda ‘yan zamba-cikin-aminci (419) ke nufatar jama’a dasu don yaudara da cutarsu.  Sai illa gamammiya ta karshe, wato illa ga rayuka.  Da dama an rasa rayuka da dukiyoyi sanadiyyar wani labarin karya ko sakon bogi da wani ya aiko.  Wannan a fayyace yake.  A kasar Indiya wani ya taba aika wani sako dauke da wasu hotuna da yake ikirarin wata kabila ce ta afka wa wata kabila a wata unguwa.  Isan wannan sako a daya daga cikin zauren WhatsApp ke da wuya, nan take sai rikici ya barke a wasu anguwanni dake makotaka da anguwar da aka ambata.  Kafin wani lokaci, tuni anyi asarar rayuka da dukiyoyi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.